• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Harkokin Adabi A Arewacin Najeriya: Jiya, Yau Da Gobe

Dokta Bukar Usman, OON by Dokta Bukar Usman, OON
November 10, 2023
in Babban Labari
1
Harkokin Adabi A Arewacin Najeriya: Jiya, Yau Da Gobe
42
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Harkokin Adabi A Arewacin Najeriya: Jiya, Yau Da Gobe

Daga Hagu: Dr. Yusuf Saeed, Dr. Bukar Usman da Farfesa Ibrahim Garba Satatima (wanda ya wakilci Shugaban Jami’ar Bayero Kano)

~~~~~~~

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026

Wannan jawabi ne na musamman da Dokta Bukar Usman, OON ya gabatar a Taron Ƙasa na 13 mai taken ‘Harkokin Adabi A Arewacin Najeriya’ wanda ya gudana a Jami’ar Abuja, a ranar 31 ga Oktoba, 2023.
~~~~~~~

Gabatarwa:
Jawabina zai karkata ne dangane da harkokin adabi a Arewacin Najeriya. Zai karkata ne wajen haska yadda harkar take kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka, zamanin da suke mulki da kuma bayan tafiyar su. Haka kuma zan taɓo yadda mata suka ɓullo cikin harkar adabi da yadda Kano ya zama wata matattara ta adabi a Arewacin Najeriya. Daga ƙarshe kuma jawabin zai taɓo makomar Adabi a nan gaba a Arewacin Najeriya.

Yankin Arewacin Najeriya:
Kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya, yankin Arewacin Najeriya ba a tantance shi ba sosai. Wannan ya kasance ne saboda shahararrun masarautun ƙasar Hausa, kamar Kebbi a Arewa Maso Yamma, a can baya tana ƙarƙashin mulkin Daular Songhai, wacce ikonta ya dangana har zuwa Agadas da a yau take cikin Jamhuriyyar Nijar. Haka kuma ta yi iyaka da wasu yankuna na Daular Kanem-Borno ta ɓangaren Arewa Maso Gabas, wanda ya dangana har wajajen Fezzan da Tibesti, Arewacin ƙasar Chadi a yanzu. Bayan Taron Berlin ne, a shekarar 1885, inda aka karkasa ƙasashen Afirka zuwa manyan ƙasashen Turai, Gwamnatin Birtaniya ta turo jami’inta na soja, Lord Frederick Lugard, domin ya kula mata da yankin Neja, kasancewar yankin mallakin ta ne da ta samu da ƙarfin soja. Wannan al’amari ya faru ne a shekarar 1897.

Gwamna Lugard ya iske Daular Sakkwato bunƙasassa, da garuruwan da ke ƙarƙashinta, wacce ta faro daga Sakkwato a Arewa Maso Yamma, zuwa Adamawa ta ɓangaren Gabas, zuwa Ilorin, ta ɓangaren Kudu. Wannan masarauta ta Sakkwato, tana ƙarƙashin mulkin Amir (daga bisani aka riƙa kiran shi da Sarki). Wannan daula, Usman Ɗanfodiyo ne ya kafa ta, ta hanyar Jihadi, inda ya samu galaba kan sarakunan ƙasar Hausa, waɗanda a can baya suke mulkin kusan dukkan garuruwan da a yanzu suke a Arewa Maso Yamma.

Wannan daula ta Sakkwato, ta rayu daga shekarar 1803 har zuwa shekarar 1903, lokacin da Gwamna Lugard ya ci ta da yaƙi. Haka kuma, shi dai Lugard ɗin tare da sauran kwamandojin soja suka mamaye Kudancin tsohuwar Daular Kanem-Borno, wacce ta yi zamani daga ƙarni na 9 zuwa na 15. Kafin cinye ta da yaƙi, a can baya wannan daula ta Kanem-Borno, tana ƙarƙashin mulkin Rabeh Fadlallah. Daga nan kuma sai shi Lugard da sauran kwamandojin Gwamnatin Birtaniya suka mai da hankalinsu ga sauran yankuna da garuruwan da ke Kudu, waɗanda ke wajen Daular Sakkwato da ta Kanem-Borno.

