Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Fitaccen ɗan fim kuma Furodusa, Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-tama ya koka da halayyar ‘yan kasuwa a Najeriya, inda ya ce ba su da tausayi wajen tsauwala farashi da nufin ƙara ƙuntata wa al’umma.
Da yake kokawa a shafinsa na Facebook, ɗan fim ɗin ya ce: “Haka kawai ‘yan kasuwa ku dinga ƙara farashin kayan masarufi ba gaira ba dalili, an rasa mai tsawatar muku?”
Ya ce “yanzu kwandon tumatiri babba ₦50,000 da kuma na ₦40,000; ƙaramin kwandon shi ne ₦10,000, kwano kuwa ₦2,500.”
Cikin alhini da takaici Iyan-tama ya koka da cewa: “Kowanne ɗan kasuwa da an wayi sai ya fake da tashin Dala ko Fetur, ya ƙara farashi, ƙarin rashin hankali kuma jama’a sai mu biye musu mu saya.”
Da yake Allah wadai da lamarin, sai ya bayyana ƙaurace wa tumatiri. “Na haƙura da kai tumatiri. Attarugu, ka ci gidanku, tattasai a je a ruɓe, ba na so, na haƙura.”
Da ya juya kan masu mulki kuwa, Hamisu cewa ya yi: “Anya, anya ana son a rage wa jama,a raɗaɗin wahalhalu kuwa? Shi kansa talakan ba ya tausa wa ɗan uwansa talaka; ta kowace hanya. Kowa kawai dama yake jira ta zo masa ya yi yadda ya ga dama – babu tausayi. Allah Ya kyauta.”














Masha Allah da wannan shafi.Allah yayi Jagora Amin.
Madalla da ayyukanka na faɗakar da al’umma. Mun gode sosai mu ma