ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)
Daga Yahuza Malumfashi

Ko Me Ya Sasm ‘Ya’Yan Ƙungiyar Hausawa Suke Suka Da Zagin Ɗanfodiyo (RTA)?
Assalamu alaikum, ya ku ‘yan uwa masu bibiyar muƙalar nan da haƙuri. A yau za mu ci gaba da tattauna al’amarin ‘ya’yan Ƙungiyar Hausawa Zalla.
Kamar yadda na faro bayani a muƙalar nan Kashi na 4, yau ma zan ɗora da tambayar da ta danganci Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo (RTA), wanda ingantaccen tarihi ya yi masa adalci, a matsayin wani babban jigon da ya jaddada Musulunci kuma ya kafa babbar daular da ta yi shuhura a Afrika ta Yamma.
Har yanzu dai muna tambaya, shin wane dalili ne ya sanya masu ƙumajin kafa Ƙungiyar Hausawa Zalla suke sukar wannan bawan Allah kuma suke ci masa mutunci, suke ƙirƙirar tarihin ƙarya, suna jingina masa?
Ga duk mai tu’ammali da kafafen Soshalmidiya, tabbataccen abu ne cewa, zai ga yadda ‘ya’yan ƙungiyar nan suke zaƙewa wajen cin mutunci ga Mujaddadi da dukkan waɗanda suke da dangantaka da shi, tun daga kan ƙabilarsa ta Fulani; har zuwa kan Sarkin Musulmi na yanzu, Mai Alfarma, Sultan Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, CFR. Haka kuma, mutum zai ga yadda suke kushe addinin Musulunci, kai tsaye ko kuma a kaikaice.
Ko a makon nan da ya gabata, mun ci karo da wani bidiyo yana yawo, inda wata mai suna Kaltume, wacce take kwarmata cewa ita ce shugabar wannan ƙungiya ta Hausawa Zalla ta duniya baki ɗaya, tana furta baƙaƙen maganganu game da Musulunci da Musulmi.
A bidiyon, ta fito ƙarara tana faɗin cewa a yanzu ita kafura ce, ta bar Musulunci. Har ma ta yi kira ga Hausawa, wai daga yanzu su daina amfani da kalmomin Larabci wajen sallama. Ta ce, maimakon a riƙa cewa “Assalamu alaikum…” sai dai su riƙa cewa “Gafaran ku dai…” Wannan ke ƙara nuna maka cewa, lallai wannan ƙungiya ba don ci gaban al’umma aka nufa da ita ba.
Ya ku ‘ya’yan Ƙungiyar Hausawa Zalla, an fa yi walƙiya, duk wani mai hankali ya gano wallenku. Babbar manufarku dai ita ce, haddasa fitina tsakanin al’umma, musamman al’ummar Hausawa da Fulani, waɗanda a halin yanzu ‘yan uwan juna ne ta fuskar zamantakewa da addini da ma auratayya tsakanin juna.
Babban burinku shi ne, ku wargaza al’ummar Arewa, ku haddasa gaba da tsanar juna tsakanin al’umma. Burinku ne kuma ku yaƙi addinin Musulunci da Musulmi. Dalili ke nan kuka ɓullo da alayen kishin Hausawa, domin ku yi ɓadda-bami, ko kuma abin da ake kira”BA-ZATA,” domin ku shammaci mutane, ba tare da sun yi aune ba.
Jama’a, yau ma a nan zan dakata. Ina sha Allahu a kashi na 6, zan ci gaba, inda za mu amsa tambayar cewa; shin Mujaddadi Ɗanfodiyo, taimakon Hausawa ya yi ko cutar da su ya yi?
A ci gaba da bibiyar mu da haƙuri. Ku huta lafiya.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online).
_______________
Kuma muna maraba da sharhi ko tsokaci ko tambaya a kan wannan maudu’i a Comment Section.
_____
👇