Turawan Mulkin Mallaka ne suka shata wa Arewacin Najeriya iyakokinta a hukumance, bisa tsarin ƙasa da ƙasa, kodayake iyakarta da ƙasar Kamaru ta ɓangaren Yamma sun bar shi sasakai ba tare da ranta cewa ba har zuwa lokacin da Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta yanke hukuncin shari’a tsakanin Najeriya da Kamaru a watan Satumba, 2002. Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ƙarfafi Hukumar Haɗaka Tsakanin Najeriya da Kamaru a watan Nuwamba, 2002, domin ɗabbaƙa hukuncin kotun ta duniya. Wani abin lura kuma shi ne, wani yanki na Daular Oyo daga ɓangaren Arewa da ya kasance ƙarƙashin Daular Sakkwato, an haɗa shi ya zama cikin Arewacin Najeriya.

A halin yanzu da muke zancen nan Arewacin Najeriya ya ƙunshi Babban Birnin Tarayya, Abuja da kuma jihohi 19, waɗanda aka yayyanka zuwa shiyyoyi uku. Waɗannan shiyyoyi da jihohinsu su ne: Arewa ta Tsakiya – Biniwai, Babban Birnin Tarayya Abuja, Kogi, Kwara, Nasarawa, Neja da Filato. Arewa Maso Gabas -:Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. Sai kuma Arewa Maso Yamma – Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sakkwato da Zamfara.

Yankin Arewacin Najeriya ya yi iyaka da Jamhuriyyar Kamaru ta ɓangaren Gabas. Ta ɓangaren Arewa da Arewa Maso Gabas kuwa ta yi iyaka da Jamhuriyyar Nijar. Sannan kuma ta yi iyaka da Jamhuriyyar Benin ta ɓangaren Yamma.

Ma’anar Adabi:
Idan muka yi la’akari da yawan malaman jami’a da suka mamaye zauren taron nan, ba za mu ɓata lokaci wajen faɗaɗa bayani game da ma’anar kalmar adabi, kamar yadda ta kasance taken taron nan ba. Maudu’in taron dai kamar yadda aka sani, shi ne: Dangantakar Adabi Da Muhalli A Arewacin Najeriya. Don haka idan muka bijiro da gajeren bayani game da ma’anar adabin ma za ta wadatar. Don haka, ma’anar Adabi shi ne, wani al’amari da rubuta ko aka bayyana da baki ko aka zayyana a hoto, ko aka sassaƙa a jikin wasu abubuwan kamar dutse ko ƙwarya da itace domin adana al’adun al’umma.

Al’umma ta samu damar samar da rubutaccen adabi ne ta hanyar ƙirƙira da fasaha, ta amfani da alamomi domin aika sakonni. A zamunna da suka shuɗe a baya, al’ummu a yankunan duniya daban-daban sun samar da haruffa domin fassara ƙwayoyin sauti. Waɗannan ƙwayoyin sautin ake haɗawa su samar da kalmomin da al’umma suka yi tarayya wajen amincewa da ma’anoninsu. Sannu a hankali har aka samar da na’urorin ɗab’i a kimiyyance, tare da ƙa’idojin rubutun wasu yarukan al’umma.

Ita kuwa al’ada tana nufin duk wata halayya ko ɗabi’a ko aiki da ke wakana yau da kullum a cikin al’umma, wacce kuma wani mai ba da labari ko marubuci ya tattara ko ya rubuta a matsayin tarihi. Wannan dalili ne ma ya sanya ake da rukunoni biyu na adana tarihi, rukunonin baka da na rubutu. Marubuta da masu bayar da labari ne ke yin sharhi da tsokaci dangane da al’amuran da ke faruwa cikin al’umma ko kuma su bayyana mana tarihin al’amuran da suka shuɗe a baya, waɗanda suka shafi zamantakewar al’umma, tattalin arziƙi, kimiyya da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire. Waɗannan bayanan su ne ke taimaka wa al’umma dangane da al’amuran rayuwarsu ta yau da kullum. Haka kuma muna da rumbunan bayanai da suka danganci tatsuniya, almara, kaɗe-kaɗe da waƙoƙi, karin magana, zambo, kirari da littattafai ko kundaye bayanai da suka danganci al’amura da maudu”ai da suka shafi al’umma.

