KAMUN LADUYIN JEMAGE (19-08-2023)
Daga Mukhtar Mudi Sipikin
~~~~~~~
Zaune nake jugudum ina ta karanta wasiƙar jaki, sai na ji “Ƙililin!” Saƙo ne ya sauka a cikin akwatin wayata. Na duba dai na ga ashe Malam Na Fagge ne ya turo mani shaguɓensa na mako, mai taken ‘Kamun Ludayin Jemage.” Ya ce, “Malam Shanshani, yau ma ga abin nan.” Ni kuwa na yi saurin karantawa. Jama’a, ku biyo ni mu karanta tare:
~~~~~~~
Hazbiya ta kalli tsuntsaye ta ce: “Ƴan uwana tsuntsaye, na yi mafarki cewa nan gaba kaɗan kifayen cikin ruwa za su fara tashi sama, suna shawagi a sararin samaniya. A cikin mafarkin kuma an nuna mun cewa bishiyoyin dajin nan za su fara tafiya. Ni dai na rikice, na kasa gane ma’anar wannan mafarkin da na yi.”
Kurciya ta yi murmushi, sannan ta ce: “Ke Hazbiya, ki gode Allah a mafarki kika ga wannan abubuwa masu rikita tunani, mu tsuntsayen dajin nan a zahiri muke ganin irin wannan lamura. Ko ba ki da labarin ma’aikatun da Jemage ya rarraba wa mataimakansa ba ko? Agwagwa, wadda duk duniya ta ƙware wajen iya ruwa, yanzu an tura ta kula da ma’aikatar kula da sheƙar tsuntsaye, Talotalo kuma da Ɗantsako wai su aka sanya a ma’aikatar tsaro ga ɓarnar Shaho…”
“Ni ba wanda ma ya fi ɗaure mun kai sai Kabarai, wanda aka naɗa a kan mai lura da walwalar tsuntsayen dajin nan. Kabarai fa, eanda ya yi ƙaurin suna wajen halayyar Yautai – Kaico!” Kanari ta tsalma baki.
Gado ya ce: “Wannan kamun ludayin na Jemage sai ka rasa gane ina ya dosa, kullum cikin birkita lamura yake, Allah Ya kyauta.” Tsuntsaye suka gama baki suka amsa da “Amin!”
Bainu ta kalli Alhudahuda ta ce: “Uban ‘yan boko!Me za ka ce a kan wannan lamari na Jemage? Amma don Allah ka yi magana mara sarƙaƙiya, yadda za mu fahimta. Yau dai a karo na farko, ka yi mana wannan alfarmar.”
Alhudahuda ya yi murmushi, sannan ya ce:
“Bainu kar ki bari zancen ‘yan duniya ya ruɗe ki. Ni ɗin nan ina ƙoƙari ƙwarai da gaske don ganin an fahimci zancena, kawai dai akasi ake samu. Yanzu dai tun da an buƙaci in ce wani abu a kan wannan abu da Jemage ya yi, to a yi mun afuwa, in ɗan karanto maku kaɗan daga cikin abin da na rubuta a ‘Diary’ na.”
Ya janyo wani ƙaton littafi duk ya yi ƙura, ya kaɗe shi, ya ɗauko tabarau ya ƙwama, sannan ya buɗe littafin, aka karkace aka fara karanto wa tsuntsaye abin da aka rubuta kamar haka:
“The Higgeledy-Piggidly Portfolio Appointments
The recent trend of appointing ministers by Jemage with little or no experience in their respective ministries has raised significant concerns about the effectiveness of governance. The term “heggedily-piggidly” aptly captures the chaotic and disorganized nature of these portfolio assignments, which undermine the very foundations of a well-functioning government.
The haphazard allocation of portfolios without regard for expertise has resulted in jumble approach to governance. It is alarming to witness ministers being placed in charge of crucial sectors where their knowledge and experience are sorely lacking. This approach not only handicaps the potential progress of these ministries but also casts doubts on the intentions behind such appointments…”
“Dakata haka! Mun fahimci matsayarka, mun gode, domin idan muka zuba maka ido sai a kai asuba ba ka tsaya ba. Mu ko bacci muke ji.” Tattabara ta katse shi.
Tsuntsaye suka yi sallama, kowa ya nufi sheƙarsa.
*Sai dai an samu rahoton balbelu sun fara lissafin yadda za su kasafta sulallan da Jemage ya ba su don a ragewa tsuntsaye raɗaɗin cire tallafin makamashin zirga-zirga.
~~~~~~~
Malam Mukhtar Mudi Sipikin, marubuci, sha’iri, ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa ne. Ya rubuto wannan shaguɓe daga Kano.
~~~~~~~












