• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, September 21, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
November 10, 2023
in Labarai
0
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 wanda Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sa wa hannu a ranar Laraba, ya na da muhimmanci matuƙa.

Related posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026

Bayanin ya biyo bayan wani kalami da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya yi, inda ya ce akwai rashin tunani a kasafin, kuma bai kamata ba.

Idris ya ce kasafin ya zama wajibi a daidai wannan lokaci, domin fuskantar hanyoyin magance waɗansu matsalolin da suka shafi tattalin arziki da ake fuskanta yanzu a Nijeriya.

Minista Idris ya yi kira ga Obi cewa ya samu lokaci, ya zauna ya natsu ya yi nazarin kasafin na Naira tiriliyan 2.17 dalla-dalla, wanda ya ƙunshi: tsaro, bunƙasa fannin noma da wadata abinci, ayyuka da gidaje, ƙarin albashi da biyan alawus-alawus ga ma’aikata, bayar da rance ta ɗaliban jami’o’i da na makarantun gaba da sakandare, bada tallafi ga marasa galihu da sauran su.

Cikin wata sanarwa da Hadimin Minista a Fannin Yaɗa Labarai, Rabi’u Ibrahim ya fitar a ranar Alhamis, Minista Idris ya ce babban abin da ake buƙatar a cimma shi ne ƙarfafa tubulan da ke ɗauke da tattalin arzikin ƙasa, domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

“Abubuwan da ke cikin kasafin duk kyakkyawan tunani ne da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bijiro da shi, saboda shauƙin sa na ganin ya taimaka ma’aikatun gwamnati sun fara gudanar da muhimman ayyukan raya ƙasa a cikin gaggawa, musamman maida hankali kan matsalolin tsaro, da kuma gaggauta ɗora tattalin arzikin Nijeriya kan hanyar farfaɗowa cikin sauri, bayan cire tallafin fetur da aka yi,” inji Idris.

Daga nan sai ministan ya shawarci ‘yan adawa cewa su riƙa yin nazarin alfanu da alherin duk wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnati ta bijiro da su, kafin su kushe shi tukuna.

Ya ce yin nazarin kafin su faɗi ra’ayin su abu ne mai fa’ida, domin a ko da yaushe su na da ‘yancin bayyana ra’ayi.

Idris ya ce ba ido-rufe aka bijiro da wannan ƙaramin kasafi na Naira tiriliyan 2.17 ba, sai da aka tuntuɓi masana da sauran dukkan masu ruwa da tsaki, kuma suka tabbatar da cewa kasafin ya yi daidai da buƙatun ‘yan Nijeriya a wannan lokacin.

A ƙarshe Idris ya tabbatar wa Obi cewa a kasafin an bi ƙa’idar tantance sahihancin adadin kuɗaɗen da kowace kwangila ke buƙata, kamar yadda Shugaba Tinubu ya bijiro da tsarin bin diddigin kwangiloli da tabbatar da an kashe kuɗaɗe ta hanyoyin da suka dace.

Previous Post

Harkokin Adabi A Arewacin Najeriya: Jiya, Yau Da Gobe

Next Post

An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

Related Posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post
An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

June 17, 2026
Tsakanin Gwamna Bago Da Wasu Malamai…

Tsakanin Gwamna Bago Da Wasu Malamai…

July 21, 2026
YAU TAKE SALLAH! BARKA DA SALLAH!

YAU TAKE SALLAH! BARKA DA SALLAH!

June 28, 2023
TSOKACINMU NA YAU (11)

TSOKACINMU NA YAU (11)

March 11, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.