Dangantakar Adabi Da Muhalli:
Muhalli na nufin wurin da mutane ke rayuwa da dukkan da’irar da ke tattare da shi. Idan ana batun dangantaka tsakanin adabi da muhalli kuwa, abu ne tabbatacce, cewa halayyar mutane tana samuwa ne daga yanayin muhallin da suke zaune, duk kuwa da cewa ana samun wasu ɗaiɗaikun mutane a cikin kowace al’umma da ake haihuwa da wata baiwa ko halayya ta musamman. Masana halayya da yanayin halittar ɗan Adam sun bayyana cewa, tunanin mutum da ayyukansa duk suna ɗamfare kuma suna samuwa ne ta sanadiyyar yanayin muhallinsa. Haka kuma abin da ke wakana a gidajenmu da garinmu da makarantunmu ko addininmu duk sakamako ne da ke wanzuwa daga muhallinmu da ɗabi’unmu. Bisa ga wannan yanayi na haƙiƙa, adabi yake haskowa a kowace al’umma.

Wani babban misali na dangantakar da ke tsakanin adabi da muhalli shi ne tatsuniya da almara. Ana amfani da dabbobi da tsuntsaye ko wani abu da ke akwai a muhallinmu domin gina tatsuniya ko almara da ke koya darussan rayuwa ga yara domin kyautata tarbiyyarsu. Idan mutum ya ziyarci ɗakunan karatu da shagunan sayar da littattafai a Arewacin Najeriya, zai fahimci wannan batu da muka ambata. Haka kuma idan mutum ya nazarci jigogin littattafan da marubutanmu suka wallafa, duk zai fahimci yadda adabi da muhalli suke da alaƙa da juna. Wannan kuma ba yana nufin cewa marubuta a Arewa ba su duba wasu bangarorin rayuwa masu kayatarwa na daban ba. Marubuta a Arewa kan yi rubutu dangane da wata fahimta tasu, bisa ga wani al’amari da suke da sani ko ilimi a kansa. Abin fahimta a nan dai shi ne, marubuta sukan yi rubutu ne bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummarsu.

A yau, duk wasu littattafai na adabi da ake gani a Arewacin Najeriya, sakamako ne na ƙoƙarin wasu ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi a hannu ɗaya da kuma gwamnatoci, a ɗaya hannun. Yanayin da ake ciki dangane da harkar adabi a yanzu, ya yi ta faruwa ne a lokuta da dama kuma a matakai daban-daban. Harkar adabi a Arewacin Najeriya wani al’amari ne na Gwamnatin Tarayyar Najeriya kuma za a iya karkasa shi zuwa matsayi ko lokuta daban-daban. Za a iya karkasa harkar adabi zuwa lokuta kamar haka: Adabi kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka, adabi a lokacin Turawan Mulkin Mallaka da kuma adabi a bayan Tafiyar Turawan Mulkin Mallaka.

Harkar Adabi Kafin Zuwan Turawan Mulkin Mallaka:
Kamar yadda dogon bayani ya gabata game da Arewacin Najeriya, domin fahimtar harkar adabi a Arewacin Najeriya, wajibi ne a waiwayi yanayin da yankin yake a ƙarƙashin Daular Usmaniyya da Daular Kanem-Borno. A tarihi, waɗannan dauloli sun zauna a ƙarƙashin mulkin Larabawa, ta sanadiyyar yaƙe-yaƙe da kasuwanci. Addinin Musulunci ya samu tasiri, wanda dalili ke nan harshen Larabci ya mamaye harkar adabi a Arewacin Najeriya a wancan lokacin. Kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka a yankin, mutane sun riƙa amfani da haruffan Larabci wajen rubutun Hausa da Fulfulde da Kanuri, a sigar Ajami. A wancan zamanin, masallai ne wuraren ɗaukar ilimi, su ne kamar jami’o’i. Da rubutun Ajami ake amfani domin adana bayanai a kotuna da wuraren mu’amala da jama’a. Haka kuma da harshen Larabci ake amfani wajen koyo da koyar da ilimi da ayyukan hukuma da sadarwa tsakanin ƙasa da ƙasa. Saboda haka, duk mai son fahimtar wani al’amari kai tsaye, a hukumance ko a ilimance da aka rubuta, sai yana da ilimin waɗannan yaruka. A wasu wuraren a Arewacin Najeriya, inda addinin Musulunci ba ya da tasiri, suna adana bayanai ne ta amfani da zayyana da sassaƙa da sauran hanyoyi a gargajiyance, kamar yadda abin yake a mafi yawan wurare a can baya. Haka kuma an riƙa amfani da rubutattun waƙoƙi wajen aika saƙo ko wa’azi da faɗakarwa, kamar kuma yadda hukumomi ke amfani da kalmomi na musamman, domin aika saƙonni na musamman tsakanin jami’an hukuma a Daular Usmaniyya da ta Kanem-Borno. Almajiran Shehu Usman Ɗanfodiyo da muƙarrabansa da ‘yan uwansa da ‘ya’yansa, musamman ma ɗiyarsa da ta yi fice, Nana Asma’u, sun yi amfani da adabi iri-iri wajen harkokinsu.

