Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
•••••••

A ranar Asabar mai zuwa, al’umma daga sassa daban-daban na Jihar Katsina da ma ƙasar baki ɗaya za su taru a garin Malumfashi, domin shaida wani muhimmin biki na tarihi, na naɗin Wazirin Galadiman Katsina, Alhaji Shehu Musa Ɗankano, wanda shi ne tsohon Ɗan Iyan Galadiman Katsina.
Wannan sarauta ta Waziri da mai girma Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi, Mai Shari’a Sadiƙ Abdullahi Mahuta ya ba shi, ya nuna amincewa da girmamawa ga irin rawar da Alhaji Shehu ya taka a rayuwarsa ta hidima ga ƙasa da al’umma.
Alhaji Shehu Musa Ɗankano mutum ne da aka san shi da kishin ƙasa da kishin al’umma. A duk inda aka same shi, yakan yi magana mai cike da ƙaunar ci gaban Arewa da Najeriya gaba ɗaya. Mutum ne da yake da hangen nesa, wanda ke ganin cewa zaman lafiya, ilimi da noma su ne ginshiƙan cigaban al’umma.
Baya ga kishinsa ga ƙasa, Alhaji Shehu babban manomi ne na zamani. Ya shafe shekaru yana ba da gudunmawa wajen bunƙasa harkar noma, ta hanyar amfani da sabbin hanyoyin noma da fasahohi na zamani. Ya kasance abin koyi ga matasa da manoma masu tasowa, saboda jajircewarsa wajen nuna cewa noma har yanzu shi ne babban tushe na arzikin ƙasa.
A fannin aikin gwamnati kuwa, Alhaji Shehu Ɗankano ya yi suna saboda gaskiyarsa, amincinsa, da ɗa’a a wurin aiki. Ya yi ritaya cikin mutunci da girmamawa bayan kammala aikinsa na shekaru da dama a ma’aikatar Gwamnatin Tarayya. Abokan aikinsa da ma na ƙasa da shi, suna yawan yabonsa a matsayin jagora mai gaskiya, wanda ya bar tarihi na kyakkyawan shugabanci da aminci.
Yanzu haka, bayan barin aikin gwamnati, Alhaji Shehu Musa Ɗankano yana ci gaba da hidima ga al’umma ta wata hanya mai ma’ana, kasancewarsa Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (Arewa Consultative Forum – ACF) reshen Jihar Katsina. A matsayinsa na shugaban wannan ƙungiya, yana amfani da ƙwarewarsa da hikimarsa wajen haɗa kan al’ummar Arewa da tallafa musu a fannoni da dama.
Naɗinsa a matsayin Waziri ba kawai alamar yabo ba ce amma wata girmamawa ce ta musamman ga mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga jama’a. Wannan sarauta za ta ƙara ƙarfafa matsayinsa a cikin masarautar Galadiman Katsina, tare da ba shi dama ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kai da ci gaban al’umma.
A yayin da muke tsumayen ranar bikin naɗi, muna fatan cewa sabon Waziri, Alhaji Shehu Musa Ɗankano, zai ci gaba da yin amfani da wannan matsayi wajen tallafa wa cigaban masarautar Galadima da Jihar Katsina baki ɗaya. Sarautarsa za ta kasance wata hanya ta ƙarfafa zumunci, ilimi, da ci gaban tattalin arziki a tsakanin al’umma, musamman ma a fannin noma da haɗin kai na Arewa.
•••••••
Masoya Wazirin Galadiman Katsina, kuna da wasu kalmomi na fatan alheri, taya murna da addu’a ga Alhaji Shehu Musa Ɗankano? Ku rubuta a Comment Section:
_______________














Allah ya taya riko
Amin Amin ya Allah.