• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, July 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Jan Hankali Ga Shugabanni

TSOKACINMU NA MAKO

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 9, 2025
in Gizago
0
Jan Hankali Ga Shugabanni

Shugabanni ku ji tsoron Allah

23
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Jan Hankali Ga Shugabanni

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Saƙon Godiya Da Bangajiya

Saƙon Godiya Da Bangajiya

July 22, 2026
MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana

MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana

July 21, 2026
Shugabanni ku ji tsoron Allah


                           •••••••
Ya kai MUTUM, ka zama mai taka-tsan-tsan da rayuwa, domin kuwa babu abin da ke tabbata. Komai daɗewar halitta, wata rana za ta gushe. Idan kana son babban misali, ka kalli JARIRI kuma ka kalli GAWA. Ɗaya zuwa ya yi yanzu, ɗaya kuma tafiya ya yi. Ko ka gane darasin haka?

Tafiya sannu-sannu kwana nesa. A duk lokacin da ka fara wani abu, sannu za ga ka kammala shi. Misali kana ɗan siyasa, a ce an zaɓe ka kan wani muƙami, Shugaban Ƙasa, Gwamna, Ɗan Majalisa ko Shugaban Ƙaramar Hukuma, bayan wani lokaci, sai ka ji ana cewa saura kwanaki kaza ka sauka; ko dai a sake zaɓenka ko kuma shi ke nan har abada.

Ya kai ɗan siyasa, ka sani cewa Hausawa suna cewa, gani ga wane ya isa wane tsoron Allah, kamar kuma yadda suka ce, abokin damo kuza. Me nake nufi da waɗannan batutuwa? Ina nufin ya kamata ka ɗauki izna kuma ka ɗauki misali da wasu ƙasashe da wasu ‘yan siyasa na wasu ƙasashe.

A lokacin da ka samu kanka bisa kujerar mulki, ka yi abota da ƙasar da za ta ƙarfafi ƙasarka ta fannonin kirki. Kada ka yi ƙawance da ƙasa ko Shugaban Ƙasar da zai cuci al’ummarka. Kuma ka aikata abin da ya dace, tun kafin wa’adin mulkinka ya ƙare.

Ka sani cewa Shugaban da ke kishin al’ummarsa shi ne ke fita waje ya jawo wa ƙasarsa arziki, ba wai ya gayyato mata tawagar ‘yan ta’adda ba. Ka zama mai ƙudurin alheri ga al’umma.

Ya kai ɗan siyasa, ya kamata ka bambanta da wasu kurayen shugabanni da ke kwashe dukiyar talakawa su kai ƙasashen waje su kimshe. Wannan kashe ƙasa ne, kashe al’umma ne. Ka sani, dabba ma fita take daga gidanta, ta samo albarka ta kawo gida, ba wai ta ɗauki na gidanta ta kai waje ba.

Ya kai mai son mutane su zaɓe ka a matsayin SHUGABA, ka zama mai kishin ƙasa kuma mai kishin al’ummarka. Ka sani, komai daɗewa, akwai ƙarshe.
_______________

Previous Post

Zargin Tallafa Wa Ta’addanci: Hafsoshin Soja Sun Aika Kakkausan Gargaɗi Ga Sahara Reporters

Next Post

A CELEBRATION OF WISDOM

Related Posts

Saƙon Godiya Da Bangajiya
Gizago

Saƙon Godiya Da Bangajiya

July 22, 2026
MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana
Gizago

MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana

July 21, 2026
Tsakanin Gwamna Bago Da Wasu Malamai…
Gizago

Tsakanin Gwamna Bago Da Wasu Malamai…

July 21, 2026
Next Post
A CELEBRATION OF WISDOM

A CELEBRATION OF WISDOM

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RAMADAN KARIM: 21-1447

RAMADAN KARIM: 21-1447

March 10, 2026
Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

INEC Ta Yi Wa Daraktocin Hukumar Huɗu Ritayar Dole

December 28, 2023
TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

June 20, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.