Harkar Adabi A Zamanin Turawan Mulkin Mallaka:
Tun da farkon zuwan Turawan Mulkin Mallaka daga Birtaniya, sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun kawar da haruffan Larabci, waɗanda da su ne ake amfani tun farko wajen rubuce-rubuce a Arewacin Najeriya; sun maye gurbinsu da haruffan boko da ake kira da “Roman Characters.” Domin cin ma wannan ƙuduri, mahukunta Turawa ba su yi da wasa ba, sun kankane al’amuran adabi a Arewacin Najeriya. A hukumance suka kafa cibiyoyin fassara, samarwa da rarraba littattafan da aka wallafa da haruffan boko a dukkan yankin Arewa. Cibiyoyin da aka kafa, yawancinsu a Kaduna da Zariya aka yi masu mazauni. Sun haɗa da Hukumar Fassara (1929), Hukumar Kula Da Al’amuran Adabi (1935), Kamfanin Wallafa Na Gaskiya (1945) da kuma Cibiyar Fassara Ta Lardin Arewa- North Regional Literature Agency, NORLA (1953). Gwamnatin Mulkin Mallaka ita ce ke yin uwa da makarɓiya dangane da abin da littattafan za su ƙunsa, wallafa su da kuma rarrabawa.

Ba su tsaya a nan ba kaɗai, domin a ƙarfafa harkar adabi ta amfani da haruffan boko, dukkan littattafan da aka wallafa, ana sayar da su ne cikin farashi mai sauƙi a dukkan sassan Arewacin Najeriya. Bayan lokaci mai tsawo a wannan turba, sai kuma cibiyoyin wallafa na gwamnati suka ƙulla yarjejeniya da kamfanonin wallafa masu zaman kansu, na cikin gida da na ƙasashen waje, domin samar da littattafan da ake buƙata. Waɗannan manyan kamfanonin wallafa sun haɗa da Kamfanin Macmillan, Kamfanin University Press da kuma Kamfanin Longman. Wani babban ƙoƙari da Gwamnatin Mulkin Mallaka ta yi domin bunƙasa harkar karatu da rubutu a tsakanin ɗaliban makarantun da gwamnati ta samar a Arewacin Najeriya, shi ne shirya gasar rubuce-rubuce. Waɗannan gasanni ne suka haifar da haziƙan marubuta ƙirƙirarrun labarun zube da wasan kwaikwayo a Arewacin Najeriya. Ɗaya daga cikinsu su shi ne Firaminista na farko kuma na ƙarshe a Najeriya, Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa.

Harkar Adabi Bayan Tafiyar Turawan Mulkin Mallaka:
An ba Arewacin Najeriya ‘yancin kai a shekarar 1959, a yayin da ita kuma Najeriya ta samu nata ‘yancin kan a shekarar 1960. Gwamnatin da ta gaji ‘yan mulkin mallaka a Arewacin Najeriya ta yi ƙoƙarin ci gaba da bunƙasa harkar adabi daidai gwargwado, ta fuskar samar da littattafai da kuma kafa Kamfanin Wallafa Na Arewacin Najeriya – Northern Nigeria Publishing Company (NNPC), a 1965. Sai dai kuma gwamnatin ta kasa jure ci gaba da wallafa littatafai da haruffan boko, tare da rarrabawa na tsawon lokaci, kamar yadda ta gada daga Gwamnatin Mulkin Mallaka.

