An Ɗaure Shi Shekara Biyu Saboda Ya Saci Mudun Wake
Daga Wakilinmu
•••••••

Wata kotu a Jihar Adamawa, ta yanke wa Iliya Abdullahi hukuncin zama gidan yari na tsawon shekara biyu saboda an kama shi da laifin satar mudu ɗaya na wake.
Iliya, mai shekara 31, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Shelleng ne a Jihar Adamawa. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Kotun Area 2 da ke garin Shelleng ce ta same shi da laifin, wanda ta ce ya saɓa wa Sashi na 277 na Kundun Dokoki na Finalkod.
Bayan an yanke masa hukuncin ne, sai aka tura shi zaman jarun a ranar 15 ga wannan wata na Nuwamba, 2025. Sai dai kuma daga bisani Allah ya kawo masa sauƙi, inda Shugabar Kwamitin Duba Al’amuran Gidajen Yari ta Jihar Adamawa, wacce kuma ita ce Babbar Jojin jihar, Mai Shari’a Hafsat Abdulrahman ta duba lamarinsa.
Babbar Jojin ta Jihar Adamawa, a yayin da ta ziyarci gidan yari na garin Shelleng, a ranar Larabar da ta gabata, shi ne ta binciki lamarin shari’ar Iliya. Bisa kan haka ta gano cewa hukuncin ya yi tsauri, inda ta sassauta masa daga ɗaurin shekara biyu zuwa shekara ɗaya kacal.
Mai Shari’a Hafsat, a yayin da take masa wannan sassauci, ta shawarci Iliya da ya gyara ɗabi’unsa a nan gaba, ya zama mai kyakkyawar tarbiyya. Ta ce ya daina sata kuma ya zama ɗan ƙasa nagari, mai tallafa wa cigaban ƙasa da al’umma.
_______________













