• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

ADABI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 11, 2026
in Adabi
0
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Hajiya Jamila Tangaza

87
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Hajiya Jamila Tangaza

 

__________

Jamila Tangaza!

“Jamila Tangaza?” Wataƙila tambayar da za ku yi ke nan, kasancewar lallai kun san sunan nan sarai amma daga baya kuka ji shiru, kamar malam ya ci shirwa. To, bari in ƙara maimaita maku sunan: Jamila Tangaza!

Babu shakka na san yanzu kun tuna da wannan sunan, domin kuwa ba zai taɓa ɓuya ba, komai tsawon zamani. Hajiya Jamila dai shahararra kuma ƙwararriyar ‘yar jarida ce, wacce ta kafa suna a aikin jarida a duk faɗin duniyar Hausa.

Ita ce ‘yar jarida mace ta farko da ta fara zama Shugaba a Sashen Hausa na Gidan Rediyon BBC kuma ta kafa babban tarihin da ya karaɗe sassan rayuwa da suka shafi, siyasa, tattalin arziki, rayuwar yau da kullum da kuma adabi. Ta gabatar da shiryen-shiryen rediyo masu ilimantarwa, faɗakarwa da gamsarwa, waɗanda suka yi tashe kuma suka samu amsuwa daga ɗinbin al’umma.

Babu aune, sai mutane suka daina jin ɗuriyarta, ta ɓace ko sama ko ƙasa. Hatta a soshalmediya, an daina ganin gilmanyarta. Wasu ma har sun fara tababar ko ta rasu ne? Amma ina, da sauran aiki…

Kamar daga sama, sai ga sanarwa daga shafinta na Facebook, inda ta bayyana ɗauke da babban albishir mai sanyaya rai ga masoyanta da ma al’umma gaba ɗaya, musamman ma masu son ilimi da ilimantarwa.

Ga abin da ta sanar, a shafin nata: “Assalamu alaikum wa rahmatullah. Bayan shekaru masu yawa, ga shi Allah ya ba ni ikon komowa filin sada zumunta na Facebook.”

Ta ce: “Mutane da yawa suna ta tambaya, cewa shekaru da yawa ba sa ji na. Ko me ya sa?

“A yunƙurina na bayyana abin da ya faru da ni bayan na ajiye aikin BBC, na koma Nigeria, na rubuta littafi mai suna: “REFUSAL: POWER, INTEGRITY, THE COST OF CONSCIENCE.”

Hajiya Jamila ta bayyana cewa wannan littafi ya ƙunshi tarihin rayuwarta. Ta yi bayani dalla-dalla kan zarge-zarge da yunƙurin ɓata suna a wancen lokaci. Ta kuma yi bayani kan yadda ta tsallake wannan ƙalubalen, bisa taimakon Allah da addu’o’in ɗinbin al’umma, musamman ma masoyanta.

Ta ci gaba da bayyana cewa a cikin littafin, ta bayyana darrusan da ta koya, musamman a ɓangaren shugabanci da abin da kan biyo bayan samun ɗaukaka, musamman ma a ƙasar Afirka, kamar Nigeria.

Tangaza ta ce har yanzu littafin yana maɗaba’a yana shan ƙwankwasa da ‘yan gyare-gyare. Sai dai ta yi wa al’umma albishir da cewa, in sha Allahu, da zarar an kammala aikin buga shi kuma ya fito, za ta sanar wa al’umma.

Game da dawowarta fagen soshalmidiya kuwa, Hajiya Jamila ta ja hankalin al’umma tare da tunatarwa. Ta ce, “a wannan lokacin da ƙasa da duniya suka kacame da matsaloli, wajibi ne mu haɗa kai domin mu taimaki kanmu. Ina rokonku da sunan Allah (swt), da mu yi mu’ala ta girmama juna, ba tare da ɓatanci, raini, ko cin zarafin kowa ba.”

Haka kuma, Hajiya Jamila ta yi togacciya da ƙa’idojin da Shari’a da Doka suka tanada, dangane da musharaƙa da juna a soshalmidiya, inda ta ce: “Kada ku manta cewa, a Nigeria, Sashe na 24 na Dokar Cybercrimes (Prohibition, Prevention, etc.) Act, 2015, wacce aka yi wa gyara a shekara ta 2024, ta haramta wasu nau’o’in aikawa ko watsa saƙonnin cin mutunci, ɓatanci, barazana, ko tsoratarwa ta hanyar kwamfuta ko hanyoyin sadarwa (wanda ya haɗa da kafofin sada zumunci, e-mail, SMS da sauransu). Yin haka na kai wa ga ɗaukar matakin shari’a, domin bin kadi.”

Da take ƙarƙare bayaninta, shahararriyar ‘yar jaridar ta ce: “A ƙarshe, ina roƙon Allah ya taimake mu, ya ƙara sutura, ya kare mu, ya ƙara mana da ƙasarmu albarka, amin. Ina godiya ta musamman ga dukkanin masoyana da ƙanina Zaidu Bala da ƙungiyoyi daban-daban da muka shafe shekaru muna mu’amala. Na gode. Allah ya saka da alheri.

__________

Previous Post

Nasihar Juma’a

Next Post

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (10)

Related Posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)
Adabi

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
Adabi

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa
Adabi

Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa

August 29, 2026
Next Post
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (10)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (10)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026
FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

September 3, 2023
The Federal Capital Territory Abuja: The Past, Present and the Future

The Federal Capital Territory Abuja: The Past, Present and the Future

September 13, 2023
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.