Haka kuma sanadiyyar sake fasalin tsarin lardi-lardi a Najeriya, mai ɗauke da lai huɗu, zuwa ƙirƙiro jihohi 12 a shekarar 1967, wannan ya haddasa mutuwar cibiyoyin nan da Gwamnatin Lardin Arewa ta ƙirƙiro domin wallafawa da rarraba littattafai. Sauran abin da ya biyo na tallafa wa adabi ya koma hannun wasu tsiraru kuma ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi, waɗanda ke rubutu da wallafa littatafai. Gwamnatocin jihohi na Arewacin Najeriya suka riƙa sayen littattafan daga hannunsu suna rarraba wa makarantunsu. Daga baya ne aka miƙa wannan aiki na kula da samarwa da amincewa da irin littattafan da ake buƙatar amfani da su ga Hukumar Bunƙasa Ilimi Da Bincike Ta Najeriya – Nigerian Educational Research and Development Council (NERDC), wacce Gwamnatin Tarayya ta kafa a shekarar 1988.

Sai dai kuma duk da cewa daga bisani an karkasa Lardin Arewa zuwa jihohi 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja, al’adar karatu da rubutun zube da waƙe da wasan kwaikwayo ta ci gaba da gudana, duk kuwa da cewa ta rage harsashi. Kasancewar an faɗaɗa gine-ginen makarantu da cibiyoyin ilimi, wannan ya sanya an samu ƙishirwa da buƙatar littattafan karatu (sakamakon aikin da cibiyoyin bunƙasa adabi da Gwamnatin Mulkin Mallaka ta samar). A kan haka sai aka samu ɓullowar wata guguwar marubuta littattafan Hausa a Kano. An sanya wa wannan sabon yunƙuri na marubuta laƙanin ‘Adabin Kasuwar Kano.’ Wannan laƙanin ya yi salo ɗaya da takwaransa da aka samu a zamanin Turawan Mulkin Mallaka, mai suna ‘Adabin Kasuwar Onitsha ‘ wanda ya yi tashe da ganiya a shekarun 1940 da 1950. Waɗannan sunaye sun samu ne saboda yanayin ingancin littattafan da ake wallafawa ya ragu, musamman ma ta dalilin cire hannu ko kuma sassauta tsaurin daga gwamnati ta ɓangaren samar da littattafai (ba kamar yadda abin yake a hannun Gwamnatin Mulkin Mallaka ba).

Bayyanar Ƙungiyoyin Marubuta:
An samu bayyanar ƙungiyoyin marubuta daban-daban, musamman a Kano, domin bunƙasa harkokin adabi, kare haƙƙoƙin marubuta da taimakon juna tsakanin marubuta. Wannan ya faru ne ta sanadiyyar yadda gwamnati ta sassauta kula da al’amarin adabi. A kan haka aka samu bayyanar wasu mawallafa da ‘yan kasuwar littafi, waɗanda ke ɗaukar nauyin bugawa da sayar da littattafan marubuta, musamman ma waɗanda ba su da kuɗin bugawa idan sun gama rubutawa. Ta dalilin haka ya sanya aka samu rashin ingancin littattafan da irin waɗannan ‘yan kasuwar littafi suke bugawa saboda an samu ƙarancin tsayayyu kuma ƙwararrun kamfanonin wallafa, gami da cewa gwamnatoci sun yi saku-saku da kula da harkokin wallafa.

Bayyanar Mata Marubuta:
An samu bayyanar mata marubuta a Arewacin Najeriya tun can zamanin Daular Usmaniyya, kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka. Ɗiyar Shehu Usman Ɗanfodiyo, Nana Asma’u ce ta share wa mata marubuta hanya, tun a wancan lokaci. Ta yi fice sosai a fagen rubuce-rubuce, musamman ma dai a fagen rubutun waƙa. Ta rubuta waƙoƙi da dama cikin harsunan Hausa da Fulfulde da kuma wasu kaɗan da harshen Larabci. Bayan Nana, an ɗauki lokaci mai tsawo kafin a samu bayyanar mata marubuta da haruffan boko. Ɗaya daga cikin mata marubuta na farko a Arewacin Najeriya, ita ce Hafsat Abdulwaheed Ahmad. Ta yi suna a fagen rubutun ƙirƙirarren labari da Hausar boko, a shekarun 1980. Ita ‘yar asalin Jihar Kano ce.

