Lallai Ne A Sallami Shugaban Hukumar Zaɓe – Majalisar Musulunci
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta Najeriya, wacce take ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III ta fitar da wata sanarwa mai zafi, inda ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta korar sabon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, bisa kalaman da ya furta, waɗanta majalisar ta ayyana a matsayin ƙazafi da cin mutunci ga addinin Musulunci.
Majalisar, a wata takardar manema labarai, ta bayyana cewa Farfesa Amupitan ya yi rubutu a kafar Soshalmidiya, inda ya danganta Shehu Usman Danfodiyo, wanda ake yi wa laƙabi da Mujaddadin Musulunci da yaɗuwar ta’addanci da kisan Kiristoci a Najeriya.

Wannan, a cewar Majalisar, babban sharri ne da kuma ƙoƙarin tozarta tarihi da martabar shahararren gwarzon Musulunci, wanda ya shimfiɗa ilimi da adalci a Arewacin Najeriya.
Bayan cikakken nazari da binciken kalaman Farfesan, Majalisar ta ce bai dace mutum mai irin wannan tunani ya ci gaba da riƙe muƙamin Shugaban Hukumar da ke da alhakin tafiyar da manyan zaɓe a ƙasar da take da mabiya addinai daban-daban ba. “Irin wannan ra’ayi, yana nuna wariya da tsana ga Musulunci da Musulmi kuma yana iya jefa ƙasar nan cikin rikici da rashin amincewa da tsarin zaɓe” a cewar sanarwar.
Haka kuma Majalisar ta yi Allah wadai da kalaman da ta kira “maganganun maƙiya Musulunci.” Ta kuma jaddada cewa Shehu Usman Danfodiyo ba ya da alaƙa da wani nau’i na ta’addanci ko tashin hankali. A maimakon haka, ya yi jihadi ne ta hanyar ilimi, adalci da wayar da kai waɗanda suka haifar da ci gaban al’umma a zamaninsa.
Majalisar ta kuma yi gargaɗin cewa, ba za ta lamunci cin zarafin Musulunci ko mashahuran shugabanninsa ba, musamman daga mutanen da suke riƙe da muƙaman gwamnati. Ta ce wannan lamari ya zama tamkar fitina da nuni da son zuciya, wanda zai iya lalata amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati.

Majalisar ta Musulunci kuma ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya gaggauta ɗaukar mataki, domin kare mutuncin Musulmai da kuma tabbatar da cewa adalci ya tabbata a tsarin gwamnati. A cewar Majalisar, irin wannan lamari yana buƙatar tsauraran matakai don kauce wa tashin hankali da rikice-rikice masu tushe a addini.

Majalisar ta roƙi Allah Maɗaukakin Sarki ya kare Musulunci daga sharrin maƙiya, ya tabbatar da zaman lafiya da adalci a Najeriya, tare da ɗaukaka kalmar Musulunci a cikin zuciyar dukkan bayinsa.
_______________












