• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Nishadi

Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

webmaster by webmaster
May 29, 2023
in Nishadi
0
Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring
25
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Littafin hikaya na The Lord of the Ring, babu ko tantama, yana ɗaya daga cikin littattafan duniya da aka yi nasarar mayar da su fim. Duk da cewa ba shi ne kaɗai littafin da aka mayar zuwa fim ba amma daga yanayin yadda aka malkwaɗa labarin, duk da cewa yana ɗauke da abubuwan al’ajabi kuma aka fitar da shi sarai, za a iya cewa fim ɗin ya bambanta da kininsa a zamance.

Wani ƙwararren mai shirya finafinai, ɗan ƙasar New Zealand, mai suna Peter Jackson ne ya samu nasarar mayar da littafin zuwa fim. Fitaccen marubuci, J.R.R. Tolkien ne ya rubuta littafin, inda shi kuma mai shirya fim ɗin ya kasa shi zuwa gida uku, ya fara fitar da kashin farko a cikin shekarar 2001.

Related posts

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

November 5, 2025

Kamar yadda aka tsara shi littafin, fim ɗin na The Lord of the Ring yana ba da labarin wani tsaffaffen zobe ne, wanda mamallakinsa yake amfani da shi wajen juya duniya ta irin yadda yake so. Labarin yana nuna Elijah Wood (Frodo Baggins), wanda wani ɗan uwansa Ian Holm (Bilbo) ya ba shi kyautar zoben. Daga bisani ne jarumin ya gano cewa ashe zoben ba ƙaramin jidali ba ne, domin tun da ya mallake shi, bai ƙara samun sukuni ba. Ba shi kaɗai ba, duk mahalukin da ya rayu a wannan zamani, bai samu kwanciyar hankali da zaman lafiya ba, har sai lokacin da aka lalata zoben, bayan an jefa shi cikin wata gagarumar wuta.

A lokacin da Frodo ya riƙe zoben a hannunsa, wani matsafi, Ian McKellen (Gandalf) ne ya ummurce shi da cewa, lallai ya niƙi gari, ya tafi zuwa wani tsauni mai nisan gaske, kuma mai haɗarin gaske, inda a can ne aka ƙera zoben shekaru dubbai da suka gabata. Ya ce a wannan tsauni ne kaɗai za a iya lalata ƙarfi da tasirin zoben, wanda haka ne kaɗai zai kawo wa duniya kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Shi kuwa Frodo bai ɓata lokaci ba, sai ya ƙuduri aniyar tafiya wannan tsauni, domin ya ceto duniya daga bala’in da ke tattare da wannan zobe da ke wurinsa. Ba shi kaɗai ya tafi wannan tafiya mai haɗari ba, domin kuwa wasu aminansa, mutum takwas sun kasance tare da shi. Waɗannan kuwa sun haɗa da Hobbit Sam (Sean Astin) da Merry (Dominic Monaghan) da Pippin (Billy Boyd). Sauran sun haɗa da Gandalf da Aragorn (Viggo Mortensen) da Boromir (Sean Bean) da Elf Archer Legolas (Orlando Bloom) da Dwarf Soldier Gimli (John Rhys-Davies).

’Ya’yan wannan ayari, sun niƙi gari suka tunkari ƙasar Mordo, inda a cikinta ne wannan hatsabibin tsauni yake. Sun yi ta tafiya cikin haɗari kala-kala, suka ratsa ta masarautar Elfish na Rivendell, sannan suka shiga surƙuƙin dajin Lothlorien. A nan ne suka samu tallafi daga Gimbiya Elf Arwen (Liv Tyler) da babanta Elrond (Hugo Weaving) da Sarauniya Galadriel (Cate Blanchett).

Tawagar Frodo ta yi ta gamuwa da ƙalubale da barazana iri-iri, inda akwai wani matsafi, wanda ke adawa da mayar da zoben, wanda kuma yake ƙoƙarin ganin ya mallake shi domin buƙatar kansa. Wannan matsafi mai suna Saruman (Christopher Lee), wanda kuma ɗan uwa ne ga Gandalf amma ya fitsare ƙafarsa yana adawa da shi. Haka kuma akwai wasu mahara, masu mugun ƙuduri, bisa jagorancin Sauron (Sala Baker), wanda su ma sun yi ta kawo wa tawagar cikas.

Baya ga waɗannan hatsabibai, tawagar Frodo ta yi ta fafata yaƙi da faɗa da wasu halittu masu tashi sama da dabbobi masu ɗauke da iskokai kala-kala. Haka suka yi ta ƙoƙari har suka isa ƙasar Mordor kuma suka samu nasarar jefa zoben cikin wannan gagarumar wuta. Daga nan kuwa suka koma gida, suka ci gaba da rayuwarsu cikin farin ciki.

Fim din The Lord of the Rings dai kamar yadda aka faɗa a baya, an kasa shi ne zuwa gida uku, The Fellowship of the Ring (2001) da The Two Towers (2002) da kuma The Return of the King (2003). Mafi yawa daga sassan fim ɗin, an ɗauke su ne a dazuzzukan ƙasar New Zealand.

Previous Post

Ashe Shaikh Jafar Mahmud Adam Bai Mutu Ba?

Next Post

GIZAGAWAN NAJERIYA Sun Yi Wa ‘Dan Uwansu Alkotonawi Gangamin Addu’a

Related Posts

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?
Nishadi

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci
Nishadi

Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

November 5, 2025
Tsakanin A’isha Humaira da Umar Baana: Sulhu Alheri Ne
Nishadi

Tsakanin A’isha Humaira da Umar Baana: Sulhu Alheri Ne

October 31, 2025
Next Post
GIZAGAWAN NAJERIYA Sun Yi Wa ‘Dan Uwansu Alkotonawi Gangamin Addu’a

GIZAGAWAN NAJERIYA Sun Yi Wa 'Dan Uwansu Alkotonawi Gangamin Addu'a

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama’a, kuma ya na yin illa ga tattalin arzikin ƙasa – Minista

Minista Ya Buƙaci Masu Sana’ar Talla A Kafafen Yaɗa Labarai Su Faɗakar Da Jama’a Game Da Shirye-Shiryen Tattalin Arziki Na Gwamnatin Tinubu

December 9, 2023
SASSANYAN AMINCI (4)

SASSANYAN AMINCI (4)

September 11, 2025
Lallai Hukuma Ta Tallafa Wa Marubuta Domin Yaƙar Jahilci – Sheikh Gamawa

NASIHAR JUMU’A: Daga Sheikh Aliyu Said Gamawa

September 1, 2023
Sasanci Da ‘Yan Bindiga: A Sake Duba Lamarin Nan A Tsanaki

Sasanci Da ‘Yan Bindiga: A Sake Duba Lamarin Nan A Tsanaki

October 13, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.