• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gumbar Dutse

Ashe Shaikh Jafar Mahmud Adam Bai Mutu Ba?

webmaster by webmaster
May 29, 2023
in Gumbar Dutse
0
Ashe Shaikh Jafar Mahmud Adam Bai Mutu Ba?
77
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Wanda ya mutu bai sauri ba, wanda kuma ke raye bai yi jinkiri ba. Yau shekara 16 ke nan cur da wasu ballagazai, shashashai, waɗanda suka kwashe shimfiɗarsu daga gaban Allah, suka zaɓi ƙasƙanci, suka yi wa fitaccen malamin Musulunci, Shaikh Jafar Mahmud Adam kisan gilla. Sai dai kuma an samu tabbataccen bayanin cewa ashe bai mutu ba. To yaya abin yake? 

A ranar Juma’a, 13 ga watan Afirilun 2007, wasu ’yan bindiga da sanyin asuba, suka halarci masallacin da Sheikh Jafar yake limanci a Unguwar Ɗorayi, Kano, suka iske shi kuwa yana jagorancin mafificiyar Sallah mai daraja, Sallar Asuba, suka ɗirka masa dalmomi a jiki. Malamin yana cikin sujada ga Allah (SWA) ya yi shahada.

Related posts

Jinjina Da Yabo Ga Nagartaccen Shugaba: Malam Labiru Musa Ƙafur, mni

Jinjina Da Yabo Ga Nagartaccen Shugaba: Malam Labiru Musa Ƙafur, mni

October 29, 2025
MAGAJI GALADIMA: Yau Ne Maulidin Magayaƙin Kano

MAGAJI GALADIMA: Yau Ne Maulidin Magayaƙin Kano

September 29, 2023

Babban abin takaici game da marigayin, ba wai yanayin mutuwarsa ba ne, a’a, asarar da aka ɗibga wa al’umma. A lokacin da Malam ya rasu, lokaci ne da al’ummarmu take matukar buƙatar muhimman malamai irinsa. Mutum ne shi da ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen karatu da karantarwa, faɗaka da faɗakarwa, ankara da ankararwa.

A lokacin da mafi yawan malaman addini suka zama makwaɗaita, shi Malam Jafar sai ya zama daban, ya kasance wanda ya san kansa kuma ya riƙe mutuncin kansa. A lokacin da wasu malaman suka siffatu da karkatar da mabiyansu saboda neman girma da kuma neman abin duniya, Malam Jafar sai ya kasance kaifi ɗaya. Ya ɗora koyarwarsa bisa turba ɗaya bisa hujja mai inganci ta Alƙur’ani da Hadisi da Ijma’in Malaman Sunna.

Wannan halayya ce ta ba shi damar kasancewa mutum jajirtacce, wanda ba ya ƙyuya ko kasala. A kullum yana cikin nazari da bincike kuma ba ya furta duk wata fatawa, ba ya ambata kowane karatu, face yana da hujja da ƙwaƙƙwarar madogara. Malami ne shi da ya kauce wa al’amuran ƙungiyanci. Idan gaskiya ta zo, ba ya shayin faɗin ta, ya Allah ga ’yan Izala ko ga ’yan Shi’a ko ga ’yan Ɗarika ko kuma ga Kirista da ma waɗanda ba su da addini. Kuma ya kasance mai amsar gyara idan ya yi kuskure. Shi ne ba ya ƙyashin dawowa baya ya bayyana kuskuren wata fatawa da ya bayar ba daidai ba a karatunsa.

Allah Ya ji ƙan sa da gafara. A lokacin da ya fara ganin take-taken marigayi malamin ’yan Boko Haram, Malam Muhammad Yusuf, Shaikh Jafar ya yi iyaka ƙoƙarinsa wajen faɗakar da shi, game da fitinar da yake neman kunnowa ga al’umma. Malamin ya yi kunnen uwar shegu da huɗubar Jafar, sai ga shi kuwa abin da ya hango ya tabbata. A yau Boko Haram ta zama annoba ga al’umma.

Managarcin malami, Sheikh Jafar ya haifar da sauyi mai girma ga al’umma, musamman ma matasa maza da mata, inda suka fahimci tsantsar abin da Musulunci ke koyarwa. Ta hanyar wa’azojinsa, al’umma sun ƙaru sosai da nagartaccen ilimi. Matasa sun fahimta da tsantsar abin da ake nufi da rayuwa, sun gane tasirin neman ilimi, sun gane tasirin neman aiki ko sana’a, kamar yadda suka gane illar zaman kashe wando.

