• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, May 2, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

HAMISU GUMEL: Dacewarsa A Muƙamin Sakataren Watsa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 9, 2023
in Adabi
0
HAMISU GUMEL: Dacewarsa A Muƙamin Sakataren Watsa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa
52
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Ibrahim Namadi, ya naɗa ƙwararren ɗan jarida, marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Muhammed Hamisu Gumel, a muƙamin Sakataren Watsa Labarai, jim kaɗan da rantsar da shi a kujerar mulki.

Related posts

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026

Ko wane ne Hamisu Gumel? An haifi ƙwararren ɗan jaridar ne a ranar 15 ga watan Agusta, 1976, a Ƙaramar Hukumar Gumel, Jihar Jigawa. Ya yi karatu har zuwa matakin Jami’a, inda ya samu shaidar digiri a fannin aikin jarida a Jami’ar Bayero Kano.
A rayuwarsa ta neman ilimi, ya halarci kwasakwasai a fannonin aikin jarida, harkar hulɗa da jama’a da kuma ƙwarewa a harkar jin ƙai da kare haƙƙin ɗan Adam a Najeriya da ƙasashen waje daban-daban. Kan haka ne ya samu cancantar zama mamba a ƙungiyoyin ƙwararrun ma’aikata da suka haɗa da Ƙungiyar Ƙwararrun Jami’an Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) da Ƙungiyar Ƙwararrun Masu Ba Da Agajin Jin Ƙai (PHAP), Ƙungiyar Masu Ba Da Hidima A Fannin Harsuna ta Najeriya (LASPAN) da kuma Ƙungiyar Masu Fassara Yaruka ta Duniya.
A fannin aiki kuwa, Malam Hamisu ya yi aiki a wurare daban-daban, waɗanda suka haɗa da, Hukumar Fiscal Responsibility Commission, Abuja daga 2011 zuwa bana, inda ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban Jami’in Watsa Labarai. Ya yi aiki a Majalisar Tarayya Abuja, a matsayin Jami’i mai taimaka wa Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, kan abin da ya shafi Kwamitin Kula da ‘Yan Gudun Hijira. Ya taɓa aiki a Hukumar Watsa Labarai ta Ƙasa daga 2002 zuwa 2011 a matsayin Babban Jami’in Kula da Tantancewa a Shiyyar Kaduna, sannan aka matsa da shi zuwa Jihar Katsina a matsayin mai kula da jihar baki ɗaya.
Gumel ya taɓa yin aiki da gidan jaridar Crystal International Newsmagazine, a shekarar 2001 zuwa 2002, a matsayin ɗan rahoto da kuma jami’in bin ƙwaƙƙwafi. Ya taɓa zama Editan Mujallar Fim a Kaduna, a shekarar 2001. Ya taɓa yin aiki a bankin Tropical Commercial Bank, a shekarar 2000 zuwa 2001, inda ya yi hidimar ƙasa (NYSC). Haka kuma ya taɓa yin aiki a kamfanin jaridar The Shield Weekly/Garkuwa Newspapers, Kano a shekarar 2000, a matsayin ɗan rahoto.
A matsayinsa na ƙwararren marubuci kuwa, Malam Hamisu ya rubuta littattafai da dama cikin harsunan Ingilishi da Hausa, cikinsu har da littafi Mai taken Sadauki Umar, wanda ya zayyano hikiyar Sahabin Annabi Muhammadu (saw), Umar bin Kaɗɗab (ra).
Kasancewar shi mutum mai haƙuri da juriya, gami kuma da iya mu’amala da jama’a, wannan muƙami da Gwamnan Jihar Jigawa ya ba shi, babu shakka ya dace. Hasali ma za a iya cewa a sargaye ƙwarya a daidai ragayarta.
Muna yi masa fatan alheri da addu’ar Allah Ya taya riƙo, amin.

 

Previous Post

An Ƙarfafa Ƙawance Tsakanin Jigawa Da Zinder

Next Post

EFCC Ta Kai Farmaki Jihar Katsina

Related Posts

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Next Post
EFCC Ta Kai Farmaki Jihar Katsina

EFCC Ta Kai Farmaki Jihar Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Burina Rubutuna Ya Zama Silar Shiriyar Al’umma – Antin Kaduna

Burina Rubutuna Ya Zama Silar Shiriyar Al’umma – Antin Kaduna

September 10, 2023
Ɓarayin Fetur Sun Kwashi Kashinsu A Hannun Sojojin Najeriya

Ɓarayin Fetur Sun Kwashi Kashinsu A Hannun Sojojin Najeriya

June 27, 2023
Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (2)

Barkwancin Ƙarshen Mako

July 22, 2023
Gwamnatina Za Ta Mutunta ‘Yancin Kafafen Yaɗa Labarai

Gwamnatina Za Ta Mutunta ‘Yancin Kafafen Yaɗa Labarai

December 19, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.