ALI BABA: Tattaunawa Ta Musamman Da Marubucin Littattafan Musulunci
~~~~~~~
Malam Aliyu Ibrahim Sani Mainagge, wanda aka fi sani da laƙanin ALI BABA, na ɗaya daga cikin marubutan da ke faɗakar da al’umma kuma ya rubuta littattafai da maƙaloli da dama. A tattaunawarsa da Taskar Gizago, ya bayyana tarihinsa da kuma irin faɗi tashin da ya sha a fagen rubuce-rubuce. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
~~~~~~~
TG: Kana ɗaya daga cikin marubutan Hausa a wannan zamani. Ko za ka gaya mana tarihinka a taƙaice?
MALAM ALIYU: Alhamdu lillahi! Sunana Aliyu Ibrahim Sani Mainagge. A gida ana kira na Baba Ali ko Ali Baba saboda an sanya mini sunan kakana ne, don haka Babata (Allah Ya yi mata rahama) take ce mini Baba, sauran maƙwabta kuma su haɗa su ce Baba Ali, daga baya ya koma Ali Baba.
An haife ni a Unguwar Sani Mainagge da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a garin Kano, kimanin shekaru 47 da suka gabata. Na halarci makarantar Alƙurani ta Malam Umaru Bakatsine, wanda shi ne malaminmu na farko (Allah Ya ƙara masa lafiya, Allah saka masa da alheri), da Malam Kamilu (Allah Ya ƙara masa lafiya da imani da nisan kwana), da ke nan unguwarmu ta Sani Mainagge, inda na kammala saukar karatun Alƙurani mai girma. Sannan na yi karatun addini a wurin malamai masu yawa da suka haa da Malam Lawan Tela (Allah Ya gafarta masa) da Malam Sani Aliyu Sani Mainagge da Malam Yahaya Hassan Gwale da Malam Muhammad Aminu S/Mainagge. Haka kuma na yi karatu a wuraren malamai masu yawa da suka haɗa da Malam Ismaila Sabon Titi da Gwani Dokta Rufai Uba Hamza Gabari da Dokta Ibrahim Muazzam Mai Bushra, tsohon Shugaban Sashen Addini da Shari’ah na Jamiar Bayero ta Kano da kuma marigayi Malam Baffa Aminu, tsohon Daraktan Sashen Addinin Musulunci na Maaikatar Ilmi ta Jihar Kano (Allah ya ji ƙan sa, Allah Ya gafarta masa). Duka waɗannan malamaina ne kuma ina alfahari da su ƙwarai da gaske.
A ɓangaren Nizamiyya, na halarci Makarantar Firamaren Maitasa da Ƙaramar Sakandiren Sabuwar Ƙofa da Kwalejin Horar da Malamai ta Gwale da Babbar Sakandiren Gwauron Dutse da Jamiar Bayero ta Kano, inda na yi digiri na farko a Ilmin Addinin Musulunci da Tarihi.
Tun daga shekarar 1996, kimanin shekaru 27 ke nan zuwa yanzu ina aiki da Hukumar Ƙananan Hukumomi ta Jihar Kano, inda nake aiki a halin yanzu a Sashen Walwala da Jin Daɗin Jama’a, a Ƙaramar Hukumar Gwale.
Haka kuma ni malamin makarantar Islamiyya ne na shekaru masu yawa, inda na yi koyarwa a Makarantun Tarbiyyatul Umma Gyaɗi-Gyaɗi da Anas Ibn Malik S/Mainagge da Ƙadi Ahmad Islamiyya Rimin Gata, duka a garin Kano. Sannan na na kafa Makarantar Haddar Alƙurani ta Darul Imara da ke Unguwar Ɗorayi Babba, daura da Titin Gwarzo a Rijiyar Zaki.
Haka kuma a shekarar 2014 na kafa kamfanin wallafa na ALI BABA PRESS, kamfanin da ke wallafa tare da fassara da gyara littattafai (Editing) a harshen Larabci da Turanci da Hausa.
A ɓangaren iyali, ina da mata uku da yaya goma sha biyu rayayyu.
TG: Tun yaushe ka fara harkar rubutu? Kuma me ya ja raayinka ga harkar rubuce-rubuce?
MALAM ALIYU: Kamar yadda na taɓa faɗa wa Gidan Rediyon Rahama da ke Kano da kuma Jaridar Aminiya, tun ina ƙarami a makaranta Allah Ya sanya mini shaawar yawan karance-karance, wanda kuma shi ya sanya na kasance marubuci.
Babban abin da ya ja hankalina zuwa rubutu, musamman littattafan addini shi ne tasirantuwa da ayyukan ci gaban addini da kuma taimakon alummarmu. Ban taɓa yin shaawar yin rubutu da ba na addini ba.
