• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, July 28, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sinadarin Rayuwa

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

SINADARIN RAYUWA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 24, 2025
in Sinadarin Rayuwa
0
Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

Bawan Damina...

38
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

November 30, 2025
A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

November 11, 2025
Bawan Damina…


                            •••••••
A wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, a yau za mu maida hankali ne wajen bayyana muhimmancin da ke tattare da aiki. Ke nan, maimakon da muke yawan surutu, muna cewa “zan yi kaza” ko kuma “ya kamata in yi kaza da kaza…” kamata ya yi mu maida hankali kacokan wajen aikata abin da muka ƙudurta.

A rayuwa, magana ba ta canza komai sai an aiwatar. Mutum na iya yin shiri ko yin shela ko yin alƙawari amma abin da ke haifar da canji shi ne aiki. Idan mutum ya mai da hankali ga yin aiki fiye da yin surutu, zai ga canje-canje a hankali suna bayyana a rayuwarsa. Wannan ƙa’ida ce da ta tabbata a tarihin duniya. Har kullum masu yin aiki ne suke cin moriyar nasara, ba masu hayaniya ko surutu kamar kanari ba.

Na farko, domin mutum ya samu nasara, dole ya ɗauki mataki kan duk wani abu da yake da burin cin mawa. Manyan buƙatun rayuwa ko burace-burace, ba su cika ta hanyar magana kaɗai. Dole ne sai mutum ya tashi, ya saka himma, ya yi ɗawainiya, ya nuna juriya da dagewa.

Mutum ya kasance mai yin ƙoƙarin aikata wani abu a kullum, ko da ƙanana ne, da haka ake samun nasara sannu a hankali. Masu iya magana ma sun ce, da tsattsafi gulbi yake cika. Mutumin da bai tsaya ya yi surutu ba, sai dai ya natsu ya yi abin da ya dace, shi yakan fi samun sakamako.

Na biyu, sarrafa ƙudurori a aikace na buƙatar tsari da bin matakai, kamar dai yadda magini yake bin tsarin gininsa mataki-mataki. Abu na farko shi ne, ka rubuta burin da kake so ka cin mawa, ka rarraba su zuwa ƙananan matakai, sannan ka ɗauki matakin aikatawa a kai a kullum.

Idan ka bar burinka a zuciya kawai kuma ka ƙi binsa da aiki, to hakan bai isa ba. Kafin ka samu nasarar cika wannan buri, dole ka yi ƙoƙari a zahiri. Da zarar ka saba da yin aiki kullum, babu abin da zai hana ƙudurinka ko burinka ya cika. Daga ƙaramin aiki, sai ya girma a hankali, har ya zama babba. Daga nan nasara za ta samu, wadda za ka yi alfahari da ita.

Na uku, ya kamata ka san cewa nasara ba ta zuwa da sauri. Ita nasara sakamakon aiki ne da ke taruwa na tsawon lokaci. Aikin da aka ɗauki lokaci ana yi ba tare da gajiyawa ba. Mutum ya kamata ya ɗauki aikinsa da muhimmanci kuma bisa tsari. Misali, kamar noman gona, sai a fara da shara, sai huɗa, sai shuka. Daga nan kuma sai noma, zuba taki da sauran ɗawainiya har zuwa girbi.

Haka kuma, akwai abin lura dangane da kowane aiki. Mutum kan fuskanci ƙalubale, a duk lokacin da yake haƙilon cika burinsa. Wani lokacin mutum kan ji kamar ya gaji, ya ji kamar ma ya watsar da aikin da ya faro. Amma idan mutum ya dage, ya jajirce da haƙuri, sai ya ga nasara.

Muhimman masana falsafar rayuwa da dama sun yi magana kan muhimmancin aiki fiye da magana. Fitaccen masanin falsafa Thomas Carlyle ya taɓa cewa: “Burin da ya fi dacewa da ɗan adam shi ne aiki, ba tunani ko surutu kaɗai ba.” Wannan shi ke ƙara tabbatar mana da cewa aiki shi ne ginshiƙin duk wata nasara da mutum ke son samu a rayuwa.

Ya kai ɗan uwa, ka sani, aiki ya fi surutu, domin surutu ba ya ƙirƙirar sakamako amma aiki yana iya sauya rayuwa gaba ɗaya.
_______________

Previous Post

An Ɗaure Shi Shekara Biyu Saboda Ya Saci Mudun Wake

Next Post

Dharmendra: Ta’aziyyar Bankwana Da Mashahurin Afto

Related Posts

Kada Ka Karaya Da Rayuwa
Sinadarin Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

November 30, 2025
A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne
Sinadarin Rayuwa

A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

November 11, 2025
A Rayuwa Babu Abin Da Ya Kai Haƙuri
Sinadarin Rayuwa

A Rayuwa Babu Abin Da Ya Kai Haƙuri

November 9, 2025
Next Post
Dharmendra: Ta’aziyyar Bankwana Da Mashahurin Afto

Dharmendra: Ta'aziyyar Bankwana Da Mashahurin Afto

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

General Buratai (A Poem)

General Buratai (A Poem)

April 26, 2026
Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

July 17, 2023
KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (2)

KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (2)

July 27, 2025
NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

August 13, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • A Voice for Eternity
  • A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions
  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

A Voice for Eternity

A Voice for Eternity

July 28, 2026
A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions

A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions

July 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.