Daga Bashir Yahuza Malumfashi
A Mako Ɗaya Kacal: Jami’an NDLEA Sun Yi Wawan Kamun Muggan Ƙwayoyi A Abuja, Lagos Da Sassan Nigeria


Jami’an Hukumar Yaƙi Da Tu’ammali Da Muggan Ƙwayoyin Ta Ƙasa (NDLEA) sun yi nasarar kama wani ɗalibi ɗan shekara 19, Benjamin Nnamani Daberechi, a Filin Jirgin Saman Ƙasa-da-Ƙasa na Nnamdi Azikiwe, Abuja, Nigeria, da ƙunshin ƙwayar methamphetamine mai nauyin kilogiram 7.2, da aka ɓoye a kwandon kifin miya, a yayin da yake ƙoƙarin fita da ita zuwa Turai, inda zai je ɗalibta.
Da yake bayyana waɗannan nasarori da hukumar ta samu ga ‘yan jarida, Daraktan Watsa Labarai Da Wayar Da Kan Jama’a na NDLEA, Mista Femi Babafemi ya ce jami’an nasu sun kama matashin ne a ranar Laraba da ta gabata (12-07-2027), a yayin da ake tantance fasinjojin da za su shiga jirgin Turkish Airlines mai lamba TK0624. Da farko an tambayi matashi Daberechi inda za shi, ya amsa da cewa zai je karatu ne ƙasar Cyprus amma da aka tsananta bincike a jikkarsa, sai aka gano ƙullin farin maganin mai nauyin kilogiram 7.2, a ɓoye cikin kifin miya. Bayan an auna da na’ura, sai aka samu tabbacin cewa muguwar ƙwayar Methamphetamine ce.
Ya ce haka kuma, jami’an na NDLEA da ke aiki a Mashigar Ruwa ta Tincan, sun sake samun nasara a ranar Talata da ta gabata (11-07-2023), inda suka kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 116.5, wacce aka ɓoye cikin jakunkuna, ƙasan ƙarafunan mota, a cikin kwantena mai lamba FCIU 8459700, wacce ke ɗauke da gwanjon motoci uku da aka shigo da su daga birnin Toronto na ƙasar Canada.
“Tsattsauran binciken haɗin gwiwa tsakanin jami’an NDLEA da Kwastam da DSS ne ya tabbatar da cewa, lallai waɗannan ƙunshi 233 da aka ɓoye cikin ƙarafunan mota, tabar wiwi ce,” in ji Darakta Femi.
Ya ci gaba da bayyana cewa, baya ga wannan nasara, a karo daban-daban, jami’an na NDLEA da ke Aikin Bincike Da Gudanarwa a Lagos sun daƙile wasu ɓata-gari da suka so shigo da ganyen wiwi ta hanyar amfani da kamfanonin aika saƙonni. A kan haka suka taɓa kama giram 336 na ganyen da aka ɓoye cikin na’urar kwamfutoci za a fita da su zuwa Dubai, suka kama mutumin da ake zargi, Ibrahim Analu, ɗan shekara 28, a Tashar Motar Iddo, Lagos, a yayin da yake shirin aika adadin wasu muggan ƙwayoyin guda 151,700 zuwa Kaduna. Haka kuma sun sake bankaɗo wani ƙullin ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 4.830 a wani kamfanin aika saƙonni, a wani jirgin ruwa da ya zo Nigeria daga birnin Douala na ƙasar Cameroon, zai wuce ƙasar Oman. An ɓoye ƙunshin ganyen ne cikin gwangwanaye 10 da ke ɗauke da tsimin gargajiya da ake kira da laƙanin Banga. Dukkansu an sanya su cikin wani katan.
A bayanin nasa ga ‘yan jarida, Femi ya ce: “Jami’anmu kuma sun yi nasarar cafke wata lauya da ke da zama a Unguwar Lekki, Lagos, mai suna Ebikpolade Helen, wacce ta ƙware a sana’ar haɗa abin sha da muggan ƙwayoyi. An kama ta ne a garin Awka na Jihar Anambra, inda dama an taɓa kama kilogiram 5 na tabar wiwi da kwalabe 12 na haɗin muggan ƙwayoyi a gidanta da ke unguwar ta Lekki.”