TG: Ya zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda, da kuma nawa ka buga a intanet?
MALAM ALIYU: Na fara rubuta littafina na farko kimanin shekaru 25 ko makamancin haka da suka gabata. Littafin da na fara rubutawa shi ne SIFFOFIN MUTANEN KIRKI, amma Allah bai sanya ya ga hasken rana ba, har takardun suka ɓace. Bayan wannan sai na rubuta littafin TAFARKI MADAIDAICI A CIKIN SANIN ILMIN ALƘURANI. Littafi ne da ke magana akan Alƙurani da iliminsa da siffofinsa da falalar karanta shi da ƙirao’i da makamantansu. Shi wannan littafin an buga shi ya fita kuma alumma da yawa sun amfana da shi, Alhamdu lillahi!
Haka kuma mun yi haɗin gwiwa ni da Malam Usman Musa Gabari (Khalifa) muka rubuta littafin Tarihin Manzon Allah (SAW) mai suna MUHAMMAD (SAW) RAHAMA GA TALIKAI, wanda Farfesa Auwal Abubakar na Jamiar Bayero ta Kano, a gabatarwar da ya yi wa littafin yake cewa, Shi ne irinsa na farko a Harshen Hausa. Daga nan sai littafin HALIFOFI SHIRYAYYU. Shi kuma yana ba da tarihin Halifanci na shekaru (30), an buga shi kuma jaridar Albishir ta kamfanin Triumph ta dinga buga wasu sassa daga cikinsa, shekaru da suka gabata. Sai littattafan Mafifitan Mutane SAHABBAI (100) na maza da mata, littattafan da Allah Ya sanya musu albarka ƙwarai da gaske, alumma masu yawa suka amfana da su. Kuma har yanzu ana ci gaba da yaɗa littafan ta hanyar kafofin sadarwa na zamani. Sai Tarihin Zaɓaɓɓun mutane ANNABAWA (25) Adam (AS) zuwa Muhammad (SAW). Wannan har yanzu bai fita ba, sai dai a shekarun baya an dinga wallafa wani sashensa ana bugawa a jaridar Attajdid. Sai AHLUL BAITI: IYALAN BABBAN GIDA da DUJAL BABBAR FITINA, sai kuma littafin SALLAH GINSHIƘIN ADDINI, wanda shi ma Allah bai sanya ya fita ba. Haka kuma na rubuta littafin HAJJI: GA WANDA YA SAMI IKO, shi ma an yi amfani da shi shekaru masu yawa. A shekarar 2010 na fara FASSARAR TAFSIRIN IBN KATHIR, wanda aka xauki shekaru kimanin shekaru goma ana aikin, kuma Alhamdulillahi! zuwa yanzu an sami nasarar kammala rubutun gaba ɗaya, tare da fito da Juzi na farko da ke ƙunshe da izifi biyar kuma yake ɗauke da kimanin shafi 500. Haka kuma an buga izifi ashirin a mujalladai guda huɗu, kuma zuwa yanzu muna ta ƙoƙarin ganin an buga littafin izifi 60 gaba ɗaya, wanda ake sa ran fitowarsa a mujalladai goma da ke da shafi kimanin dubu biyar. Haka kuma na rubuta littafin TARIHIN MUSULUNCI A ƘARNI NA ASHIRIN (1900-2000). Shi ma ba a iya buga shi ba zuwa yanzu.
Haka kuma na fassara littafin MAATHURAT na Shahid Hasanul Banna da RISALATUT TAALIM da muka fassara tare da Malam Umar Shehu Tsakuwa.
Haka kuma na rubuta maƙalu da yawa da aka gabatar a wasu tarurruka wasu an buga su, wasu kuma ba a buga su ba.
Kuma kamar yadda na faɗa a baya kamfaninmu na wallafa, ALI BABA PRESS na yin ayyuka masu yawa na wallafa da gyara (editing) da fassara littattafai. Mun yi aikin tattara fassarar Sahihul Bukhari na Jamiar Bayero ta Kano kuma mun fara aikin tattara Tafsirin Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi zuwa littafi, wanda ba a iya kammala aikin ba saboda wasu matsaloli.
TG: Waɗanne irin matsaloli ka fuskanta a matsayinka na marubuci?
