• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, April 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

KE YARINYA: ANYA KUWA YANA SON KI DA GASKE?

TSAKURE DAGA LITTAFIN ƘYALLIN NAIRA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
February 22, 2025
in Adabi
0
KE YARINYA: ANYA KUWA YANA SON KI DA GASKE?

Littafin Ƙyallin Naira na Bashir Yahuza Malumfashi

49
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

KE YARINYA: ANYA KUWA YANA SON KI DA GASKE?

Littafin Ƙyallin Naira na Bashir Yahuza Malumfashi

•••

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026

Ya kalle ta guƙi, idanuwansa a cikin nata ya ce: “Ga ki kyakkyawa, son kowa ƙin wanda ya rasa. Ga ki da fasali da kyan diri, ga ƙuruciya, wacce kowane ɗa namiji ya kalle ki zai ji e, yane-yane!

“Kuma ba ki rasa manema ba fa, domin ga su nan birjik! A kullum kika fita sai an samu masu tayawa. Mazaje na gaske, attajirai, ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati; waɗanda daɓensu ya gama jin makuba.”

‘Yar Auta dai har yanzu tana sauraren shi ba tare da ta ce uffan ba. Shi kuwa bai tsaya ba, ya ci gaba da maganarsa. “A cikin maneman naki, akwai wani guda ɗaya tamkar da dubu, wanda ke share maki kowane irin kuka – madamar kuɗi na maganinsa.

“Kin fi ƙarfin motar shiga ta zamani, komai tsadar ta. Kin fi ƙarfin muhalli mai kyau mai tsada, mai ƙaye, cike da kayan alatu na zamani.

“Wayar zamani komai tsadar ta, kina cikin sahun farko na masu mallakar ta.

“Kin fi ƙarfin kuɗin kashe galarin gabanki. Kina kyauta da Dala ba Naira ba. Kin maida Saudiya, Dubai da sauran manyan biranen duniya kamar ƙasashen haihuwarki.

‘Yar Auta

“A taƙaice dai, a duk rayuwarki, babu abin da kika rasa sai abu ɗaya – Aure! Kin shaida mani cewa, a duk lokacin da kika yi wa maneminki maganar aure, ba ya so. Ɓata rai yake yi. A taƙaice ma, kwanakin baya da kika sake tada masa da batun AURE, fitowa ya yi hoha, ya shaida maki cewa: “Ni fa ina son ki ne kawai amma ba da AURE ba! Don haka, kada ki ƙara yi mani maganar aure a sha’anin rayuwarmu!”

‘Yar Auta ta ja dogon numfashi, fuskarta a murtuke kamar hadarin da ke shirin zubar ruwa; ta kalli mutumin da take kira da Yaya amma ta kasa furta komai. Ta sake duƙar da kai ƙasa, wani hawaye mai ɗumi ya fara biyar kumatunta.

“Ke nan lokaci ya yi da ya kamata ki nazarci rayuwarki.” Yayan nata ya ci gaba da magana. “Ki yi karatun-ta-natsu, tun kafin lokaci ya gama ƙure maki. Ki tambayi kanki, shin me ya sa mutumin nan yake wadata ki da komai na rayuwa amma bai son maganar aure a tsakaninku?”

Bayan ya yi shiru na kamar daƙiƙa uku, sai ya ƙara cewa: “Auta, ki ƙara tambayar kanki; shin anya da gaske wannan mutumin yana son ki?”
_______________
Tsakure daga BABI NA UKU, a littafin KYALLIN NAIRA na Bashir Yahuza Malumfashi.

Previous Post

GENERAL ABACHA: A LETTER FROM HEAVEN

Next Post

Minista Idris Ya Taya Gwamna Bago Murnar Cika Shekara 51

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
Minista Idris Ya Taya Gwamna Bago Murnar Cika Shekara 51

Minista Idris Ya Taya Gwamna Bago Murnar Cika Shekara 51

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

October 5, 2025
BAYAN KAMMALA TARON HAƊIN KAN ƘASA A NIJAR, KO ƘUDURORIN TARON ZA SU YI TASIRI?

BAYAN KAMMALA TARON HAƊIN KAN ƘASA A NIJAR, KO ƘUDURORIN TARON ZA SU YI TASIRI?

February 20, 2025
GWAMNAN JIHAR NIGER YA ƘADDAMAR DA YAƘI DA TSAGERU DA ƁATAGARI

GWAMNAN JIHAR NIGER YA ƘADDAMAR DA YAƘI DA TSAGERU DA ƁATAGARI

April 23, 2025
Aure Sunnar Ma’aiki: Taya Murna Ga Uba Nagari Shehu Musa Sarkin Ƙofa

Aure Sunnar Ma’aiki: Taya Murna Ga Uba Nagari Shehu Musa Sarkin Ƙofa

October 26, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.