• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, June 13, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (8)

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 13, 2025
in Babban Labari
0
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (8)

Injiniya Tukur Hassan Tingilin, FNSE

33
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (8)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

June 12, 2026
Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

June 11, 2026
Zannan Galadima, Injiniya Tukur Tingilin, a yayin jawabi a zauren karrama DPO na Malumfashi, CSP Bello Umar da sauran masu taimakon al’umma ta fuskar tsaro a Malumfashi da kewaye

 

                       _______________

Jama’a masu bibiyar wannan rahoto mai kama da muƙala, wannan shi ne rahoto kashi na 8, dangane da wannan babban taro da aka gudanar na Malumfashi Facebook Connect. Idan ba mu mance ba, an gudanar da taron ne a ranar Lahadi, 12-12-1446 (Hijiriyya), 08-06-2025 (Miladiyya).

Kamar yadda muka yi alƙawari, a wannan rahoton za mu yi bayani ne game da ɗaya daga cikin jajirtattun mutanen da aka karrama a wannan taron. Wannan kuwa shi ne Manajan Darakta na Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina, Dokta Tukur Hassan Tingilin, FNSE.

√ Wane Ne Dokta Tukur Tingilin?

Tukur Hassan Tingilin. An haife shi ne a Unguwar Tingilin Malumfashi, Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina, a ranar Asabar – 4 ga Rajab, 1398 (Hijiriyya), daidai da 10 ga Yuni, 1978 (Miladiyya). Ya yi karatu mai zurfi, tun daga firamare, har zuwa matakin da ya samu Digirin Digirgir (PhD) a fannin Injiniya da ya shafi Ilimin ƙarafa (Mechanical Engineering). Ya yi gwagwarmayar neman ilimi a wurare da dama a cikin Najeriya da ƙasashen waje, musamman ma dai ƙasar China, inda a can ya yi karatun Digiri na biyu da na uku.

Injiniya Tingilin hadimin jama’a ne. Ya yi aikin koyarwa, kamar kuma yadda ya kasance mai fafutukar taimakon al’umma ta hanyar ƙungiyoyin sa-kai na tallafa wa al’umma. Haka kuma shi ɗan siyasa ne, wanda ya sadaukar da kansa domin hidima wa jama’arsa. A yanzu haka, shi ne Manajan Darakta na Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina.

A hagu, Dokta Tingilin yana gaisuwa ga Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi, Mai Shari’a Sadiƙ Abdullahi Mahuta

√ Dalilin Karrama Dokta Tingilin:

Ba Injiniya Tukur kaɗai ba, dukkan waɗanda aka karrama a wannan taro, mutane ne da sunansu ya buga tambari wajen taimakon al’umma a Malumfashi da kewaye, kamar mutane irin su Dokta Bala Funtua, Injiniya Muntari Sagir, Jibrin Sama’ila Jibson, Haruna Musa Rugoji da sauransu. Don haka an karrama Injiniya Tukur Tingilin a wannan taro ne bisa cancanta.

A hagu, Injiniya Tingilin, a yayin tattauna al’amuran tsaro

Tun ma kafin ya kai ga hawa wannan muƙami na Manajan Darakta a Gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa, duk wanda ya san shi, ya san mutum ne shi da ya saba da gudanar da ayyukan tallafa wa al’umma, musamman ma ta fuskar aikin gayya, ilimi da abin da ya shafi tallafi ga majinyata a asibitocinmu.

Ya zuwa yanzu, maganar gaskiya ba za a iya lissafa irin yawan tallafi da gudunmawar da Dokta Tingilin yake bayarwa ga al’umma ba, musamman ma ta hanyar gidauniyarsa ta Zanna-Wali Foundation. Duk fannin da ka duba, abin da ya kama da ɓangaren tsaro, harkar lafiya, ruwan sha, ilimi da kuma tallafin kuɗi kai tsaye ga mabuƙata, Injiniya yana yin iyaka ƙoƙarinsa.

A hagu, Injiniya Muntari Sagir tare da Alhaji Jibrin Sama’ila Jibson, a zauren taron Malumfashi Facebook Connect

Wata babbar ɗabi’a aka shaidi Dr. Tingilin da ita, ita ce ɗabi’ar jajircewa da ƙoƙarin neman na kansa. Yana da karimci da kara. Yana girmama mutane kuma ba ya ramuwar gayya.

Waɗannan dalilai da ma wasunsu da dama, su ne dalilan da suka sanya ya kasance ɗaya daga cikin zaratan mutanen Malumfashi da aka karrama a wannan babban taro. A lokacin da za a miƙa masa kambin karramawa, ba ya wajen taron, domin kuwa a lokacin yana ƙasa mai tsarki, Makka, wajen aikin Hajji. Muna yi masa fatan alheri.

A dama, Alhaji Jibrin Sama’ila Jibson ne yake amsar kambi daga Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Alhaji Mukhtar Abdullahi, a zauren taron

Ina sha Allahu, a rahoto na gaba, kashi na 9, za mu tattaunawa a kan DPO na Malumfashi, CSP Bello Umar, wanda shi ma aka karrama, saboda gudunmawarsa ta fuskar tsaro a Malumfashi da kewaye.
_______________

Previous Post

Sasanci Da ‘Yan Bindiga: A Sake Duba Lamarin Nan A Tsanaki

Next Post

Bayan Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina: Ya Kamata A Tallafa Wa Iyalan Mutanen Da Aka Tarwatsa

Related Posts

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar
Babban Labari

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

June 12, 2026
Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato
Babban Labari

Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

June 11, 2026
Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano
Babban Labari

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Next Post
Bayan Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina: Ya Kamata A Tallafa Wa Iyalan Mutanen Da Aka Tarwatsa

Bayan Sulhu Da 'Yan Bindiga A Jihar Katsina: Ya Kamata A Tallafa Wa Iyalan Mutanen Da Aka Tarwatsa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

LAMENTATION FOR MAIDUGURI

LAMENTATION FOR MAIDUGURI

September 10, 2024
Rusau A Kano: An Fara Kama Ɓarayin Kayan Mutane

Rusau A Kano: An Fara Kama Ɓarayin Kayan Mutane

June 5, 2023
A PRAYER

A PRAYER

September 29, 2024
Wakilin RFI HAUSA Malam Kabir Yusuf Ya Rasu

Wakilin RFI HAUSA Malam Kabir Yusuf Ya Rasu

July 3, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe
  • FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco
  • Yau Za A Fafata Tsakanin Canada Da Bosnia-Herzegovina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe

Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe

June 13, 2026
FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco

FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco

June 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.