• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, June 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

HANJIN JIMINA

WAƘEN FASAHA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
May 27, 2025
in Adabi
0
HANJIN JIMINA

Hanjin Jinjina

5
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

HANJIN JIMINA
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

_____

Related posts

ALHAMDU LILLAH

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Hanjin Jinjina

Bismillah ni zan fara,
Da godiya gun Allah,
Ubangiji Rahamanu,
Mai juya dukkan yayi,
Ba zan gaza yo dace ba.

Ni nai yabo ga Rasulu,
Manzo mijin su Khadijah,
Baban su Rukayya, Fatima,
Gwarzo Badadin Allah,
Tsira da amincin Rabba.

Ya ‘yan uwa ku taho nan,
Ku ban aron kunnuwanku,
Zan ɗan zubo tambihi,
Ɗan tsokaci da nasiha,
Ban zaɓi tozarci ba.

Lallai mu lura mu gane,
Yau zamani ya canza,
Ya zo da launi-launi,
Wani baɗini, wani buɗe,
HANJIN JIMINA ne babba.

Yau ga waya ta salula,
Ta ƙunshi tsarin tsurfa,
Wani kam da kyau, ba laifi,
Wani har akwai amfani,
Wani kau guba ne babba.

Yau waya fa ta zama tsani,
Mai ingiza aikin fasadi,
Wasu na ta nuna tsiraici,
Wasu ma suna yin sata,
Kaico! Abin bai kyau ba.

Ga abin takaici muraran,
Wannan waya ‘yar hannu,
Ɗalibanmu duk ta kangarar,
Ta hana su duba kitabu,
Sai sharholiya ba wai ba.

Wasu na ga matan aure,
Sam ba su tsoron Allah,
Shaiɗan suke wa aiki,
Ta salula sun zama fajirai,
Ba su daina shashanci ba.

Yau ga matasan namu,
Sun daina neman tsaba.
Sun riƙe waya don Yahoo,
‘Yan damfara ba lasi,
Aikin ga bai rana ba.

Kaicon budaren namu,
Wai don gadarar suna,
Sun mamaye kan TikTok,
Aure suke gun jinsi,
Ba su bar rawar tamɓele ba.

Yau ina iyayen yara?
Lallai ku buɗe idanu,
Ku ne kuke tarbiyya,
Aikinku ne ku yi gyara,
Ba ku ga zaman hutu ba.

Ya ku matasa ku gane,
Mazanku har matanku,
Ku mai da hankali sosai,
Ilimi fa shi ne tsani,
Mai shi ba zai taɓe ba.

Ku kiyayi aikin kasada,
Na Shaiɗan baban adawa,
Limamin haddasa fitina,
Shi ne uban salula,
Mai bin shi bai dace ba.

Lallai ku riƙe karatu,
Na Allah, har da na boko,
Sannan ku ɗau tarbiyya,
Ku guje wa illar salula,
Ba kwa rasa yin toho ba.

Mai baituka dai ni ne,
Bashir Yahuza Gizago,
Malumfashi garina,
Na roƙi Allah dace,
Ba zai ƙi tanyo na ba.
– Tammat –
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi
Alhamis, 24-11-1446 (Hijiriyya)
22-05-2025 (Miladiyya)
__________

Previous Post

Ya Kamata Marubuta Mu Karkata Alƙalaminmu Ga Matsalolin Al’umma

Next Post

Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

Related Posts

ALHAMDU LILLAH
Adabi

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
Next Post
Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

I was a security guard – Tinubu addresses Nigerians in India

I was a security guard – Tinubu addresses Nigerians in India

September 8, 2023
SAƘON ADDU’A DA TAYA MURNA GA SHUGABAN JAMI’AR FUDMA: FARFESA AMINU ADO KAFUR

SAƘON ADDU’A DA TAYA MURNA GA SHUGABAN JAMI’AR FUDMA: FARFESA AMINU ADO KAFUR

May 19, 2025
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

July 10, 2025
ZUWA GA MALAM NUHU RIBADU (NSA)

ZUWA GA MALAM NUHU RIBADU (NSA)

July 20, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji
  • Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)
  • POSITIVE COMRADE

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

June 7, 2026
Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

June 3, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.