Yadda aka samu jinkirin bayyanar mata marubuta a Arewacin Najeriya da kuma batun jigon da suka fi maida hankali a kansa cikin rubuce-rubucensu, ya zama maudu’in tattaunawa a fagen adabi. Wani babban dalili da ya haifar da jinkirin bayyanar marubuta mata da wuri, shi ne yadda aka riƙa hana mata shiga makarantun boko a Arewa, aka fi maida hankali wajen saka maza a makaranta.

Mata Marubuta a Arewacin Najeriya sun fito da wani salo na aika saƙonni ga al’umma, musamman domin wakiltar jinsinsu, kasancewar suna ƙorafin cewa maza marubuta ba su yi masu adalci, wajen fito da matsalolin da ke addabar su. Mata marubuta, sun maida hankali wajen bayyana matsalolin mata a rubuce-rubucensu, kamar auren dole, aure tsakanin mabambantan ƙabilu, batun ƙaddara, auren mace fiye da ɗaya, batun rikici tsakanin kishiyoyi, batun haihuwa da raino. Sauran jigogin na rubuce-rubucen mata sun haɗa da batun neman ilimi ga mata, girmama mata ko cin zarafinsu, addini da imani da kuma jin ƙai. Hakan ya yi daidai da karin maganar da ke cewa, mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo. Haka kuma mata sun yarda da batun ciwon ɗiya mace, na mace ne; cewa su suka san zurfin matsalolinsu, don haka su suka fi cancanta su bayyana su. Kodayake akwai yiwuwar cewa suna wuce makaɗi da rawa, wajen zuciya matsalolin da kuma nuna son kai ga jinsinsu na mata.

Irin yadda mata marubuta a Arewacin Najeriya suka maida hankali wajen rubuce-rubuce da suka danganci al’amuran mata, shi ya haifar da wata guguwar rubutu da aka yi wa laƙani da ‘Adabin Soyayya’ ko ‘Littattafan Soyayya.’ Sai dai duk da cewa mata ne suka fi yawa a samar da littattafan soyayya, amma maza marubuta ma sun yi tasiri sosai a wannan fage. Haka kuma an zargi marubutan maza da mata da ragon azanci, inda suke kwafar fina-finan Indiya da na Amurka kai tsaye, su rubuta labaransu da Hausa a littattafansu. Littattafai da fina-finan Hausa sun samu karɓuwa sosai a Arewacin Najeriya. Domin jan hankalin waɗanda ba sa fahimtar Hausa, a yanzu ana saka fassarar Ingilishi a fina-finan na Hausa.

Yadda Kano Ya Zama Matattara Adabi:
A shekarun 1990, Birnin Kano ya yi fice a fagen harkokin adabi a Arewacin Najeriya, domin kuwa ya zama wani matattara adabi, inda marubuta, mawallafa da kamfanonin ɗab’i suka cika kuma suka tumbatsa. Kano ya samu wannan tagomashi da ɗaukaka saboda yana da yawan jama’a kuma da yanayin yadda ya zama wata mahaɗa ta al’ummar Arewacin Najeriya da al’ummomin Afirka ta Arewa da na Gabas ta Tsakiya tun zamani mai daɗewa, wajajen shekarar 1320. Tun a wancan lokaci Kano ya zama wata matattara ta kasuwanci da sana’a, da ake yi wa laƙani da ‘zango.’ Tun a wancan lokaci ‘yan kasuwa daga Kano da sauran Arewacin Najeriya suna yawon kasuwanci zuwa ƙasashe daban-daban na Arewaci da Gabashin Afirka da suka haɗa da misalin Sudan da sauransu. Kano ya zama matattarar da ta samar da musayar ilimi tsakanin masu sana’o’in hannu da masu fasaha da ƙirƙire-ƙirƙiren kayan gargajiya. Haka al’amarin ya haɓaka ta fuskar adabi, inda marubuta da masu karatu maza da mata suka ƙulla alaƙa, suka samar da babbar kasuwar littattafai da ake wallafawa ba a Kano kaɗai ba, har da sauran sassan Arewacin Najeriya.

