Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
A ranar Asabar mai zuwa, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Dr. Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci taron ƙaddamar da manyan littattafai biyu, waɗanda suke ƙarfafa muhimmancin da’awa a kafafen sadarwa na zamani. Taskar Gizago ta tattauna da marubucin littattafan biyu, Malam Aliyu Ibrahim Sani Mainagge, dangane da littattafan da kuma yadda taron zai gudana, da sauran muhimman batutuwa da suka shafi Musulunci, wallafa da da’awa. Ga yadda tattaunawar ta gudana:
__________
Ka ba mu tarihinka a taƙaice.
Malam Aliyu: Sunana Aliyu Ibrahim Sani Mainagge. Ni marubuci ne kuma mai fassara littattafai, tare da sha’awar ayyukan da suka shafi yaɗa ilimi, da’awar Musulunci, tarbiyya, tattalin arziki, kafofin sadarwa da ci gaban al’umma.
Ni ne wanda ya kafa kamfanin ALI BABA PRESS, mai wallafawa da buga littattafai a harshen Hausa, Larabci da Turanci.
Na shafe shekaru ina gudanar da ayyukan rubuce-rubuce da fassara, musamman a fannin ilimin addinin Musulunci. Daga cikin manyan ayyukan da muka gudanar akwai fassarar Tafsirin Ibn Kathir cikin mujalladi goma sha biyu, waɗanda suka ƙunshi kusan shafuka 6,000. Na kuma yi ayyuka tare da hukumomi da ƙungiyoyin ci gaban al’umma na cikin gida da na waje, da nufin bunƙasa ilimi da kyautata rayuwar al’umma.
Babban burina shi ne in taimaka wajen samar da ilimi mai amfani, ƙarfafa da’awar Musulunci da rubuce-rubuce, tare da samar da hanyoyin da za su taimaka wa al’umma wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa.
Ya zuwa yanzu, littattafai nawa ka wallafa?
Malam Aliyu: Ya zuwa yanzu, na rubuta, na fassara kuma na samar da littattafai masu yawa a fannoni daban-daban na ilimin addinin Musulunci, da’awa, tarbiyya da ci gaban al’umma.
Daga cikin manyan ayyukana, akwai fassarar Tafsirin Ibn Kathir cikin mujalladi goma sha biyu mai kusan shafuka 6,000 da sauran littattafan da suka shafi rayuwar Musulmi da ci gaban al’umma.
Haka kuma, a matsayin kamfanin wallafa littattafai, ALI BABA PRESS na ci gaba da samar da littattafan da za su taimaka wajen yaɗa ilimi da wayar da kan al’umma.
Game da adadin littattafan da aka wallafa sun haɗar da na tarihin Musulunci tun daga Tarihn Annabi (SAW), wanda masana suka ce shi ne irinsa na farko a harshen Hausa. Da Tarihin Sahabban Manzon Allah (SAW) da aka buga litattafin MAFIFITAN MUTANE SAHABBAI (100) na Maza da MAFIFITAN MATA SAHABBAI (100). Da Tarihin Halifofi da ya ba da tarihin Halifofi (4) na Manzon Allah (SAW) da Tarihin Musulunci a Karni na Ashirin (20). Haka kuma mun yi fassarar littafin Shahid Hasanul Bannah; Risalatut-Talim da Al-Ma’athurat da littafan Imamul Ghazaliy: Ayyuhal Walad da Hikimomin Allah Cikin Halittar Ɗan Adam da sauran littatafai masu yawa. Yanzu haka ma muna rubuta littafin Tarihin SHEHU USMAN ƊAN FODIYO da Gwagwarmayar Kafa Daular Musulunci, wanda muke sa ran mayar da shi fim a ƙarƙashin talabijin ɗinmu ta TAJDID TV.
Ka yi mana bayani a taƙaice game da ƙunshiyar waɗannan littattafai biyu da za a ƙaddamar.
Malam Aliyu: Littattafan biyu da za a ƙaddamar, sun ta’allaƙa ne da muhimman ginshiƙai guda biyu da muke ganin suna da matuƙar tasiri wajen ci gaban Da’awar Musulunci a wannan zamani, kafofin sadarwa da tattalin arziki.
Littafi na farko shi ne, AMFANIN KAFOFIN SADARWA WAJEN YAƊA DA’AWAR MUSULUNCI. Wannan littafi ya yi bayani ne kan muhimmancin amfani da kafofin sadarwa wajen yaɗa saƙon Musulunci da isar da ilimi ga al’umma. Ya tattauna hanyoyin amfani da rediyo, talabijin, jaridu, mujallu da kafafen sada zumunta na zamani, kamar Facebook, WhatsApp, YouTube, TikTok, Instagram da Telegram da saurasu.
Manufar littafin ita ce, wayar da kan malamai, masu Da’awa da sauran al’umma game da yadda za a yi amfani da waɗannan kafafe cikin hikima, tsari da bin ƙa’idojin Musulunci, domin yaɗa gaskiya, ilimi da kyawawan ɗabi’u.
Littafi na biyu shi ne, AMFANIN TATTALIN ARZIKI WAJEN GINA DA’AWAR MUSULUNCI. Wannan littafi ya mayar da hankali ne kan muhimmancin tattalin arziki wajen ginawa da tabbatar da ɗorewar ayyukan da’awa. Ya bayyana yadda samar da kuɗaɗen shiga na halal da gudanar da dukiya yadda ya dace, taimakon juna, sadaka da waƙafi za su taimaka wajen gudanar da ayyukan da’awa cikin inganci da ɗorewa.
Littafin ya kuma jaddada buƙatar ƙungiyoyin da’awa su samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga masu ɗorewa, maimakon dogaro da gudunmawar lokaci-lokaci kawai ko dogaro da tallafn ƙasashen waje.
