KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Daga Mukhtar Mudi Sipikin
A ranar Asabar, 29/072023, Shanshani na ta laluben kurtun magana, sai ya ankara da giccin wani muhinmin sako ya sauka cikin akwatinsa na Whattsapp. Nan da nan ya bude, sai ya iske ashe Malam Na Fagge ne ya rubuto masa dogon tsokaci, wanda ya kalato daga Fadar Tsuntsaye. Ga abin da yake cewa:
~~~~~~~~
Kamar dai kullum, tsuntsaye sun taru a mahaɗa ana ta tattauna lamarin da ke wakana a Daji, da kuma yadda tsare-tsaren Shugaba Jemage ke ƙara cilla dubban tsuntsaye cikin halin ha’u’la’i da ƙaƙa-n-ka-yi da ake ciki, har dai aka zo maganar Yautai mugun tsuntsu da yadda lamura suka canza masa.
Kurciya cikin mamaki ta kalli tsuntsaye, ta ce: “Duniya juyi-juyi! Wai yau har rigima ake tsakanin Shirwa da Mikiya a kan wa zai kama Yautai, ya ajiye shi a wajensa. Ku tuna fa lokacin da Yautai ya yi ta cin karensa ba babbaka, haka kawai ana zaman lafiya, Yautai ya ce sai ya canza fasalin sulallan Dajin nan, tsuntsaye suka shiga cikin bala’i. Amma Yautai bisa goyon bayan Babba-da-jaka, suka kau da kai akai ta shan wahala.”
Hazbiya ta karɓa da cewa: “Ai Yautai cutar da ya yi a dajin nan ga tsutsaye ba zai misaltu ba, sai dai mu ce Allah Ya saka mana abin da ya yi mana, da shi da wanda suka mara masa baya.”
Salwa ta ce: “Wai kuwa ya labarin sunayen mataimakan da Jemage ya tura majalisar su Ragon-Maza ne? Sunayen su waye ya fito? Kun san ni ba bibiyar labaru nake ba, sannan ba na sauraron fashin baƙin masana, wato “Experts” don zai iya kai ni ga haɗiyar zuciya.”
Hazbiya ta ce: “Ni fa na yi zaton Jemage a shirye yake, don ban taɓa tunani za kai har yanzu ba a gama da wannan lamarin ba, sai ga shi ya ba ni mamaki. Yanzu dai an ce sunayen tsuntsaye 28 ya fito, ga kaɗan daga cikin sunayensu:
Gauraka
Carki,
Shamuwa,
Zabuwa,
Birbiri,
Shaho,
Mujiya,
Cakwaikwaiwa,
Jimina,
Ɗan Tsako,
Aku,
Agwagwa,
Talo-Talo,
Makwarwa…”
“Dakata Hazbiya! Na ji kina ta lissafo sunaye, amma har yanzu ban ji kin kama sunan Shugaban Rundunar Jan-Baki ba, sannan kuma ban ji kin faɗa mana makomar Ungulu ba, tana cikin jerin sunayen nan ko kuwa?” Tattabara ta katse ta.
Hazbiya ta amsa da cewa: “Tattabara kin fiye azarɓaɓi da gaggawa wallahi, da kin yi shiru da za ka ji ƙarshen yadda lamarin zai kasance! Shi Shugaban Rundunar Jan-Baki, har yanzu lamarinsa bai bayyana sosai ba, kawai dai Rundunar Jan-Baki ne ke fatan shugabansu ya yi shan kai, duk da dai ba da shi aka je yaƙi ba, ita kuma Ungulu ana tunanin ba za ta tsallake tantacewa daga ‘yan Majalisar Ragon-Maza, ba tare da cece-kuce ba, sannan kin san akwai daftarin madubi da ya bayyana a majigi zai iya kawo masa cikas, don haka an ce za a naɗa shi shugaban tsuntsaye masu riƙon tsintsiya na dajin nan gaba ɗaya.”
Gado ya juya ya kalli, Alhudahuda, wanda tunda aka fara hira bai ce komai ba; ya ce: “Malam Alhudahuda me za ka ce game da wannan tsuntsaye da Jemage ya naɗa?”
Alhudahuda ya yi gyaran murya ya ce: “The prognostication of the potential ramifications attendant to the appointment of matamaikan Jemages is currently inchoate, as it hinges upon the forthcoming revelation of their respective portfolios, elucidating their precise spheres of influence within the governmental apparatus.
“The veritable consequences are contingent upon the nature of their designated….”
Ganin dai Alhudahuda ya fara ɗaukar zafi, tsuntsaye suka tashi, kowa ya yi hanyar sheƙa. Suka bar shi yana ta zuba Turanci shi kaɗai.
~~~~~~~
Malam Mukhtar, marubuci, dan siyasa kuma dan kasuwa ne a Kano.
~~~~~~~