MALAM ALIYU: Matsalolin ba su wuce waɗanda kowane marubuci ko duk wani mai manufa a rayuwarsa yake fuskanta ba. Duk da haka ina godiya ga Allah bisa karamcinsa, domin rubuce-rubucena suna samun tagomashi a wurin alumma. Muna roƙon Allah Ya karɓa mana. Kuma na sami tallafawar mutane masu yawa da ba zan manta gudunmawarsu game da waɗannan rubuce-rubuce ba. A gaba-gaba akwai Alhaji Imam Ahmad Zubair, mni da marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji (Dokta) Ado Bayero (Allah Ya yi masa rahama), wanda shi ne ya fara ɗaukar nauyin fara buga mana littafinmu na Tarihin Annabi Muhammadu (SAW), da Dokta Bashir Shehu Galadanci, wanda shi ya fara ɗaukar nauyin buga littafinmu na Sahabbai (100), a lokacin yana Babban Mai Ba Gwamna Shawara Kan Ilimi da Sabuwar Fasahar Sadarwa a Jihar Kano da Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi da Mai girma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ya fara buga izifi biyar na littafin Fassarar Tafsirin Ibn Kathir da Alhaji Sammani Adamu (El-Samad) da kuma Alhaji Nuumanu Barau Ɗanbatta, wanda shi ne ya buga mana izifi ashirin na Fassarar Tafsirin Ibn Kathir da kuma Alhaji Sani Baba Bauchi da sauran mutane masu yawa. Allah Ya saka musu da alheri.
TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori ka samu ko kuma akasinsu?
MALAM ALIYU: Ina ji a raina cewa, Allah Ya yi min babban karamci da ya sanya ni a sahun marubuta na addinin Musulunci. Mutane da yawa ma suna alfahari da cewa sun san ni a matsayina na marubuci, don haka ina farin ciki da jin daɗi da ɗimbin nasarori da ba za su ƙididdigu ba. Idan na waiga baya na ga yadda tafiyar take, ina ƙara gamsuwa da jin daɗi da godiya ga Ubangijina, kuma ina fatan zai ci gaba da taimaka mana wajen wannan aikin
TG: A harkar rubuce-rubuce waɗanne marubuta ne gwanayenka da kake koyi da rubutunsu?
MALAM ALIYU: Gaskiya gwanayena a harkar rubutu suna da yawa, amma dai daga cikinsu akwai Malam Abubakar Imam (Allah Ya yi masa rahama). Ba shakka ya yi matuƙar tasiri a rayuwata da kuma Malam Bature Gagare marubucin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa (Allah Ya yi masa rahama) da abokina Malam Usman Musa Gabari (Khalifa) da Malam Bashir Tofa (Allah Ya yi masa rahama). A waje kuma akwai Dokta Yusuful Ƙardhawiy (Allah Ya yi masa rahama) da Dokta Muhammad Bakar Ismail da Dokta Aliyu Muhammad As-Sallabi. Allah Ya saka musu da alheri.
TG: Ya zuwa yanzu wane sabon littafi kake kan rubutawa kuma zuwa yaushe zai fita ga alumma?
MALAM ALIYU: Duk da yake yanzu akwai ayyuka masu yawa da suka sha kaina, amma har yanzu akwai littattafai da nake mi kan aikinsu. Ina ci gaba da gyaran Fassarar Tafsirin Ibn Kathir, haka kuma ina aikin wani littafi a kan Darussan Tarihin Annabi Yusuf (AS) da kuma wani littafi a kan Waƙafi. Haka nan ina aikin Fassarar Tafsirin Shehu Ibrahim Inyas mai suna Fi Riyadhit Tafsir.
TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko kai ma kana da shirin rubuta wani littafi na faɗakarwa da za a maida zuwa fim?
MALAM ALIYU: Duk da yake dai ni na fi ƙarfi a harkar rubutun addini, amma idan yanayi ya samu, zan iya rubutu da za a iya amfani da shi wajen shirin fim. A baya ma akwai wani Producer da ya nemi shirya fim da littafinmu na DUJAL, kuma ban ƙyamaci hakan ba, sai dai kawai abin ne bai yiwu ba.
TG: Mene ne babban burinka dangane da rubutu?
MALAM ALIYU: Babban burina dangane da rubutu shi ne neman yardar Allah. Ƙananan burikan kuma ba su wuce ganin waɗannan rubututtukan sun yaɗu a cikin alumma ana amfana da yan gudunmawar da muka bayar ba, musamman ma dai na ga an buga cikakken kammalallen littafin FASSARAR TAFSIRIN IBN KATHIR da yardar Allah.
TG: Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta yan uwanka da kuma alumma masu karanta littattafanka?
MALAM ALIYU: Kira na ga marubuta, mu sake dagewa, tare da neman taimakon Allah. Ba wani abu mai muhimmanci da yake iya yiwuwa cikin sauƙi, sai an yi gwagwarmaya, an dage sannan ake cin nasara. Haka kuma ina kira ga gwamnatocinmu da attajirai da sauran

alumma da cewa su sanya hannunsu cikin waɗannan ayyuka na alheri, aikin addinin Musulunci da ci gaban alumma kama in kama ne, da haka sai ka ga an ci nasara baki ɗaya, alumma ta burunƙasa.













