NANA Rahma Abdulmajid Ta Bankaɗo Sharrin Hausawan Bogi
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Tun bayan da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayyana amincewa tare da goyon baya ga Nana Asma’un Zamani – Malama Rahma Abdulmajid dangane da ƙudurinta na shirya fim game da tarihi da ayyukan gwarzuwar Musulunci, ɗiyar Mujaddadin Musulunci, Nana Asma’u bint Shehu Usman Ɗanfodiyo; shi ke nan sai hankalin Dillalan Shaiɗan ya tashi.
Bisa ga wannan babban shiri na Nana Rahma, sai Hausawan Bogi suka sako karnukansu zuwa Soshalmidiya, suka shiga kwarwa da haushi – kamar yadda suka saba, suka yi ta suka da zage-zage, suna la’antar Nana Asma’u da mahaifinta Shehu Ɗanfodiya, suka kuma shiga suka da aibanta ita kanta Rahma, duk dai domin su sare mata gwiwa, su hana ta gudanar da wannan BABBAN AIKI da zai wayar da kan al’umma, ya samar da cigaba ta fuskar ilimin mata da sauransu.
Sai dai kuma ga dukkan alamu, Hausawan Bogi sun makara. Maimakon daƙile aniyar Nana Rahma, sai ma suka ƙara mata ƙaimi da ƙarfafa gwiwa, domin kuwa al’umma sun ankara da ɗimbin alheran da wannan fim zai haifar a duniyar ilimi.
A jiya Rahma ta fito da ƙarfinta, ta ƙara jaddada aniyarta ta ci gaba da wannan babban aiki, sannan kuma a hannun ɗaya ta yi wa Hausawan Bogi wankin babban bargo. A wani faffaɗan saƙon da ta wallafa a shafinta na Facebook mai taken: “Buɗaɗɗen Saƙo Zuwa Ga Masu Kare Haƙƙin Hausa…” Rahma ta warware zare da abawa, tana cewa:
“Buɗaɗɗen saƙo zuwa ga masu kare haƙƙin Hausa, musamman irin su Malama Kaltuma da Gimbiyar Hausa, fatan kuna cikin ƙoshin lafiya.”
Nana Rahma ta ci gaba da cewa: Tun bayan ɓullar labarin shirinmu na yin fim kan rayuwar Nana Asma’u Ɗanodiyo, na ga kun tsananta da rubuce-rubuce da saƙonni na murya, inda kuke yin sharhi ko martani kan abin da har yanzu ma ba ku san mene ne ba.
Wannan ne dalilin da ya sa na ji ya kamata na fayyace muku wasu abubuwa guda uku kamar haka:
1-Ni dai sunana Rahma Abdulmajid. A shekara mai zuwa zan cika shekaru 30 cif ina bai wa harshen Hausa gudunmawa ta hanyar rubutu, wanda na fara tun ban wuce shekara 15 ba. Wataƙila ma da yawanku a lokacin ba ku san wene ne Bahaushe ba. A cikin waɗannan shekaru, na fuskanci ƙalubale da ya girmi barazanarku, ba tare da na fasa ba. Babban abin da nake da yaƙinin na nuna a wannan tsayin shekarun, shi ne yadda Bahaushe ke iya kyautar abu mafi ƙima gare shi, wato harshensa don sadar da amfani; har ga wanda ma ba Bahaushe ba.
Ba ni kaɗai ba, akwai dubban marubuta da malaman jami’a, waɗanda ba Hausawa ba ne zalla. Sun yi wa harshen Hausa hidimar tattara adabinsa da Ilminsa da tarihinsa, tun kafin zuwa na har aka iso yau, ku ma kuka samu kuke amfani da ayyukansu wajen rubutunku.
2-Aikin fm ɗin Nana Asma’u, na shirya yinsa ne don bayyana wani gagarumin aikin ‘ya mace Musulma a Arewacin Najeriya, kan yaɗa ilmi ba yaƙi da cin garuruwa ba – aikin bai da alaƙa da ƙabilanci ko yare. Manufar aikin shi ne, Arewa ta fara bayar da labarin kanta da kanta.
Irin wannan aiki na bajinta, ba mu sami irinsa a sauran gimbiyoyin da kuke faɗa na Hausawa ba tukuna sai a kan Nana Asma’u. Shi aikin tarihi ba aikin shaci-faɗi ne ko fatar baki ko kiran sunaye ba. Ita kanta Nana Asma’u, duk da ta yi rubutu, sai da aikin tace labarinta ya ɗauke mu shekaru uku. Kun ga ke nan ba wai aiki ne za mu yi a kan tatsuniyoyin da ba su da tushe, sai don an haɗa su da sunan martani ko fushi ba.