Makomar Adabi A Nan Gaba:
Kamar yadda aka bayyana a baya, Kano dai ya zama matattarar adabin Hausa. Wani ci gaba da aka samu, shi ne yadda wasu daga cikin marubutan Hausa suka riƙa mayar da littattafansu zuwa fina-finai. Wasu kuma suka riƙa rubutawa suna sayar wa masu shirya fina-finan na Hausa. A kan haka sai ga shi marubutan Hausa suka watsar da rubutun zube, suka rungumi rubutun labarun fim, ba don komai ba sai ganin yadda harkar fim take kawo kuɗi da sauri fiye da wallafa littafi. Duk da cewa an samu ci gaba, harkar adabi ta bunƙasa ta fuskar shirya fina-finai da rubutun zube a Arewacin Najeriya, to amma akwai cikas ta fannin rubuce-rubucen kimiyya da kuma rubuce-rubuce a sauran yarukan Arewacin Najeriya.

Akwai wani cikas kuma ta fuskar adabi a Najeriya, musamman an gaza naƙaltar fasahar yadda za a shirya almara a bidiyo ta amfani da zane-zanen dabbobi (animation). Ta ɓangaren waƙe-waƙe da gambara na zamani kuwa, nan ma an samu ci gaba, domin kuwa ana ta samun ƙaruwar irin waɗannan mawaƙa. Marubuta sun maida hankali wajen rubuta labarun abin da ke faruwa cikin al’umma, musamman ma dai canjin zamani, a sakamakon bunƙasar birane da yadda suka haifar da wasu gurɓatattun halaye da kuma yadda matasa ke ƙaurace wa karkara suna shiga birane saboda ƙyale-ƙyalen rayuwa da ke can. Marubuta suna samar da darussa domin kawo canji a rayuwar al’umma. Haka kuma suna jawo hankalin mutane domin su saba da halayyar karatu. Suna yin rubutu domin samar da nishaɗi da shaƙatawa, musamman a irin yanayin da ake ciki na ƙunci da rashi.

Wani abin lura kuma shi ne, akwai manyan garuruwa a Arewacin Najeriya, kamar Katsina, Zariya, Kaduna, Ilorin, Jos, Bauchi da Gombe da sauransu, da suke da muhimmanci ta fuskar ilimin zamani amma har yanzu ba su kai shaharar Kano ba, idan ana maganar rubuce-rubucen ƙirƙira da fasaha, musamman ma yadda Birnin ya zama matattarar adabi – rubutu, wallafa, shirya fina-finai da kasuwancin su.

Kammalawa:
A yayin da muke kammala wannan jawabi, wani abin da ya kamata a lura da shi, shi ne yadda al’amuran suka riƙa wakana dangane da harkokin adabi a Arewacin Najeriya. Na farko dai kafin zuwan Larabawa da suka kawo fasahar rubutu da haruffan Larabci (Ajami), akwai adabin baka da kuma na zayyana da sassaƙa. Daga bisani kuma aka samu tsarin rubutu da haruffan boko, a lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka zo yankin ke nan. Ta ɓangaren dangantaka tsakanin adabi da muhalli kuwa, wannan al’amari ne da ya zama da’iman a kowane zamani da yanayi. Musamman dai muhalli da yanayin zamantakewar al’umma, su ne ke haifar da abin da ake rubutawa da taskacewa.

