Littafin Bango Ya Tsage: Takaitaccen Tsokaci Da Shawara
Babu shakka, duk mai kishin adabi, dole ya jinjina maka dangane da wannan babban aiki da tuni ya kamata a ce an yi shi. Amma godiya ga Allah da ya zo, a yanzu. Ba a makara ba.
Babu wanda zai kushe wannan aiki, sai wanda ya kawo ƙyashi da hassada. Don haka ya kamata tsangayoyin Hausa na jami’o’i da kwalejojin ilimi na duniya su amshi wannan aiki da kyau sosai.
Wannan babban aiki yana ɗauke da muhimman abubuwa guda biyu: Bunƙasa Adabin Hausa da na Afirka da kuma kawo fahimta tsakanin al’adun Hausawa da na Ibo.
Ya kamata marubutanmu na Hausa su ɗauki hannu, su nitsa cikin binciken al’adunmu na dauri na cikin gida, su samar da manyan litattafai na alfahari irin wannan. Ba kawai a tsaya kallon finafinan Indiya ana kwafowa ana maka wa Hausawa ba. Idan muka tsaya ga littattafan gaske da marubutan Afirka suka samar, za mu gina namu masu inganci da amfani ga al’umma.
Malam Ibrahim Sheme , ina da ‘yan shawarwari guda biyu game da wannan babban aiki naka.
1-A fahimtata sunan littafin nan: “Bango Ya Tsage” bai kamaci fassarar “Things Fall Apart” ba, musamman idan muka duba ma’anar karin maganar ‘sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wurin shiga.’ Shi tauraron littafin Things Fall Apart, tun da farko ba wani bango ba ne. Hasalima ya faro haƙilon rayuwarsa daga tushe – bai da gatan komai. Don haka, ina ba da shawara da a ƙara nazari a samo sunan da ya dace, duk kuwa da cewa BANGO YA TSAGE yana da daɗi da kama fuska, to amma ma’anarsa ba ta dace da ƙunshiyar littafin ba.
2-Shawara ta biyu, ita ce game da amfani da tsarin Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Kowa ya san matsayarka da fahimtar ƙashin kanka game da wasu daga ƙa’idojin rubutun Hausa, musamman abin da ya shafi rabawa ko haɗewar lamurran mallaka.
Ko a can baya, musamman dangane da mashahurin littafinka na ‘YARSANA’ an sha daga da masana Hausa. Babu shakka rashin bin waɗannan ƙa’idoji na bai ɗaya a duniyar manazarta nahawun Hausa, ba ƙaramar naƙasu take kawo wa mashahuran littattafanka ba.
Don haka ina shawartarka da cewa, ya kamata a wannan babban aiki na Bango Ya Tsage, ka daure ka ɗabbaƙa ƙa’idojin nan na bai ɗaya, ka jingine wannan na ƙashin kanka. Ba don gazawa ba, amma domin tafiya da Duniyar Manazarta Hausa. Ina ganin hakan zai ƙara wa aikinka martaba a DUNIYAR HAUSA.
Ina fatan za ka kalli shawarwarin nan da idon basira, a matsayin gudunmawata ga kishin adabin Hausa da rubutunsa.
Ina yi maka fatan alheri da fatan littafin nan zai amfani al’umma, amin.
~~~~~~~
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Babban Editan Jaridar Taskar Gizago
~~~~~~~

Na karanta shawarwarinka, kuma gaskiya sun zo daya da nawa. Kuma ni ma a shafinsa na Facebook na gaya masa shawararka ta farko.
Haka ne. Allah kara mana fahimta. Na gode sosai.
Salaam.
Sai yanzu na dawo kan wannan shawarar da ka kawo a kan littafin Bango Ya Tsage. A lokacin da ka yi ta, aiki ya rufe ni, kuma an yi “comments” masu ɗimbin yawa a kan rubutun da na yi a Facebook waɗanda ba zan iya amsa su ɗaya bayan ɗaya ba.
1. Ba shakka, sunan da na ba littafin a fassara shi ya fi dacewa da shi. Ba za ka fahimci dacewar fassarar sunan littafin ba har sai ka san ma’ana da manufar sunan da Chinua Achebe ya raɗa wa nasa littafin, da kuma inda ya ɗauko sunan. Akasin yadda ka ce, ba Okonkwo ba ne “bango” a labarin. “Bango” na nufin ita al’ummar Ibo a lokacin da Turawan mishan da na mulkin mallaka suka kutsa kai a ƙasar. Okonkwo ya so a ce al’ummar sa sun cure sun zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, kada su rarraba, domin su yaƙi kutsen da Turawan suka yi masu, suka wargaza su, suka kawo masu baƙin al’adu da addini. Hausawa sun ce “sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wurin shiga.” A littafin Things Fall Apart na Achebe, “bangon” (wato al’ummar Ibo) ya tsage ne, shi ya sa “ƙadangare” (wato Turawa) suka samu har suka kurɗa cikin su, suka kawo masu rarrabuwar da ta jawo masu faɗa da junan su. Wannan rarrabuwar ita ce “things fall apart” – wato abubuwa sun tarwatse; al’amurran al’ummar Ibo sun tarwatse!
A tawa fassarar, na ƙi in ce “al’amurra sun tarwatse” ko “abubuwa sun tarwatse” kamar yadda wasu na ga wasu masu sharhi suka so in ce. Dalili shi ne yin hakan zai karya ƙa’idar yin fassara, wato zai zama “direct translation”. Abin da na yi shi ne “fassara daidai da maudu’i”, wato “contextual translation.”
A cikin littafin kuwa, na yi ƙoƙari matuƙa wajen bin kalmomi da jumlolin magana na Achebe na asali sau da ƙafa don tabbatar da cewa ban kauce alƙiblar da ya dosa ba, ko ainihin manufar da yake so ya isar ga mai karatu. Na tabbatar za ka fahimta yanzu.
2. Ƙa’idojin Rubutu: ???
Ibrahim Sheme
15 ga Agusta 2024
VeGA SHAWATA TA BIYU:
Malam Ibrahim Sheme , na gamsu da bayaninka sosai dangane da shawarata ta 1.
Amma dangane da shawara ta 2, ina ganin kamar ka samu tangarɗa wajen kwafo sharhin nawa duka, daga ainahin shafin Taskar Gizago , ka ɗauko iyaka shawarata ta 1, ka bar ta biyu.
To ga ta biyun nan kamar yadda na bayyana tun da farko:
~~~