3-Shawarata gare ku: Maimakon yaƙar kada a yi fim ɗin wani ko wata don yana Fulani, ku kawo mana labarai da ingantattun tarihi mai ɗauke da gudunmawa da wata gimbiya ta Hausa ta bayar; wanda har yau ake cin moriyarsa. Mu kuwa in sha Allah, da mun kammala aikin Nana Asma’u za mu dira a kansa, mu aikata shi. Ba ma Hausawa kaɗai ba, ƙofarmu a buɗe take wajen shirin yin fim a kan ƙabilun Arewa da suka haɗa da Gbagi, Tiv, Kanuri, Jukum da sauransu.
Kawai dai mu sharaɗinmu, muna son mu yi fim ne kan wata gudunmawa ga bil’adama, haɗin kai da zaman lafiya da fim ɗin zai bayar, maimakon haddasa gaba da ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.
Misali, ba zan yi fim a kan Gimbiya Daurama, in ce an rasa Bahaushe ɗan Daura da zai kashe maciji a rijiya ba, sai da baƙon Balarabe ya zo ya ceci Gimbiya ya aure ta. Ko kuma in yi fim kan Sarauniya Amina, tana kashe ƙabilar Nufawa, tana kwaso ‘ya’yansu a matsayin bayi; don kawai ina son nuna gwarzuwar Bahaushiya – kamar yadda na ji Kaltum na buƙatar in yi fim a kanta, don kawai akwai gunkinta a National Theatre a Lagos ba.
Wannan a wajena zai zama cin zarafi ne ga tarihin Bahaushe, wanda aka sani da jarumta, juriya da kyauta da rashin son rigima. Fim ba sunayen gwaraza ne kamar roƙo ko waƙa ba. Labari ne na abin da mutum ya aikata tare da wasu jarumai, ko dai a ƙirƙira ko a nuna na gaskiya.
A ƙarshe, ina mai ba ku shawara da ku sirka salon gwagwarmayarku, daga fito-na-fito, maganganu marasa tabbas. Ku bari a riƙa tattaunawa a kan doron ilmi cikin haƙuri da kyautata lafazi. Ni ba Bafulatana ba ce amma ba da takobi Fulani suka kawo ni yin aikin Nana Asma’u ba – da rubutaccen tarihi ne a kanta da ayyukanta. Sannan ba su taɓa hantara ta ko iface-iface a kan me ya sa ba a yi fim a kan kakarsu ba. Hasali ma, ban taɓa zama da wani daga cikinsu da ke bambance Hausawa da Fulani ba. Hakan ta sa muka yi sha’awar aikinsu. Amma zafin kai ba ya tanƙwara mutane, sai dai ma ya ƙara tunzira su.
Idan fa da gaske haƙƙin Bahaushe kuke nema, babu wata ɓoyayyar ajanda, to ku bayar da ƙofar tattaunawa cikin lafuzza na hankali da ilmi a kan wannan lamari. In sha Allah za ku gan mu tare da ku a wannan gwagwarmayar.
Na gode. ‘Yar uwarku Rahmar Arewacin Najeriya.”
Bayan Nana Rahma Abdulmajid ta kammala babban saƙonta, mutane da dama sun tarfa albarkacin bakunansu. Ni kaina na ce wani abu, domin kuwa na daɗe da sanin muguwar aƙidar waɗannan mutane da ke sukar Mujaddadi Ɗanfodiyo, wanda dalili ke nan ma na sanya masu laƙabin “Hausawan Bogi.” Ga abin da na ce:
•Ma sha Allah! Malam Nasiru Adamu El-hikaya zo ka ga yadda Malama Rahma Abdulmajid ta yi wa Hausawan Bogi wankin babban bargo.
Lallai Rahma ta ƙyalo gafalallun nan kuma babu shakka watan faɗuwar darajarku ya kama. Babban abin da muke so daga kowace ƙungiya, ba ta kawo mana RARRABUWAR KAI da RUƊANI ba a Arewa. Abin da al’ummarmu take ƙishi, shi ne faɗakarwa da tunasarwa da wayar da kai, domin samar da zaman lafiya da cigaba.
A wannan sabon ƙarni na wayewa da cigaba, babu ruwanmu da KISHIN ƘABILA ko YANKI. Babu ruwanmu da WARIYA da TASHIN-TASHINA marar alfanu, wacce ba za ta tsinana mana komai ba. Abin da muke buƙata shi ne HAƊIN KAI domin taimakon cigaban alummarmu. Mu a fahimtarmu, kowane yare ne kai, kowane mabiyin addini ne kai, ko daga wacce shiyya ka fito, madamar kai MUTUM ne ɗan Adam, to muna buƙatar fasaharka, hikimarka, basirarka da iliminka, domin a haɗu a taimaki juna.
Ina roƙon Allah ya taimaki Rahma da duk masu tunani irin nata, su yi nasarar fito da irin waɗannan manyan finafinai, domin wayar da kan al’umma.
Saƙo daga Bashir Yahuza Malumfashi, Mai Yaƙi da Ƙabilancin Hausawan Bogi!
_______________













