Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Birgediya Janar S.K. Usman (mai ritaya) ya kammala karatun Digirin-Digirgir (Doctor of Philosophy – PhD) a fannin Nazarin Tsaro da (Defence and Security Studies) a Kwalejin Horar da Sojojin Najeriya, Nigerian Defence Academy (NDA), Kaduna, bayan shafe shekaru yana gudanar da bincike mai zurfi, jajircewa da kuma sadaukar da kai wajen ci gaba da neman ilimi.
Janar Usman, Sarkin Yaƙin Kanwan Katsina, ya karɓi takardar shaidar digirin PhD ɗinsa a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, a yayin bikin yaye ɗalibai na 36 da Kwalejin NDA ta gudanar. Wannan nasara ta kasance wani babban ci gaba a rayuwarsa ta karatu da kuma aiki.
Tsohon babban jami’in sojan ya bayyana wannan nasara a matsayin cikar wani babbar buri da ya daɗe yana nema a fannin karatu, yana mai cewa shekarun da ya shafe yana gudanar da bincike da jajircewa sun haifar da sakamakon da yake fata.
Janar Usman, wanda ya taɓa zama Mai Magana da Yawun Sojojin Ƙasar Najeriya, ya bayyana godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki da kuma iyalansa, masu kula da bincikensa, malamai da masu ba shi shawara, abokan aiki da sauran waɗanda suka ba shi goyon baya da ƙwarin gwiwa a tsawon wannan tafiya ta neman ilimi mai cike da ƙalubale.
Bikin ya kasance na musamman ga iyalan Usman, domin ’yarsa ta fari, Nabeelah Sani Usman, ita ma tana cikin waɗanda suka kammala karatun Digiri na biyu (Master’s) a wannan bikin yaye ɗalibai.
A cewar Birgediya Janar Usman, yin bikin nasarar karatun uba da ’ya a lokaci guda a wannan babbar makarantar koyar da harkokin soji ya sanya ranar ta zama abin tunawa da kuma cike da farin ciki da gamsuwa ga iyalinsa.
Ya ce samun Digirin-Digirgir ba wai kawai ƙarin wata takardar shaidar ilimi ba ce, illa dai wata alama ce da ke nuna muhimmancin jajircewa, ladabtar da kai, ci gaba da neman ilimi da kuma ƙoƙarin neman sani.
Haka kuma, Janar Usman mai ritaya ya bayyana matuƙar farin cikinsa da samun wannan Digirin-Digirgir daga NDA, wadda ɗaya ce daga cikin manyan cibiyoyin ilimi a Najeriya da suka yi fice wajen koyar da ilimin soja, tsaro da harkokin kariyar ƙasa.
Ya ce zai yi amfani da ilimi da ƙwarewar da ya samu a yayin karatunsa na Digirin-Digirgir wajen ƙara bayar da gudunmawa ga ilimi da bincike, sadarwar dabarun ƙasa, tattaunawa da nazarin harkokin tsaro da kariyar ƙasa, da kuma ci gaban Najeriya.
Wannan nasara ta ƙara wani muhimmin matsayi a tarihin tafiyar karatu da sana’a ta Birgediya Janar S.K. Usman (mai ritaya), yayin da kammala karatun ’yarsa da Digirin Master’s a lokaci guda ya ƙara wa bikin yaye ɗalibai na 36 na NDA armashi, tare da mayar da shi wani muhimmin abin tunawa ga iyalan Usman.
__________













