Shekara 30 A Inuwar Aure: Fatan Alheri Ga Editan Rfi Hausa
A yau Litinin 29-12-1444 (Hijriyya), 17-07-2023 (Miladiyya), Babban-Editan Sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa, Rfi, Malam Bashir Ibrahim Idris da Uwargidansa suka cika shekara 30 cur a cikin Sunnar Aure.
Kamar yadda ya bayyana a turakarsa ta Facebook, shi da matar tasa sun yi aure ne a ranar 17-07-1993. Ya zuwa yanzu dai Allah Ya albarkace su da zuri’a.
A madadin ni kaina, Bashir Yahuza Malumfashi, Babban-Editan Jaridar Taskar Gizago da iyalina, ‘yan uwa da abokan arziki, muna yi wa Malam Bashir da iyalinsa fatan alheri. Haka kuma muna yi masu addu’ar Allah Ya ƙara masu ƙauna da arziki da lafiya da imani.













