• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Nishadi

Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

NISHAƊI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 5, 2025
in Nishadi
0
Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

Mawaƙi Abdulkarim: Burna Boy

32
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
Mawaƙi Abdulkarim: Burna Boy


                            •••••••
Fitaccen mawaƙin Afrobeats ɗan Najeriya, Damini Ogulu wanda aka fi sani da Burna Boy, ya samu arzikin shiga inuwar Musulunci, inda a farkon makon nan ya bayyana cewa ya bar Kiristanci ya rungumi addinin Musulunci.

A cikin wata hira da aka yi da shi a kafar watsa labaran nishaɗi ta Plaqueboymax, mawaƙin wanda ya taɓa lashe kyautar Grammy ya ce ya taso a matsayin Kirista ne daga gidansu. Ya ce hakan ya faru ne saboda iyayensa Kirista ne, kamar yadda yankinsu ma ya kasance na mabiya addinin Kirista

Ko mene ne ya ja hankalinsa zuwa shiga Musulunci? Shahararren mawaƙi Burna Boy ya ce daga baya ne ya yanke shawarar rungumar Musulunci, bayan ya daɗe yana nazarin wasu addinai daban-daban domin neman cikakkiyar fahimta. Sai dai ya ce wannan bincike da nazari nasa sun haifar masa da ƙarin tambayoyi fiye da amsoshi, inda daga ƙarshe ya aminta da shiga Musulunci.

Ya ce: “Addini wani tsari ne na sarrafa rayuwa. A duk bincikena, kullum nakan gano cewa akwai wata hujjar kimiyya guda ɗaya, wacce ke saɓa wa kowane littafi. Komai yana fitowa ne daga wayewar rana.”

Ya ci gaba da cewa: “Ni mutum ne mai ruhi sosai. Na yi amanna da cewa mu halittu ne. Idan mu halittu ne, dole akwai mahaliccinmu. Na lura kowa da irin fassara da hangen da yake yi wa addini.

“Wannan shi ne abin da iyayenka suka yi imani da shi. Wannan shi ne abin da aka haife ka a ciki. Na tashi a matsayin Kirista amma daga baya na musulunta. Na barranta da duk sauran addinai, domin na yi nazari a kansu duka. Har yanzu ina ƙoƙarin gano wane addini ne na gaskiya kuma na ainihi?”

Mawaƙi Burna Boy, wanda ya canja suna zuwa Abdulkarim ya ci gaba da bayanin cewa: “Mafi yawan lokacin da nake binciken gaskiya, nakan fuskanci yawan ruɗani. Wannan ita ce matsalar. Abin da kawai na sani shi ne, gaskiya akwai wani abu a sama da ke kiyaye ni. Ina da alaƙa da wannan. Shi ya sa idan na yi addu’a, ina jin kamar ana sauraro na kuma ana amsa mani.”

√ Wane Ne Burna Boy?
An haifi Damini Ebunoluwa Ogulu, Burna Boy a ranar 2 ga Yuli 1991 a garin Fatakwal na Jihar Rivers, Najeriya. Ana yi masa laƙabi da African Giant, ODG da Big. Baya ga kasancewarsa mawaƙi, yana kuma sana’ar rubutawa da shirya waƙoƙi. Ya fara waɗannan sana’o’i tun daga shekarar 2010. Yana da kamfanin shirya waƙoƙi na Spaceship Records. Sunan mahaifinsa Samuel Ogulu, wanda yake da kamfanin yin walda. Mahaifiyarsa kuwa sunanta Bose Ogulu, wacce take aiki a matsayin tafinta. Yana da ‘yar uwa ɗaya, mai suna Nissi Ogulu.

Abdulkarim Burna Boy yana zaune ne a katafaren gidansa na alfarma da ke Unguwar Lekki, Legas, kodayake yana yawan zuwa Amurka domin sana’arsa ta waƙa, inda kuma yake da gida a birnin Los Angeles. Ya ƙware a salon waƙa iri huɗu, Afrobeats, Reggae, Dancehall da Pop.

Muna roƙon Allah ya dawwamar da shi cikin wannan addini na Musulunci kuma ya kasance mai ingantaccen imani har ƙarshen rayuwars. Amin-Summa-Amin.

‘Yan uwa, wane fatan alheri za ki yi wa ɗan uwa Abdulkarim Burna Boy? Ku bayyana a Comment Section.
_______________

Previous Post

Ba Mu Da Wata Ƙasa Kamar Najeriya

Next Post

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

Related Posts

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?
Nishadi

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?
Nishadi

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
Tsakanin A’isha Humaira da Umar Baana: Sulhu Alheri Ne
Nishadi

Tsakanin A’isha Humaira da Umar Baana: Sulhu Alheri Ne

October 31, 2025
Next Post
Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

2027 and the Rise of a Third Force: Can ADC’s Political Heavyweights Unseat Tinubu?

SHIN KO GAMAYYAR ‘YAN ADAWA NA JAM’IYYAR ADC ZA SU IYA KADA TINUBU A 2027?

July 3, 2025
Kwankwaso’s Return to APC: Between the Devil and the Deep Blue Sea

Kwankwaso’s Return to APC: Between the Devil and the Deep Blue Sea

July 11, 2025
An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

July 29, 2023
WHEN THE SPIRIT WHISPERS: Littafin Tsarkake Tunani Da Samar Da Saita Rayuwa

WHEN THE SPIRIT WHISPERS: Littafin Tsarkake Tunani Da Samar Da Saita Rayuwa

October 11, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.