A taƙaice, littattafan biyu suna koyar da cewa yaɗa da’awa yana buƙatar ingantacciyar hanyar isar da saƙo da kuma ingantaccen tsarin tattalin arziki da zai ɗauki nauyin wannan saƙo.
Ka yi mana bayani game da rana, lokaci da wurin ƙaddamarwar. Haka kuma, ka bayyana wasu daga cikin manyan mutanen da aka gayyata kuma ake sa ran za su halarci taron.
Malam Aliyu: An tsara gudanar da bikin ƙaddamar da littattafan ne in sha Allahu kamar haka: Rana: Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026. Lokaci: Ƙarfe 9:30 na safe. Wuri: Makarantar Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies (Legal), Kano.
Taron yana da muhimmanci ba kawai a matsayin bikin ƙaddamar da littattafai ba, har ma a matsayin wata dama ta tattauna hanyoyin inganta Da’awar Musulunci ta fuskar sadarwa, tattalin arziki da haɗin gwiwar al’umma.
Daga cikin manyan baƙi da aka gayyata ko ake sa ran halartar su, akwai Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ya amince da gudanar da taron ƙaddamar da littattafan, tare da wakilcin Mai Girma Wazirin Kano Alhaji Sa’adu Shehu Giɗaɗo.
Akwai Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hon. Murtala Sule Garo, wanda ake sa ran halartar sa a matsayin Babban Baƙo Na Musamman.
Akwai Mai girma Shugaban Karamar Hukumar Gwale, Hon. Abubakar Mu’azu (Mojo), a matsayin Babban Baƙo
Akwai Mai Girma Kwamishinan Lamurran Addini na Jihar Kano, Dr. Tijjani Sani Auwal a matsayin Shugaban Taro.
Alhaji Ibrahim Sabi’u (Linda), wanda aka tsara ya kasance Babban Mai Ƙaddamar da littattafan. Akwai Dr. Ali Tamasi Mu’azu, Provost na Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies, Kano a matsayin Babban Mai Masaukin Baƙi. Akwai Sheikh Aminu Aliyu Gusau (Modibbo Gusau), wanda aka gayyata a matsayin Babban Malami Mai Jawabi I. Akwai Sheikh Muhammad bn Uthman, wanda aka gayyata a matsayin Babban Malami Mai Jawabi II.
Haka kuma, ana sa ran halartar malamai, shugabannin hukumomi da ƙungiyoyi, masu da’awa, marubuta, ’yan jarida, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi da ci gaban al’umma.
Muna fatan taron zai zama wata dama ta haɗa kan malamai, shugabanni, mawadata da sauran masu kishin ci gaban al’umma domin tattauna yadda za a inganta ayyukan Da’awa da samar musu da hanyoyin ci gaba masu ɗorewa.
Wane kira ko nusarwa kake da shi ga al’umma gaba ɗaya dangane da waɗannan littattafai biyu?
Malam Aliyu: Kirana ga al’umma, musamman malamai, masu da’awa, shugabannin ƙungiyoyi, ’yan kasuwa, masu hannu da shuni da matasa shi ne, mu fahimci cewa ci gaban Da’awar Musulunci ba zai dogara da himmar malamai kawai ba; yana buƙatar haɗin gwiwar kowa da kowa.
A yau, muna rayuwa ne a zamanin da kafofin sadarwa suke da matuƙar tasiri wajen gina tunanin al’umma. Idan ba mu yi amfani da su yadda ya dace wajen yaɗa ilimi da kyawawan ɗabi’u ba, to, za mu bar wasu su yi amfani da su wajen yaɗa saƙonnin da ba su dace da addininmu da al’adunmu ba.
Haka kuma, ayyukan da’awa suna buƙatar kuɗaɗe domin buga littattafai, gudanar da makarantu, shirya tarurruka, samar da kafafen sadarwa da tallafa wa malamai. Saboda haka, wajibi ne mu haɗa himmar da’awa da kyakkyawan tsarin tattalin arziki.
Ina kira ga masu hannu da shuni da ’yan kasuwa da su ɗauki tallafa wa ilimi da wallafa littattafai a matsayin wata hanya ta saka jari a cikin al’umma da neman lada a wajen Allah.
Ina kuma kira ga malamai, ɗalibai da sauran masu son ilimi da su karanta waɗannan littattafai, su tattauna abubuwan da ke cikinsu, sannan su yi amfani da shawarwarin da suka dace wajen inganta ayyukansu.
A ƙarshe, ina kira ga al’umma da su ba da gudunmawa mai ma’ana wajen tallafa wa ƙaddamar da waɗannan littattafai da yaɗa su a tsakanin al’umma. Gudunmawar ba kuɗi kaɗai ba ce; tana iya kasancewa ta hanyar sayen littattafan, tallata su, rarraba su ga makarantu da ɗakunan karatu, ko taimakawa wajen isar da saƙonsu ga waɗanda za su amfana.
Manufarmu ba ita ce ƙaddamar da littattafai kawai ba amma ita ce tabbatar da cewa ilimin da ke cikinsu ya isa ga al’umma, ya haifar da sauyi mai kyau kuma ya taimaka wajen gina Da’awar Musulunci bisa ingantaccen ilimi, kyakkyawan tsari da ɗorewar tattalin arziki.
Ina roƙon Allah ya sanya wannan aiki ya zama mai amfani ga Musulunci da Musulmi, ya albarkaci waɗanda suka taimaka wajen samar da shi, kuma ya ba mu ikon amfani da ilimin da muka samu wajen kyautata rayuwarmu da ta al’umma.
Na gode.
__________












