• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, July 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 14, 2026
in Babban Labari
0
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Wanda ake zargi da tozarta Manzo (saw), Fasto Emmanuel Sunday Garba

31
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026
Wanda ake zargi da tozarta Manzo (saw), Fasto Emmanuel Sunday Garba

 

__________

Arewa ta daɗe da samun kanta cikin rikici iri daban-daban, musamman ma wanda ya fi ƙamari da ɗaukar hankali, shi ne mai nasaba da bambance-bambancen addini da akida.

Ko a makonnin da suka gabata, an samu irin waɗannan rigingimu masu yoyon bambancin addini a Jihar Filato, waɗanda suka haddasa salwantar rayukan mutanen da suka haɗa da mabiya addinan Musulunci da Kirista.

A wannan karon, musamman an ɗora zargin alhakin faruwarsu a wuyan mutum biyu, Rabaran Ezekiel Dachomo da kuma ɗan ƙasar Amurka, mai bushara, Alex Babir. An zarge su da gabatar da jawabai da huɗubobin da ke tunzura mabiya addinin Kirista, domin su tayar da fitina tsakanin abokan zamansu, Musulmi.

Ba a gama alhinin wannan fitina ba, kwatsam kuma sai aka wayi gari da wata fitinar mai muni, inda aka samu ƙazaman bayanan cin zarafin Musulunci da Musulmi daga bakin Fasto Emmanuel Sunday Garba. An samu bidiyonsa, inda yake cin zarafin Alkur’ani da ma Manzon Allah, Annabi Muhammadu (saw). Ga al’ummar Musulmi, wannan lamari ne mai matuƙar muni da ke haddasa tunzuri da baƙanta zuciya. Dalili ke nan da dama daga malaman Musulunci da ma al’umma suka buƙaci hukuma da ta ɗauki matakin doka a kansa, domin hana al’umma ɗaukar doka a hannunsu a kansa.

Wane ne Fasto Emmanuel Sunday Garba? Tabbatattun bayanai sun nuna cewa, an haife shi a ranar 28 ga Oktoba 1975. Asalinsa ɗan Jihar Gombe ne amma mazaunin Jos, Jihar Filato, inda yake gudanar da al’amuran da suka shafi huɗubobin addinin Kirista.

Sai dai kuma duk da cewa yana gabatar da kansa a matsayin fasto, bincike mai zurfi a shafukansa na sada zumunta da suka haɗa da Facebook, Instagram da sauransu, bai gano wata tabbatacciyar shaida ba, wadda ke nuna sahihancin matsayinsa na fasto, ko alaƙarsa da wani coci ba. Haka kuma babu inda aka samu bayanin da ke nuna cewa ya taɓa samun horo ko ƙwarewa kan ilimin addinin Kirista da har ya kai matsayin fasto.

Bincike kuma ya nuna cewa, Emmanuel bai da wani coci na kansa da yake tafiyar da lamuransa na bushara. Sai dai an samu tabbacin cewa a shafukansa na soshalmidiya yake tafiyar da al’amuran nasa. Yana tsara bidiyo da bayanai na suka da cin zarafi ga Musulunci, Musulmi da fitattun malaman Musulunci. Akasari yakan ɗauki wasu sassa na wa’azin malaman Musulunci, sannan ya bi su da munanan sharhi da cin zarafi, domin tunzura mutane da nufin haddasa fitina.

Emmanuel Garba ya yi ƙaurin suna sosai a lokacin rikicin Jos na bayabayan nan, inda yawaitar bidiyoyin munanan kalamansa a kan Musulunci suka zama ruwan dare a kafafen sada zumunta. Yakan yanke sassa daga huɗubobi ko wa’azuzzukan Musulunci, sannan ya gabatar da tsokaci na tozarci da cin zarafi; abin da ke ƙara rura wutar rikici.

Ya zuwa yanzu dai al’ummar Musulmi a Arewacin Najeriya sun harzuƙa kuma suna ta kiraye-kiraye ga hukumomi da su ɗauki matakin gurfanar da shi a gaban kotu, sakamakon cin zarafin da ya yi wa Manzon Allah (saw).

Fitaccen mai wa’azin Musulunci, Malam Adam Ashaka, yana cikin masu wannan kira ga hukuma, kamar yadda wasu kuma da dama da suke jaddada ɗaukar mataki a kansa, idan har hukumomi ba su yi haka ba.

Wani fitaccen mai amfani da shafin X mai suna Buhsting, @M_buhsting ya bayyana ra’ayin da al’ummar Musulmi suke da shi, inda ya rubuta a shafin nasa, cewa:

“Wannan mutum daga Jihar Gombe yake. Ya ƙetare layin da bai kamata a ƙetara ba, domin ya zagi Manzon zaman lafiya, Annabi Muhammad (SAW), a cikin mummunar hanya. Mu masu bin doka ne kuma ba mu goyon bayan ɗaukar doka a hannunmu. Haƙƙin gwamnati da hukumomi ne su gaggauta nemo shi, domin ya fuskanci hukunci. Idan ba a ɗauki matakin doka a kansa ba, to kada a zargi Musulmi idan suka yanke shawarar ɗaukar mataki da kansu. Rayukanmu da duk abin da muka mallaka sadaukarwa ne ga Manzon zaman lafiya, Annabi Muhammad (SAW).”

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum da dama, sun soki lamarin, suna cewa abubuwan da Emmanuel Garba yake yi, ba sahihiyar tattaunawar addini ba ce, illa dai yunƙurin tayar da rikici da nufin samun ɗaukaka.

Yayin da kiraye-kirayen a kama shi ke ƙaruwa, mutane da dama na sa ido domin ganin yadda hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki za su magance wannan lamari da ke ƙara ta’azzara.

______

Previous Post

MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

Next Post

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

Related Posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista
Babban Labari

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo
Babban Labari

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria
Babban Labari

Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

June 25, 2026
Next Post
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

January 31, 2026
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria

Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

June 25, 2026
Na Samu Rufin Asirin Rayuwa Dalilin Rubutu Fiye Da Kwalin Digirina – NAS

Na Samu Rufin Asirin Rayuwa Dalilin Rubutu Fiye Da Kwalin Digirina – NAS

September 25, 2023
A New Dawn for Agricultural and Technological Education in Malumfashi/Kafur

A New Dawn for Agricultural and Technological Education in Malumfashi/Kafur

June 19, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.