• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki

Sun yaba da yadda ya yi wa al'umma hidima

webmaster by webmaster
June 4, 2023
in Labarai
0
Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki
121
SHARES
62
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Related posts

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

August 13, 2026
Birgediya-Janar Sani Usman Kuka-Sheƙa (mai ritaya), shi ne Sarkin Yaƙin Kanwan Katsina, kamar kuma yadda ya kasance tsohon Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya. Yana daga cikin na hannun daman tsohon Ambasadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), OFR, Betaren Biu kuma Garkuwan Keffi. A wannan rahoto na musamman, Janar SK Usman ya bayyana yadda suka ziyarci Daura a makon nan:
A ranar Juma’ar da ta gabata (02-06-2023) na samu martabar yin rakiya ga Mai Girma Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) CFR (Magayakin Ƙasar Hausa), tsohon Babban Hafsan Rundunar Sojojin Najeriya, tsohon Ambasadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, zuwa birnin Daura mai daɗaɗɗen tarihi, a Jihar Katsina, Najeriya.
Maƙasudin ziyarar shi ne domin gaisuwa ta musamman ga babban ɗan kishin ƙasa, dattijo, tsohon Shugaban Ƙasa, Mai Girma Janar Muhammadu Buhari, GCFR kuma domin taya shi murnar kammala shugabancin Najeriya na tsawon shekaru takwas. Haka kuma mun yi masa fatan alheri da addu’ar ci gaba da samun nasara a rayuwarsa ta gaba. Haka kuma mun yi masa godiya da irin goyon baya da tagomashi da ya riƙa bai wa Janar Buratai, a lokacin shugabancin Rundunar Sojojin Najeriya. Mun yaba masa da irin yadda ya yi wa al’ummar Najeriya da ma duniya baki ɗaya hidima a tsawon shekarun mulkinsa.


Irin wannan muhimmiyar ziyara ba za ta kammala ba, ba tare da mun miƙa gaisuwa ta musamman ga Uban Ƙasa, Mai Martaba Sarkin Daura, Farouk Umar Farouk CFR ba. Don haka, wannan ziyara ta ba mu damar gabatar da Sallar Juma’a a babban masallacin Daura tare da Mai Martaba Sarki da Shugaba Buhari, sannan kuma muka ziyarci fadarsa.
Babu shakka, wannan ziyara ta ƙayatar da mu, musamman yadda ta farfaɗo mana da tarihin wannan muhimmin gari da masarauta da ta share sama da shekaru 3,000 a duniya. Wani al’amari muhimmi da ya ɗauki hankalina, shi ne irin kaifin basirar Mai Martaba Sarki da irin karsashinsa da kula da mu cikin karimci, duk kuwa da cewa ya cin ma shekara fiye da 91. Mun yi amfani da wannan dama wajen yabawa da nuna matuƙar godiyarmu da irin karimcin da ya nuna mana da ƙauna, a matsayinsa na uban al’umma.
A duk tsawon ziyarar nan tamu, an nuna mana tsantsan karimci, gami da ingantaccen abincin rana, wanda Alhaji Mamman Daura da Ambasada Muntari Ali Daura suka tanadar mana. Abokina Alhaji Rabe, sai da ya tanadar mani da sanannar “fura da nonon Daura” domin kawo tsaraba Abuja.
Babu raba ɗaya biyu, tabbas wannan ziyara za ta daɗe a zuciyata, a matsayin ɗaya daga zumunci mafi fa’ida da suka faru a rayuwata. Babu shakka na ƙaru da ilimi da zumunci da ƙauna, kamar yadda ta ƙarfafa mani gwiwar ci gaba da riƙe halayen gaskiya da amana. Lallai na ji daɗin wannan ziyara mai girma da muhimmanci, wacce ba zan iya ƙimanta ta da komai ba.
Previous Post

Rusau A Kano: Ina Bayan Gwamna Abba Gida-Gida

Next Post

Sheikh Abduljabbar Ya Kusa Samun ‘Yanci

Related Posts

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne
Labarai

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina
Labarai

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

August 13, 2026
An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci
Labarai

An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci

August 12, 2026
Next Post
Sheikh Abduljabbar Ya Kusa Samun ‘Yanci

Sheikh Abduljabbar Ya Kusa Samun 'Yanci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KO YANZU ZA A IYA FARA KARATU A BABBAR KWALEJIN NOMA TA NABANJE – Malam Labiru Ƙafur

KO YANZU ZA A IYA FARA KARATU A BABBAR KWALEJIN NOMA TA NABANJE – Malam Labiru Ƙafur

August 5, 2025
MENE NE SO?

MENE NE SO?

April 27, 2025
Sokoto State: ASATTAHIR Foundation Supports 1000 IDPs, Vulnerables  By Ibrahim Danfulani

Sokoto State: ASATTAHIR Foundation Supports 1000 IDPs, Vulnerables By Ibrahim Danfulani

December 26, 2023
Katsinawa Suna Murna Da Ɗaukakar Da Maryam Idris Ta Samu

Katsinawa Suna Murna Da Ɗaukakar Da Maryam Idris Ta Samu

September 20, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)
  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon
  • Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

August 24, 2026
Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon

Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon

August 23, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.