Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
__________
Kamar yadda Shafin Northern Nigeria Hub a intanet ya ruwaito, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, kuma ɗan takarar Gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami, ya mayar da martani mai zafi kan suka da ake yi dangane da fara yaƙin neman zaɓe da wuri, inda ya bayyana cewa tsoratarwa da barazanar da hukumomin gwamnati ke yi, alama ce ta cewa tafiyarsu na dab da samun nasara.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana a baya-bayan nan, Sheikh Pantami ya yi watsi da yunƙurin da abokan hamayyarsa ke yi na tsoratar da magoya bayansa, ta hanyar amfani da hukumomin tsaro. Ya jaddada cewa tsangwamar siyasa ko barazanar ɗauri ba za su hana su ci gaba da tafiyarsu ba.
“Da zarar ka kalli waɗannan idanuwan, za ka san ba za a iya razana mu da barazana ba,” in ji Pantami. “Idan ka fara wata tafiya kuma aka fara yi maka tsoratarwa, wannan alama ce ta cewa nasara na gabatowa. Bayan na yi rashin mahaifina, mahaifiyata, ɗana da sauran makusantana, babu abin da ya rage a duniya da zan ji tsoro a kansa.”
Pantami ya kuma ƙalubalanci abokan hamayyarsa, musamman shugabanninsu, da su daina yin maganganu a fakaice, su fito fili domin gudanar da muhawara ido-da-ido, tare da gabatar da hujjoji ga al’ummar Jihar Gombe.
“Idan ba ku yarda da abin da muke faɗa ba, kada ku tsaya gefe kuna magana. Ku aiko da gayyata a hukumance, mu haɗu ido-da-ido, jama’a su gani waye ke da hujjoji na gaskiya,” in ji shi.
Kalaman Pantami sun zo ne a matsayin martani a fakaice ga wani jawabi da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi a baya. A lokacin da yake magana kan dokokin yaƙin neman zaɓe. Gwamna Inuwa Yahaya ya soki wasu ‘yan siyasa da ya zarga da karya ƙa’idojin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta hanyar fara yaƙin neman zaɓe kafin lokacin da doka ta tanada, tare da yaudarar jama’a.
A cikin jawabinsa, Gwamna Yahaya ya kuma yi tsokaci kan dogon tarihinsa na ilimi da tarbiyya a Jihar Gombe, musamman a fannin ilimin addinin Musulunci. Ya bayyana cewa tun kafin siyasar zamani ta samu karɓuwa, shi Alaramma ne, yana mai nuna cancantarsa da matsayinsa a tsakanin al’umma.
Kodayake Gwamna Yahaya bai ambaci sunan Sheikh Pantami kai tsaye ba, masu sa ido kan harkokin siyasa sun ɗauki kalamansa kan fara yaƙin neman zaɓe da kuma cancantar ilimin addini a matsayin martani kai tsaye ga tarurruka da jawaban da Pantami ke yi a sassa daban-daban na jihar.
Sabbin kalaman Pantami sun nuna cewa takun-saƙar siyasa a Jihar Gombe tana ƙara ɗaukar zafi, yayin da ɓangarorin biyu ke ci gaba da amfani da kalamai masu ƙarfi a daidai lokacin da ake tunkarar fafatawar siyasa mai zuwa.
__________












