KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Daga Mukhtar Mudi Sipikin
Hazbiya ta kalli dandazon Tsuntsayen, ta ce: “Wannan satin fa an sha kwaramniya a dajin nan da kuma maƙwbtansa. Lamarin ma har sai Tsuntsu ya rasa gane wane abu ne ya fi jan hankali?”
Salwa ta ce: “Ni abin da ya ban mamaki shi ne, labarin da na ji a kan tsuntsayen Jihar Kyawawa, da yunwa ta ishe su, har ta kai sun cire tsoro sun fasa rumban tsaki. Gaskiya lamarin da ban tausayi. Tsuntsaye tura ta fara kai su bango fa, lallai Jemage ya kamata ya yi abin da ya dace, don a samu sauƙi.”
Kurciya ta yi murmushin ƙarfin hali, sannan ta kada baki ta ce: “Da alama ba ki saurari hirarsa da masu rahoto ba, ai ya bayyana cewa wai hanyar nan ita kaɗai ce tilo, da za ta kai mu tudun mun tsira!
“Wani abin haushin ma da takaici da rainin hankali, shi ne, wai ya san irin wahalar da mu ke sha, ku ji fa? Jemagen da sama da shekara arba’in bai san wahalar tsaki ba, kullum tsaki yake samu mai taushi ga ruwan sukar yana korawa yana jiƙa maƙoshinsa, yana daga cikin sheƙarsa ba tare da ya fita kiwo ba, wai shi zai kalle mu ya ce “Wai ya san irin wahalar da mu ke sha!” Kullum yana cikin ‘latu da daula, yana tashi cikin ayarin masu gadi, ‘yayansa suna fantamawa sannan…” Kurciya ta fashe da kuka.
Gado da ke gefenta, cikin rarrashi ya ce: “Ki yi haƙuri, tabbas abun na su da rainin hankali. Ni abin da yake ƙara ɓata min rai ma shi ne, tun zamanin Babba-Da-Jaka ake cewa wai za a buɗe rumbu a raba wa tsuntsaye tsaki amma har yau shiru. Ga shi shi ma Jemage ya ɗora da wannan maganar mai kama da tatsuniya, har yau ba tsuntsun da zai tabbatar maka da cewa ya amfana da tsakin da ake cewa an raba!”
Bainu ta ce: “Ni kuma abin da ke ƙara ba ni haushi, shi ne, yadda aka mayar da mu mabarata mayunwata! Wai za a raba mana tsaki kyauta! A faɗa wa Jemage ya riƙe tsakinsa, mu abin da muke so a sassauta mana, mu dinga siye da sulallanmu da arha, mu ba cima zaune ba ne, ba kamar shi da ake ciyar da shi da kuɗinmu ba!”
Tantabara, wadda tun da aka fara hirar ba ta ce komai ba, ta ce: “Ni fa na lura kamar ba ku damu da rigimar da Jemage ke san cilla mu ciki ba ko? Ko ba ku da labarin Jemage ya dage sai ya dawo da hamɓararren Shugaban tsuntsuyen maƙwabtanmu ne?
Wannan abu ba ƙaramar matsala zai cilla Arewancin dajin nan namu ba, lallai ne tsofaffinmu da ‘yan shila, da kowa da kowa ya fito ya yi Allah wadai da wannan aniyar ta Jemage da abokansa.”
Alhudahuda ya ce: “Ƙwarai kuwa, The prospective deployment of Mikiya force by Jemage and co, to countermand “Maƙwbtan Dajinmu” post-coup situation may herald a perilous concatenation of escalating hostilities, imperiling the lives and welfare of hapless civilians. Rather than this precipitate bellicosity, prioritizing the diplomatic entreaty, conciliatory mediation, and political dialogue would proffer a sagacious recourse towards ameliorating the crisis and galvanizing democratic governance and equilibrium…”
“Dakata! Alhudahuda, yanzu fa ba lokacin dogon Turanci ba ne, lokacin aiki ne. Dole ne mu yi wani abu kan wannan matsalar, in Jemage ya yi mana nisa dole mu tilasta wa Majalisar Ragon-Maza da ke wakiltar mu, da zu taka wa Jemage birki!”
Hazbiya ta katse shi.
Kanari ta ce: “Ba don dare ya yi ba, da mun tattauna matsalar ‘yar uwarmu da aka ba ta muƙami aka ƙwace…”
“Ma tattauna wani satin, Allah Ya tashe mu lafiya.” Hazbiya ta katse Kanari. Tsuntsaye suka yi sallama, kowa ya nufi sheƙarsa.
*An hango Ungulu da muƙarrabanta suna ta murnar kasancewar shugaban tsuntsaye masu riƙon Tsintsiyar Daji. Sannan an jiyo su, suna faɗar baƙaƙen maganganu ga Shugaban Rundunar Tsuntsaye Jan-Baki.
~~~~~~~
Malam Mukhtar marubuci, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa ne a Jihar Kano (05-08-2023)
~~~~~~~














Ma sha Allahu, Allah ƙara basira Ya kuma kawo mana ɗauki cikin wannan halin da muke
Amin Amin Ya Allah. Muna godiya da jimirinku na bibiyar jaridar nan. Muna maraba da shawarwari daga gare ku, yadda za mu inganta ayyukanmu, domin gamsarwa gare ku. Mun gode sosai.