Prince Abdussamad Badamasi: Allah Tashi Kafaɗarka
Daga Sagir Magaji

•••••••
Assalamu alaikum. Wannan ƙarin bayani ne dangane da rashin lafiyar da wannan bawan Allah yake fama da ita da kuma neman taimako da aka wallafa a kafar sadarwa ta Facebook. Maganar gaskiya, abin da aka wallafa na game da yekuwar neman taimako, lamarin ba gaskiya ba ne kuma ba daga wajen Prince Abdussamad Badamasi abin ya fito ba.
Hasali ma, shi bai da masaniyar za a yi hakan amma tabbas, a matsayinsa na majinyaci, yana buƙatar addu’a daga al’umma domin yana fama da rashin lafiya.
Yadda abin ya faru shi ne, manyan masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Jihar Katsina ne suka yi sanarwar cewa za su je su duba lafiyarsa, domin tun da yake kwance ba su taɓa zuwa duba shi ba. Kuma sun yi wannan sanarwa ce a guruf nasu na Whatsapp. Dalili ke nan Sakataren ƙungiyar ya ce gaskiya ba za su je duba shi hannu biyu ba, ya kamata su haɗa wani abu su kai masa. To dalilin da ya sa suka yi wannan rubutu ke nan da Turanci, wanda yanzu haka yake yawo a kafar facebook da sunan nema wa majinyacin taimako.
Maganar gaskiya makusantansa ba su ji daɗin wannan al’amari na yayata neman taimakon kuɗi ba kuma sun nuna ɓacin rai game da al’amarin. Sai dai kuma sun sanar da ni cewa tabbas Prince ba shi da lafiya kuma yana buƙatar addu’a daga al’umma.
Muna roƙon Allah ya ba Prince lafiya kuma waɗanda suka aikata wannan al’amari na yekuwar neman kuɗi domin jinyarsa su kula, domin gaba. Allah ya kiyaye gaba, amin.
_______________













