HAWAYE DON AFIRKA
Daga Dokta Hadiza Nuhu, OON
~~~~~~~
A yayin da ake ta laluben hanyoyin samun maslaha tsakanin Ƙungiyar ECOWAS da Sojojin da suka hamɓarar da Gwamnatin Farar Hula a Jamhuriyyar Nijar, ita kuwa Dokta Hadiza Nuhu, OON alƙalami ta ɗauka ta zubar da hawayen takaici domin ceto Arewa da Niger da Nigeria da ma Afirka gaba ɗaya

daga makircin ‘yan duniya da ke son jefa al’ummarta cikin uƙubar yaƙi. Ga baitukan, kamar yadda ta rero su:
~~~~~~~
Bismillah Rabbi Sarki Tabaraka,
Ga ni ɗauke da baituka,
Ba ni hikima da ɗaukaka,
Zan zo da zance na ECOWAS.
Na yi salati ga Hamidu,
Muhammadu Manzo Mujaddadu,
Shi ya yi yaƙi da hakidu,
A cikin aiki na ECOWAS.
Jama’a ku ba ni kunnuwa,
Ga Nijar ana kururuwa,
An tsananta dukkan abubuwa,
A yunƙurinsu na ECOWAS.
Ga sojoji da bindiga,
Sun sheƙo za su daddaga,
Ta Nijar sun ka ɓuɓɓuga,
Niyyarsu AREWA ECOWAS.
Mun gane wayon da jijjifi,
Arewa a take da yayyafi,
Da ruwan bala’in ƙarfi.
Mun gane hila ta ECOWAS.
Tarenmu ce za a wargaza,
An fake don rugurguza,
An kitso girin ragargaza,
Sai anka ɓullo ta ECOWAS.
Sabonsu kullum su ɓarnata,
Kuka ake babu kurumta,
Duniya duk an maganta,
Su ba ruwansu ECOWAS.
Shin ita ba ƙungiya ce ba?
Ta haɗin kan ƙasar baba?
Jimilla sha biyar duba?
Ƙasashenta ita ECOWAS?
Ita ba mai tallafi ce ba?
Don ci gaban ƙasashen ba?
Ba ta cin zarafi ce ba?
Shin ina manufarta ECOWAS?
Ya za ta juye da yaudara?
Za tai yaƙi cikin gadara?
Da ‘yan gidanta tsirara?
Ko wannan shi ne ECOWAS?
Shin ko ‘yar kanzagi ce?
Ta tsofaffin fatake ce?
Sanannun masu ƙwace?
Kar fa a yaudare ki ECOWAS!
Su fa ‘yan duniya jari ne.
Aikinsu zamba yaudara ne,
‘Yan mallaka da ƙwace ne.
Gara ki farka fa ECOWAS.
Aikinsu su dai su bautar,
Dukiya sun ka ƙwatar,
Ƙasashenmu sun durƙusar,
Lallai ki guje su ECOWAS.
Sun kashe ‘yan kishin ƙasa,
Masoyanmu a cikin ƙasa,
Janar Murtala mai ƙasa.
To a hir ɗin ki ECOWAS.
Mu’ammar Gaddafi jarumi,
Thomas Sankara hakimi,
Mun rasa su sai jimami,
Ko kin manta ne ECOWAS.
Su ne dillalan makamai,
Masu rarraba mukamai,
Sun haddasa yaƙi maimai,
Ba za mu amince ba ECOWAS.
Ga su nan suna ta leƙe,
Sun biyo mu a hayyaƙe,
Mu bar waige ido mu feƙe,
Mu san sirrinsu ECOWAS.
Akwai ‘yan kanzagin cikinmu,
Shugabanni ruɓabbun wajenmu,
Kwaɗayinsu sui ta mulkinmu,
Ba kishin ƙasa ba ECOWAS.
Ba ruwansu da talakka,
Suna tai masa takakka,
Talauci yunwa makaka,
Ki buɗe idonki ECOWAS.
Babu tsaro a cikin ƙasa,
Sun hana illimin matasa,
Ba aiki sana’a ‘yan ƙasa,
Ya kaiconmu kin ji ECOWAS.