Wata nasarar da NDLEA ta samu a ranar Alhamis da ta gabata (13-07-2023), kamar yadda Darakta Femi ya bayyana, ita ce kama wani mai suna Abubakar Shuaibu, a Unguwar Cappa, kan titin Mushin/Oshodi da kwalabe 86 na sinadarin Kodin, mai awon lita 8.6, a cikin motarsa ƙirar bas Toyota mai lamba FFA 241 YB. An kama wasu ƙarin mutum biyu da ake zargi, Razak Ogunbo da Adeola Idowu a ranar Talata (11-07-2023) a Unguwar Ikorodu da lita 51 na lamurjen muggan ƙwayoyi. Kamar kuma yadda a ranar Laraba (12-07-2022) aka kama kilogiram 372 na tabar wiwi da kwalabe 48 masu adadin lita 48 na lamurjen muggan ƙwayoyi a gidan wani dilan muggan ƙwayoyi da ya tsere Unguwar Akala da ke Mushin a Lagos.
A jihar Ondo kuwa, jami’an NDLEA wani gida suka fafara, a Unguwar Ehin-Ala, Ƙaramar Hukumar Akure ta Kudu, inda aka cafke wani Abubakar Zayyanu Gyambar, mai shekara 28. An same shi da manyan jakunkuna masu nauyin kilogiram 1,944 na tabar wiwi. Inda kuma shi wani da ake zargi, Henry Wilson, mai shekara 50, aka kama shi a garin Ogume na Ƙaramar Hukumar Ndokwa ta Yamma, Jihar Delta da irin wannan taba mai nauyin kilogiram 216.5.
A Arewa kuwa, an kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 45.41 a hannun Adam Hassan, mai shekara 27 a kan hanyar Ingawa-Mani-Mashi, a Jihar Katsina, yana zuwa Jamhuriyar Nijar.
“An kama kilogiram 70 na wani sinadari daga hannun Mamman Nur Shettima, a ranar Asabar (15-07-2023), a kan hanyar Kano zuwa Nguru, Jihar Yobe.”
A Jihar Kano, an kama wani Abdulhamid Lawan Bayero, mai shekara 48, a ranar Juma’ar da ta gabata, a Unguwar Ɗan Agundi da sunƙin tabar wiwi 114, mai nauyin kilogiram 71.7. A daidai lokacin kuma aka kama ƙwayoyin Tamol (Tramadol) guda 50,000 a Ƙofar Waika.
Darakta Femi ya sake bayyana wata babbar nasarar da NDLEA ta samu a ranar Alhamis da ta gabata, inda suka kama muggan ƙwayoyi guda 912,600, ciki har da Tramadol a wasu motocin haya biyu, ɗaya daga Lagos za ta Kano, aka kama ta a titin Abuja-Jere-Kaduna. Wanda aka kama shi ne Sahabi Lawal mai shekara 25.
A Jihar Borno kuwa, nan ma jami’an na NDLEA ba su yi ƙasa gwiwa ba, domin kuwa a cewar Femi, sun kama Umar Tijjani Mustapha, mai shekara 32 a Gangamari, ɗauke da kilogiram 55.25 na tabar wiwi, duk a ranar Alhamis da ta gabata.
Da yake jinjina wa jami’ansa, bisa namijin ƙoƙarin da suka nuna, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya-Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya yaba wa jajirtattun jami’an hukumar da ke Filin Jirgin Saman Ƙasa-da-Ƙasa na Nnamdi Azikiwe Abuja da na Tincan, Lagos, Ondo, Katsina, Yobe, Delta, Kano, Kaduna da Borno da kuma Sashin Gudanarwa da Bincike da ke Lagos da kuma dukkan jami’ai da ke sassan ƙasar nan.
“Lallai ku ƙara zage damtse ku kula,” inji Shugaba Marwa.