Idan ba a ‘yan lokutan nan ba, a can baya, an fi sanin al’ummar Arewacin Najeriya da halayyar sauraren rediyo fiye da karatu. Wannan kuwa ya faru ne a sakamakon ƙarancin ilimin zamani a yankin, idan aka kwatanta da yankin Kudancin Najeriya. Kodayake daga bisani an yi amanna da ilimin na zamani amma duk da haka yawan adadin yaran da ba su zuwa makaranta, al’amari ne mai sosa rai. Mutane a Arewacin Najeriya ba su da halayyar rubuce-rubuce, kodayake a ‘yan lokutan nan an fara samun canji, kasancewar wasu suna rubuta littattafan tarihin rayuwarsu, wasu kuma ana rubuta tarihin wasu fitattu, kamar kuma yadda ake samun wasu masana suna rubuta littattafan ilimi a fannoni daban-daban. Babu shakka akwai buƙatar a bunƙasa halayyar karatu da rubutu a Arewacin Najeriya, duk kuwa da cewa kallace-kallacen talabijin da fina-finai suna kawo wa al’amarin barazana, balle kuma yaɗuwar kafafen sada zumunta na intanet. Daga wani nazari da na yi na ƙashin kaina, na fahimta da cewa al’umma a Arewacin Najeriya suna sha’awar karatu, musamman idan an wallafa littattafan da inganci. Don haka ya kamata a fito da tsare-tsaren kwaɗaita halayyar karatu da rubutu, ya hanyar shirya gasar rubuce-rubuce a fannonin ilimi daban-daban. A maida hankali wajen rubuta littattafan ilimi domin makarantun firamare da sakandare, sannan a mayar da hankali wajen rubuta littattafan da za su fito da kyawawan al’adu da yarukan al’ummu daban-daban na Arewacin Najeriya. Wannan babban ƙalubale ne da ya kamata a fuskanta da gaske. Haka kuma ya kamata a fara koyo da koyar da ilimi cikin harsunan gida, domin a magance ɓacewar harsunanmu na gado da kyawawan al’adunmu.

Haka kuma duk da cewa wallafa jaridu a Arewacin Najeriya na susucewa saboda ɓullowar jaridun intanet, amma abin takaici ne yadda gidajen jaridun suka yi ƙaranci, idan aka kwatanta da Kudancin Najeriya. Wannan kuwa yana ishara ne da cewa akwai ƙarancin ilimin zamani a Arewa.

Ya kamata a ƙara maida hankali wajen bunƙasa ilimin zamani da koyar da shi a Arewacin Najeriya. Ya zama wajibi ga gwamnatocin jihohi da attajirai da ƙungiyoyin sa-kai a Arewa su tashi tsaye wajen bunƙasa ilimi a Arewacin Najeriya. Ya kamata a dawo daga rakiyar alƙawarin ƙarya da romon baka da ake yi wa al’amuran ilimi a Arewacin Najeriya – gwamnati ce ya kamata ta jagoranci wannan babban aiki, bilhaƙƙi da gaskiya.

Ina fatan wannan muhimmin taro zai ba masana da masoya harkokin adabi, ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi dama da ƙwarin gwiwar tantance yanayin da adabi a Arewacin Najeriya yake ciki, domin su ba da gudunmawa wajen bunƙasa shi. Haka kuma su tantance masu himma da ƙoƙari a fagen hidimta wa adabi, domin ƙarfafa su, su ci gaba da bunƙasa adabi a wannan yanki. Babu mamaki, daga sakamakon wannan babban taro, za a iya tantance inda adabi ya dosa, wajen bunƙasa da yaɗuwa a Arewacin Najeriya.

Ina matuƙar godiya ga kowa.
~~~~~~~
Dokta Bukar Usman, OON, makiyayin hikimomin al’umma, marubuci, shi ne Shugaban Ƙungiyar Makiyaya Hikimomin Al’umma. Tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja. Ya gabatar da wannan jawabi a ranar 31 ga Oktoba, 2023.
~~~~~~~

Previous Post

KANA SON FAHIMTAR MATA?

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

Comments 1

  1. flagstoneveneydel2q9+2esq9a57g5nd@gmail.com says:
    2 years ago

    ut sunt perspiciatis ut laboriosam qui id voluptatum rerum aut nihil et veritatis suscipit et ex natus. voluptas sed non quia debitis ab assumenda occaecati.

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General – Dr. Bukar Usman

BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General – Dr. Bukar Usman

April 14, 2025
Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

Health: Daura sets to commission Federal Medical Center

September 9, 2023
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

May 24, 2025
AREWA (A Poem)

AREWA (A Poem)

August 19, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.