• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 4, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Ya Kamata Marubuta Mu Karkata Alƙalaminmu Ga Matsalolin Al’umma

_ NAFISA AUWAL

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
May 26, 2025
in Adabi
0
Ya Kamata Marubuta Mu Karkata Alƙalaminmu Ga Matsalolin Al’umma

Marubuciya Nafisa Auwal da littafinta TAURARUWA

27
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ya Kamata Marubuta Mu Karkata Alƙalaminmu Ga Matsalolin Al’umma
– Nafisa Auwal

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
Marubuciya Nafisa Auwal da littafinta TAURARUWA

 

                             _____

Nafisa matashiyar marubuciyar Hausa ce mai ƙoƙari. A wannan tattaunawa da Taskar Gizago, ta bayyana al’amura da dama da suka shafi rubutu da marubuta. Ta koka game da masu rubutun batsa a Soshalmidiya, kamar kuma yadda ta buƙaci marubuta gaba ɗaya da su karkata alƙalaminsu kan matsalolin al’umma domin kawo gyara. Ga abin da take cewa:

_____

TG: Mu fara da cikakken sunanki da kuma tarihinki a taƙaice.

Nafisa: Sunana Nafisa Auwal Abubakar kuma ni haifaffiyar Jihar Kano ce Ƙaramar Hukumar Nassarawa, Unguwar Brigade-Gama, Mazaɓar Ƙaura-Goje.

TG: Yaushe kika fara makarantar boko da Arabiyya kuma ya zuwa yanzu, mene ne matakin iliminki?

Nafisa: Na yi makarantar firamare a Ƙaura-Goje Primary School, inda na yi sakandare a Makarantar ‘Yan Mata da ke Brigade-Gama, G.G.A.S.S Gama-Tudu. Na yi karatun addini a makarantar Nana Asma’u Bintu Fodio Islamiyya da ke Unguwar Kwana Huɗu, inda na samu nasarar sauke Alƙur’ani mai girma.

TG: Yaushe kika fara rubutu kuma me ya ja hankalinki ga rubutu?

Nafisa: Na fara rubutu tun ina aji uku a makarantar firamare, sanadiyyar yawan karance-karancen littattafai da nake yi tun ina ‘yar ƙanƙanuwata kuma hakan ya samo asali daga yawan gani da nake yi yayyena mata suna karatun litattafan, ni ma sai na kwaɗaitu. Daga haka na fara.

TG: Ya zuwa yanzu littattafai nawa kika rubuta, guda nawa aka wallafa a takarda, guda nawa aka wallafa a soshalmidiya?

Nafisa: Ya zuwa yanzu na rubuta littattafai sun kai guda ashirin amma a cikinsu guda ɗaya ne na buga a matsayin littafi sai kuma shiri da nake yi na fitar da ƙarin wasu guda biyu a bana, sannan ban taɓa sakin littafina a Soshalmidiya ba.

TG: Cikin littattafanki, wanne ne ya fi kwanta maki a rai kuma saboda me?

Nafisa: Cikin littattafaina na fi son Tauraruwa, ba wai don ya fi dukkan labaran da na rubuta ba sai don kasancewar shi ne na farko da na fara cika burina da shi a wallafa littafi, sannan kuma na buga shi cikin nasara; ya karɓu sosai fiye da yadda na yi tsammani.

TG: A matsayinki na marubuciya, wane ƙorafi ke gare ki dangane da harkar rubutu da wallafa?

Nafisa: Ba ni da wani ƙorafi a kan rubutu da wallafa sai dai ina da takaici a kan wasu daga cikin marubutanmu, musamman na Shoshalmediya da suke amfani da baiwarsu wajen yin rubutu na batsa, wanda wannan a gani na zubar da ƙimar rubutu da marubuta ne. Kullum fatana Allah ya sa su gane cewa ita baiwa ba sai an kauce hanya take cika baiwa ba. Akwai marubuta da suka shahara ba tare da sun kauce hanya ba.

TG: Ko wane alheri kika samu daga harkar rubutu, wanda ba za ki mance da shi ba?

Nafisa: Rubutu ya samar mini da alherai da dama na kuɗi da alfarma da damarmakin rayuwa da abubuwa da dama, waɗanda ba lallai ma na iya zayyano su baki ɗaya ba.

TG: Ko kina nadamar zama marubuciya?

Nafisa: Ban taɓa nadamar zama marubuciya ba. Hasalima, ina jin alfahari duk lokacin da na tuna cewa ni ma ina da wata baiwa da ba kowa ke da irinta ba, sannan duk lokacin da aka kira ni marubuciya ina farin ciki kuma ba na fatan wata rana ta zo da zan yi nadamar zama marubuciya.

TG: Mene ne babban burinki a rayuwa dangane da rubutu?

Nafisa: Dukkan wani buri da na fara rubutu domin cin masa, alhamdu lillah, na cin masa. Sai dai da yake mutum ba ka raba shi da buri, to a yanzu kam burina shi ne alƙalamina ya yi kaifin da zai yi rubutun da zai kawo sauyi ga matsalolin al’umma zuwa nan gaba.

TG: Ko kina da wani kira na musamman ga gwamnati da attajiri da ma sauran al’umma dangane da harkar rubutu da wallafa?

Nafisa: Kira na ga marubuta ne kaɗai. Ina fatan za mu mayar da hankali wajen yin rubutu a kan matsalolin da suke addabar al’ummarmu a halin yanzu saboda fargar da jama’a da sauran shugabanni, domin su mayar da hankali ga jama’a da buƙatunsu.

Previous Post

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

Next Post

HANJIN JIMINA

Related Posts

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Next Post
HANJIN JIMINA

HANJIN JIMINA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

I Will Tackle Banditry Head-on – Governor Radda

I Will Tackle Banditry Head-on – Governor Radda

August 24, 2024
Kasafin 2024 Ya Fitfita Jaddada Ajandar Sassaita Nijeriya – Idris

Kasafin 2024 Ya Fifita Jaddada Ajandar Sassaita Nijeriya – Idris

December 4, 2023
Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
ƊANLADI HARUNA

ƊANLADI HARUNA

July 12, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.