Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________

A ranar Alhamis da ta gabata (30-07-2027 Miladiyya, 15-02-1448 Hijiriyya), fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya fitar da sabuwar waƙa mai taken “Malam Ya Yi Rawa Ba Wai Ba,” wacce babu raba ɗaya biyu, shaguɓe ce ga Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami, ɗan takarar Gwamna a Jihar Gombe, ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar PDP, a zaɓen 2027 mai zuwa.
Ga duk wanda ya saurari waƙar, cikin lokaci zai fahimta da cewa ba ta bambanta da salo da tsarin mawaƙin ba, yadda yake muzantawa da kushe duk wani da yake adawa da jam’iyyarsa ta APC. Waƙar cike take da zambo da ƙage da muzanta ƙima da mutuncin Sheikh Pantami, duk kuwa da cewa bai kama sunansa ba ƙarara.
Sai dai ba kamar yadda aka zata ba, a wannan lokacin, waƙar Rarara; wacce babban nufinta shi ne ta haskaka ƙimar ɗan takarar Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Jamilu Isyaku Gwamna, na Jam’iyyar APC kuma ta dakushe hasken Sheikh Pantami na PDP. Sai dai kuma reshe ya juye da mujiya. Maimakon waƙar ta dakushe hasken Pantami, sai ta ƙara haskaka shi kuma ta ƙara masa masoya.
Tun daga fitar waƙar a shafin Rarara na Facebook, sai masoyan Pantami suka fara kwarara bayanai na sukar Rarara da ɗan takararsa, a gefe guda kuma suna nuna ƙauna da soyayya ga Sheikh Pantami.
A yayin da wasu suka riƙa tausasa harshe ga Rarara, wasu ma har sai da suka riƙa antaya zagi da tsinuwa ga mawaƙin. Wasu kuma suka riƙa neman a nome shafukan mawaƙin na soshalmidiya.
Ga kaɗan daga cikin abubuwan da masoya Sheikh Pantami suka riƙa bayyanawa:
Ibrahim Namoriki da Turanci ya yi magana, inda ya ce: “If you believe say he’s @nimal in human skin like my comment!”
Shi ma Hon. Sanusi Lawal Shehu, da Turanci ya yi nasa tsokacin, ya ce: “Political differences should never be an excuse for insulting or disrespecting anyone.
“Songs and public messages should promote unity, respect and healthy debate not personal attacks.
“We can support our party and still uphold the dignity of others.
“Criticize ideas and actions but avoid attacking people’s character.
“Respect is a value that benefits everyone.”
Shi kuwa Zaid Muhammad, Ingausa ya yi, inda ya ce: “Duniya ce wallahi but in sha Allahu you will reap what you sow, waw@ kawai.”
Malam Idris Abdullahi roƙo ya yi ga masoya Pantami, yana cewa: “Don girman Allah, mu taru mu reporting account ɗin nan! Wanda yake tare dani, please like and report, please…”
Ita kuwa Malama Maijidda Muhammad Sani cewa ta yi: “Idan ganga ta cika zaƙi, lokacin fashewarta ya yi! Kana samunka, kana kira wa kanka hau, masifa da azal kuma har ƙwaryar ɗakinka za ta zo ta same ka.
“Kana cin mutunci mutane ana biye maka amma ban da na Malaman Addini. Wannan kam ka ƙetara layi da kalamanka. Cin mutuncin da ka yi a waƙar Mai Malafa ba ta kai wannan cin mutuncin da ka saki a kan Malam Pantami ba. Kuma duk mutumin kirki ba zai goyi bayanka da wannan wulaƙantacciyar waƙar ba.
“Allah wadaran naka ya lalace. Tir da fiƙira irin wannan mai haɗa Malamai da kayan maye! Allah w@daranka Dauda. Karatun allonka bai anfane ka ba.”
Shi kuwa Usman Mani Mai’aduwa Usman ST, ga abin da ya faɗa cikin fushi: “Ina da waƙoƙinka kusan ɗari biyu amma saboda wannan waƙar, wallahi na goge su kuma na ts@ne ka, ɗan w@hala.”
