• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, August 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Shugabanci A Aikace: Gwamna Raɗɗa Ya Jagoranci Jami’an Tsaro Wajen Farautar ‘Yan Ta’adda

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 9, 2023
in Babban Labari
0
Shugabanci A Aikace: Gwamna Raɗɗa Ya Jagoranci Jami’an Tsaro Wajen Farautar ‘Yan Ta’adda

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa, yana ba da umurni ga jami'an tsaro, yayin farautar 'yan ta'adda

67
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Shugabanci A Aikace: Gwamna Raɗɗa Ya Jagoranci Jami’an Tsaro Wajen Farautar ‘Yan Ta’adda

Gwamna Raɗɗa a bakin aiki
Gwamna tare da jami’an tsaro

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya jagoranci jami’an hukumomin tsaro na jihar zuwa farautar ƙasurguman masu aikata laifi, musamman ‘yan ta’adda a maɓuyarsu a ƙaaryar birnin Katsina.

Related posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026

A wata takardar manema labarai da Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamna, Ibrahim Kaula Mohammed ya rarraba, ya ce Gwamna Raɗɗa da kansa ya shiga gaba, ya jagoranci jami’an tsaron, inda suka farmaki maɓuyar ‘yan ta’addar da daren Talatar da ta gabata.

“Tun misalin ƙarfe 10 na dare suka fita aikin, har zuwa ƙarfe 11:30,” in ji Kaula.

Kamar yadda bayanan suka gabata, Gwamna da ayarin jami’an tsaron sun shiga unguwannin Sabuwar Unguwa, Sharara Pipe, Ɗanhaƙo, Filin Polo, Ƙofar Guga da kuma Tudun Matawalle.

“Yan ta’addan sun addabi mazauna unguwannin da ma sauran sassan birnin. Cikinsu akwai ɓarayin da suka ƙware a ƙwacen waya da amshe dukiya.” Kamar yadda Kaula Mohammed ya bayyana.

A ƙoƙarinsa na ganin ya kakkaɓe muggan masu aikata laifuka a jihar, Gwamna Raɗɗa ya umurci jami’an tsaro a jihar da su tashi tsaye, su yi aiki wurjanjan domin kakkaɓe duk wani ɗan ta’adda daga jihar.

Haka kuma a safiyar yau Laraba, Gwamnan ya kira taron gaggawa na shugabannin hukumomin tsaro da ke jihar, inda aka tattauna yadda za a magance matsalar tsaro da ta dawo a wasu sassa na jihar.

Ya nuna takaicinsa dangane da ƙalubalen rashin tsaro da ke addabar jihar. Don haka ya buƙaci shugabannin hukumomin tsaron da su ƙara ƙaimi a aikinsu, kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar.

Previous Post

Wa Ke Tsoron Malam Elrufa’i Ya Zama Minista?

Next Post

KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

Related Posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara
Babban Labari

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami
Babban Labari

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026
Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama
Babban Labari

Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

July 30, 2026
Next Post
KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

NASIHA: Waƙen Ƙarfafa Gwiwa

NASIHA: Waƙen Ƙarfafa Gwiwa

July 22, 2023
GOBARA TA TASHI A KASUWAR MADALLA

GOBARA TA TASHI A KASUWAR MADALLA

January 29, 2024
Yau Maulidin Katsina First

Yau Maulidin Katsina First

July 10, 2023
Namu Ya Samu: Kira Da Shawara Ga DCG Abdulbasir Hamisu

Namu Ya Samu: Kira Da Shawara Ga DCG Abdulbasir Hamisu

August 5, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon
  • Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu
  • Musulunci Ba Addinin Tsauri Ko Sakaci Ba Ne…

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon

August 23, 2026
Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

August 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.