Burina Rubutuna Ya Zama Silar Shiriyar Al’umma – Antin Kaduna
Daga Binta Tukur
~~~~~~~
Malama Sadiya Muhammad, wacce aka fi sani da laƙanin ‘Antin Kaduna’ marubuciya ce ta kwatance. Haka kuma jakadiyar marasa galihu ce, domin kuwa tana da gidauniya da take gudanarwa, inda take nema wa naƙasassu da marasa galihu tallafi. Wakiliyar Taskar Gizago ta musamman, BINTA TUKUR, ta tattauna da ita, inda ta baje kolin bayanai dangane da rayuwarta ta rubutu da kuma haƙilon ta na taimakon raunana daga cikin al’umma.
~~~~~~~

TG: Kina ɗaya daga cikin manyan marubutan Hausa, ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice?
ANTIN KADUNA: Assalamu alaikum warahamatullah. Farko dai sunana Sadiya Muhammad Abdulllahi, wacce aka fi sani da Antin Kaduna. An haife ni a garin Kaduna, a cikin ƙwaryar Tudun Wada. Na yi karatun firamare da sakandare duka a nan cikin Kaduna. A yanzu haka ina da shaidar karatu a mataki na difiloma a fannin harshen Larabci.
TG: Tun yaushe kika fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinki ga harkar rubuce-rubuce?
ANTIN KADUNA: Na fara rubutu a shekarar 2007. Farko abin da ya jawo ra’ayina na fara rubutu shi ne sha’awar rubutun, inda daga baya ya rikiɗe ya dawo kishin adabi.
TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa kika buga a intanet?
ANTIN KADUNA: Na rubuta littattafai guda goma sha ɗaya, inda yanzu kuma ina rubuta waɗansu guda biyu a intanet, ‘Badaƙalar Rayuwa’ da ‘Azal.’
TG: Waɗanne irin matsaloli kike fuskanta a matsayinki na marubuciya, musamman ma a soshalmidiya?
ANTIN KADUNA: Matsaloli akwai su bila adadin. Gaskiya kasancewar yanzu rubutun shi kansa da fitar da shi ya zama abin da ya zama sai dai mu ce Allah Ya shiga cikin lamarin; domin ba a cewa komai.
TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori kika samu ko kuma akasin su?
ANTIN KADUNA: Alhamdu lillahi, na samu nasarori da dama. Sai dai in ce na gode wa Allah da masoyana, sannan kuma ina alfahari da harshena na Hausa.
TG: Baya ga harkar rubutu, kin tsunduma cikin harkokin tallafa wa al’umma don inganta zamantakewar aurensu. Ta yaya kika faro wannan kuma ko za ki yi mana cikakken bayani game da ƙalubalen wannan aiki?
ANTIN KADUNA: To ala kulli halin, duk inda bawa ya tsinci kansa ya gode wa Allah, domin ba yin kansa ba ne, yin Allah ne. Wannan gidauniya tawa na jima da tunanin kafa ta saboda marasa ƙarfi da gajiyayyu da masu buƙata ta musamman, tun kafin in fara rubutu nake faɗ tashi a kanta. Ina ɗan kai kawona da ɗan abin da ke hannuna, daga baya da abin ya fara fin ƙarfin arziƙina, na fara miƙa ƙoƙon barana ga wanda nake tunanin zai iya tallafawa daidai gwar gwado.
Wani zubin a samu wani zubin ba a samu, kasancewar In dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Kuma nakan nemi taimako ne a zagayen inda nake, daga baya ne na faɗaɗa. Daga nan garin da nake sai ahankali gaskiya. To sai ma na fi samun tallafi a wajen Kaduna kuma muna samun ƙalubale sosai inda za ku ga mun zama kamar tsani wajen miƙa saƙon mabuƙata. To mu kuma sai a dinga mana kallo kamar mabarata saboda wasu in kana masu kallon za su iya taimakawa kai masu magana sai su share ka, ko kula ka ba za su yi ba.
To wannan abin yana karya mani gwiwa, sai in ga kamar suna kallon ki a ƙasƙantacciya. Shi ya sa wani lokacin in mara ƙarfi ko mara lafiya ko dai wani mabaraci ya taho gare mu, ba na iya ce masa babu, sai dai in ce in ya yarda a ɗauke shi a miƙa ƙoƙon bararsa, in wani ya ga Allah ya ga Annabi sai ya taimaka masa.
Wani lokacin ma a yi ta watsawa amma ko ƙwandala ba za a samar masa ba… Kai abin akwai wahala gaskiya. Shi kuma sai ya ga ka ƙi ka taimaka masa ne. Muna yi ne dai saboda Allah, duk wanda ka taimaka ma wa da sulenka, ladarka na nan tana ta gudana har ranar da Allah zai tashe mu a gabansya dawo maka da abarka. Allah ya sa mu dace.
TG: A matsayinki na marubuciya, mene ne babban burinki game da rubutu?
ANTIN KADUNA: Babban burina game da rubutu, shi ne rubutuna ya zama silar shiriyar wasu, sannan kuma in ji shi ko in ji labarin ya kai ƙasashe, inda ƙafata ba za ta iya kaiwa ba, inda tunanina bai taɓa tsammanin rubutun zai kai ba; sai in ji rubutuna ya kai. Wannan ya ishe ni godiyar Allah.
TG: Ko kina da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanki da kuma al’umma masu karanta littattafanki da sauran al’ummar da kike ba Shawarwari?
ANTIN KADUNA: Kiran da zan yi ga gwamnati shi ne, ta jawo mu mu marubuta a jiki domin akwai gudunmowar da mu ma za mu iya takawa a cikin gwamnati, wanda da rubutunmu da basirar da Allah ya ba mu, za mu iya taimakawa sosai fiye da yadda da ba a zata ba, in sha Allahu.
Kran da zan yi ga y’an uwana marubuta shi ne, a kodayaushe in za mu yi rubutu, mu dinga tsaftace kalamanmu, mu daina rubutu kara zube saboda tarbiyyar yaranmu manyan gobe. Sannan kuma mu zamo tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Idan za mu yi magana, mu yi ta da murya ɗaya.
Daga ƙarshe ina mana ta’aziyyar rasuwar ɗan uwanmu, masoyinmu, bawan Allah, Auwal Garba Ɗanbarno. Allah Ya kai haske ƙabarinsa, Ubangiji Ya kula da bayansa , Amin.
Haka kuma ina jinjina wa makaranta littattafaina, ina son su kamar yadda suke so na. Alherin Allah ya isa gare su a duk inda suke. Sannan har gobe da jibi ba zan fasa faɗi masu cewa, duk inda suka ga rubutuna ko maganata, su yi mani addu’ar gamawa da duniya lafiya, da fatan Allah Ya yi wa zuri’ata albarka da addu’ar Allah Ya kai rahama ƙabarin aminiyata Zahara’u Baba Yakasai da ɗanta Shuraim. Allah Ya sa suna cikin kyakkyawan masauki, Amin.
~~~~~~~