A karantarwarsa, Malam bai bar shugabanni da ’yan siyasa ba, bai bar masu sarautar gargajiya ba, haka kuma bai bar ma’aikatan gwamnati ba, bai bar ’yan kasuwa ba, kamar kuma yadda bai bar talaka ba. Idan mai mulki ya kauce wa gaskiya, ɓalo-ɓalo zai fito ya fayyace masa illar haka. Ya yi yaƙi da azzaluman duniya, ya fayyace fari daga baƙi. Ya sassaita tunanin al’umma da hasken iliminsa.

Wani abin takaici shi ne, har zuwa yau ɗin nan da aka cika shekara 16 cur da kisan gillar da aka yi wa Malam, babu wani da aka kama daga cikin wadanda suka gudanar da aika-aikar. Kuma muna gadarar wai muna da jami’an tsaro, muna da shugabanni!

Sai dai kuma babban saƙon da a yau ake aikawa ga gafalallun da suka yi wannan aika-aika da duk waɗanda suka ɗaure musu gindi shi ne, jinin Malam Jafar bai zuba a banza ba. Haka kuma su sani, su ji da babbar murya, lallai Shaikh Jafar bai mutu ba, yana nan a raye, domin kuwa ɗimbin almajiransa da ɗimbin ilimin da ya bari a doron ƙasa suna nan a raye kuma suna ci gaba da yaɗuwa a duk faɗin duniya.

Malam Jafar bai mutu ba. A yanzu haka muna kyautata ingantaccen zaton yana can a makwancinsa na ni’ima.
Su kuwa makasa, mashaya jinin al’umma, ina makomarsu take? Tabbas haƙiƙa suna cikin baƙin ciki da ƙasƙanci da wulaƙanci. A kullum addu’armu gare su ita ce, Allah Ya dawwamar da su cikin baƙin ciki, a nan duniya da kuma gobe ƙiyama.

Malam Jafar Mahmud Adam dai an haife shi ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, 1960, a garin Daura na Jihar Katsina. Ya samu gurbin karatun gaba da firamare a 1984, inda ya shiga Government Teachers’ College Gwale, wacce a yanzu ake kiran ta da sunan Government Arabic College Gwale. Ya kammala a 1988, daga nan ya samu gurbin ci gaba da karatu a Jami’ar Musulunci ta Madina a Saudiyya. Ya yi karatunsa a can na tsawon shekaru huɗu, inda ya kammala a 1993.

Marigayi Malam Jafar ya kasance ina-ka-fito-nazari-ina-za-ka-da’awa. Gaba ɗayan rayuwarsa ta kasance a hidimar Musulunci.

Muna roƙon Allah Ya ji ƙan sa da gafara, Ya amshi shahadarsa, Ya ci gaba da raya ayyukansa a faɗin duniya. Allah Ya yi masa sakayyar zaluncin da aka shuka masa, Ya tona asirin makasansa da duk waɗanda suka ba da goyon bayan haka ta tabbata. Allah Ka tada mana da magajinsa, wanda zai ci gaba da haskaka addininKa ga al’umma.

Malam Jafar Adam, muna tuna ka, muna yi maka addu’a a kullum. Allah Ya ji ƙan ka!

Previous Post

Kana Son Zaman Lafiya? Ka Bi Shawarar Sani Rogo

Next Post

Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

Related Posts

Jinjina Da Yabo Ga Nagartaccen Shugaba: Malam Labiru Musa Ƙafur, mni
Gumbar Dutse

Jinjina Da Yabo Ga Nagartaccen Shugaba: Malam Labiru Musa Ƙafur, mni

October 29, 2025
MAGAJI GALADIMA: Yau Ne Maulidin Magayaƙin Kano
Gumbar Dutse

MAGAJI GALADIMA: Yau Ne Maulidin Magayaƙin Kano

September 29, 2023
Next Post
Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Katsina At 36: Gov Radda Felicitates with Founding Fathers, Citizens

Katsina At 36: Gov Radda Felicitates with Founding Fathers, Citizens

September 24, 2023
Gwamnati Ta Nemi Google Ya Daƙile Bazuwar Bayanan Da Ka Iya Wargaza Najeriya

Gwamnati Ta Nemi Google Ya Daƙile Bazuwar Bayanan Da Ka Iya Wargaza Najeriya

October 14, 2023
TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

April 22, 2025
TAKAICI: Waɗannan… Duk A Cikin Mako Ɗaya?

TAKAICI: Waɗannan… Duk A Cikin Mako Ɗaya?

November 20, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.