Shi kuwa Umar Magaji, da zafi ya ɗebo, inda ya ce: “Allah ya ts+ne maka albarka da duk zuri’arka Rarara. Duk wanda yake tare da ni, ya danna mani like.”
Abubakar Ismail kuwa da Ingilishi ya yi tsokacinsa, inda ya fara da addu’ar cewa: “May Allah keep us away from the ignorance of those who lack wisdom. Politics should never be an excuse for insults or disrespect. Everyone deserves dignity and mutual respect, regardless of political differences.”
Shi kuwa Ishaq Ɗahiru cewa ya yi: “Tun daga yau za ka fara t@ɓewa har sai ka yi bara. W@wa kawai!”
Autan Jagora kuwa, gugar zana ya yi, inda ya ce: “Duk wanda ya yarda sun rasa abin da za su kama, domin su ɓata Malam sun rasa, ya danna mani like.”
Da muka leƙa shafin Jaridar Zinariya kuwa, mun samu wani tsokaci mai tsawo daga Abban Hajiya, wanda ya bayyana cewa:
“Ba za mu lamunta ba. Gombe ba Kano ba ce. Mu al’ummar Jihar Gombe mutane ne masu daraja da mutunci kuma muna mutunta magabatanmu ko da ra’ayin siyasa ya bambanta. Mu ba za mu taɓa lamunta, Dauda Kahutu Rarara ya zo ya ci wa ɗaya daga cikin jagororinmu mutunci ba.
“Irin waƙoƙin da Rarara yake yi wajen cin carafin shugabannin siyasa a Jihar Kano, wallahi-wallahi-wallahi mu a Jihar Gombe, ba za mu taɓa lamuntar hakan ba. Domin Gombe ba Kano ba ce.
“Idan shi Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, shi ne yake saka Rarara yana irin wannan cin zarafi, to muna sanar da Sarkin Gombe; ya yi maza ya dakatar da shi. In kuma Rarara shi ne yake ta kansa, to muna sanar da Rarara cewa Gombe ba Kano ba ce.
“Ko mene ne dalilin da ya sa Rarara ba ya cin mutuncin jagororin siyasar Jihar Katsina, ko da jam’iyya ta raba su, suna APC, ‘yan adawa suna ADC ko PDP? Me ya sa Rarara ba ya zaginsu ko cin mutuncinsu amma a sauran jihohin yake haka, musamman Jihar Kano?
Shin ko me Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami zai ce game da wannan waƙa ta cin mutunci da Rarara ya yi masa? Kamar da ma ya san hakan zai faru, tuni Malam ya bayyana manufarsa ga ‘yan adawa da sauran masu cin zarafinsa, ba mawaƙi irin Rarara kaɗai ba. Ga abin da yake cewa, a wani faifan bidiyo:
“Za a zage mu, bai dame mu ba. Za ai mana habaici, bai dame mu ba. Za ai mana isgili, bai dame mu ba. Wallahi, Tallahi, Billahi, babu mutumin da a duniya zai maka wannan, ya rage darajarka a wurin Allah (swt), babu shi.”
Sheikh Pantami ya ci gaba da cewa: “Akwai wanda ya tambaye ni cewa, wai me ya sa kai ko an zage ka, bai damun ka? Bai dame ni ba, domin wa zai rage mani daraja? Allah ne kadai zai yabe ka, ka ɗaukaka. Allah ne kadai zai aibata ka, ka ƙasƙanta. Duk duniya babu mai wannan siffa sai Allah.
“Don haka, me zai dame ka da ɗan Adam? In ka ga dama, ka kafa rediyon BBC World Service, ka kafa CNN kullum, awa 24 kwana bakwai, ni kake zagi, bai dame ni ba. Babu abin da za ka rage ni da shi.
Malam Pantami ya ƙarƙare da cewa: “Duk yabon da ka yi mani a duniya, gabannin ka yi, wani ya yi wanda ya fi naka. Duk zagin da za ka yi da habaici, wani ya yi wanda ya fi naka. To mece ce baƙuwar magana? Babu wani abu sabo?”
_____
Wannan ke nan! Jama’a, yaya kuke ganin wannan al’amari? Ku bayyana ra’ayinku a Comment Section.
__________