Wallahi duk gwanin tausayi,
Jama’a mu yo tsinkayi,
Salon bauta cikin laulayi,
Habawa ke ko ECOWAS!
Kai waɗannan shugabanni,
Ko mu kira su “wau-gabanni”
Burinsu su sa mu cikin bani.
Ina kike ne yanzu ECOWAS?
Sun kira kuraye daga sassa,
Ga Babbar Fara Farar Saa
Mabiyarta Marka tasa,
Kin san da zamansu ECOWAS.
Ga algunguma ita Guila,
Za tai mana kisan gilla,
Sun haɗa kai sun ƙulla,
Sun shigo su ta ECOWAS.
Fafiratan ba mu yarda ba.
Nijar da mu gida babba
Tun Marka ma ba ta zo ba,
Gidan duniya bare ECOWAS.
Mujaddadi can ya faru,
Aikinsa sai ka ji ƙaru,
‘Yan mallaka sun ka taru,
Sun ka raba mu ECOWAS.
Sunka haɗa mu da bare,
Su masu ɗaukar taɓare
Zage-zage halinsu zare,
Zo ki gane ke ECOWAS.
‘Yan Nijar akwai halacci,
Ba su batu na ƙasƙanci,
Babu ruwansu yin butulci,
Suna son mu kin ji ECOWAS.
Su ‘yan uwa ne a Musulunci,
Shacin iyaka bai halacci,
Iyakar ta mallakar ƙunci,
Ba mai raba mu ECOWAS.
Ku ‘yan Arewa ga gargaɗi,
Ɓatan ɓaƙatantan ba daɗi,
Ku rasa Kuɗun can tabɗi!
Ku rasa Nijar ga ECOWAS.
Allah ni dai na yi roƙo,
Dunƙule mu kamar ƙoƙo,
Nijar da Arewa ƙara maiƙo,
Na zumunci ko babu ECOWAS.
Mu huce zagin Biyafarawa,
‘Yan Oduduwa ma sun taɓawa,
Mu ne abin ƙi Najeriyar Arewa,
Ga shi an zo da ECOWAS.
Kar mu sake mui butulci,
Nasara nufinsa ya yi ɓaci,
Ya shata layi don rabon ci,
Kar ki biya shi kin ji ECOWAS.
Duniya ta gan mu ɗinke,
Kar mu rabe don su banke,
Ɗaidaikunmu za su make,
Sannan su hada da ECOWAS.
Haba Tinubu mun ji haushi,
Kalamanka sun yi kaushi,
A kan Nijar har ka tashi,
Razana mu da ECOWAS.
Lallai ka sani shi zalunci,
Bai sa mulki yai inganci,
Tafi sannu kar kai ƙaskanci,
Kar ka biye wa ita ECOWAS.
Fara Fararsa da ita Marka,
Haɗa da Guila sai ka farka
Cin amana su sunka tafka.
Najeriyarka ta fi ECOWAS.
Najeriyarmu duk mun san ta,
Matsaloli duk sun cika ta
Nemo maganinsu don ta huta,
Ka ƙyale batun wofi na ECOWAS.
Yunwa fatara babu tsaro,
Watanka biyu duk ka faro,
Mulkinka yau mun ji tsoro,
Kana ta batu na ECOWAS.
Arewa dai tai maka gata,
Ta yi halacci babu rata,
Ta zabe ka jiya da gata,
Babu hannun ita ECOWAS.
Kai za ka kare dimokuraɗiyya?
Ka ƙyale Nijar ‘yantacciya
Ka dawo ta mu Jamhuriyya
Ka gyara ƙyale ECOWAS.
Ka sani yaƙi shi haɗari ne,
Arewa ba ta son yaki ne,
Da Nijar tun da ‘yan uwa ne,
Kar ka biye zugar ta ECOWAS.
Ni Khadijah na yi nawa,
Sai ku ƙara fahimtarwa,
Allah ka yi mana afuwa
Raba mu da makircin ECOWAS.
Haɗa kanmu duka cikin aminci,
Allah daɗo rahamarKa mai ci,
Ka wadata mu da abinci,
Ka warware tuggunta ECOWAS!
~~~~~~~













