• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, November 3, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sharhi

Yadda ‘Yan Mata Suke Tsunduma Cikin Karuwanci A Arewa

TAƁARƁAREWAR TARBIYYA

Aminu Lawan Hassan by Aminu Lawan Hassan
October 26, 2026
in Sharhi
0
Yadda ‘Yan Mata Suke Tsunduma Cikin Karuwanci A Arewa

Yadda 'yan mata ke shiga karuwanci a Arewa

50
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Taɓarɓarewar Tarbiyya: Yadda ‘Yan Mata Suke Tsunduma Cikin Karuwanci A Arewa

Daga Aminu Lawan Hassan

Related posts

Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

June 3, 2026
SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
Yadda ‘yan mata ke shiga karuwanci a Arewa

 

__________

Na tsaya da motata, domin in tsallaka titi, in sayo wasu abubuwa. Kafin ma in fito daga motar, sai wasu ‘yan mata biyu, waɗanda a gani na ‘yan shekaru kusan talatin da ɗoriya, suka ƙaraso ta gefen dama na ƙofar.

Na sauke gilashin motar, sai ɗaya daga cikinsu, cikin murmushi mai ɗaukar hankali, ta tambaye ni cewa:

“Baba, ta hanyar Mandawari za ka yi?”

Na haɗe rai, sannan na amsa mata da wata tsawa mai ƙarfi:

“A’a!”

Ta tsorata ƙwarai, har ta yi saurin ja da baya daga jikin motar.

Na je na sayo abin da ya kai ni wurin, na dawo na shiga motata, sannan na yi tafiyata. Amma tunanina ya ci gaba da kai-komo tamkar mazari.

Na fara tambayar kaina – shin waɗannan mata sun shiga wani hali ne na rashin abin hawa, kuma da gaske taimakon suke nema? Na yi la’akari da musamman, ganin cewa tufafin da suke sanye da su na mutunci ne.

Ko kuwa dai sana’ar nan ta “Good Evening” ce ta ƙaura zuwa Unguwar Sharaɗa, bayan da a baya aka fi sanin ta a yankunan da ke kusa da Randabawul na Central Hotel da Sabon Gari?

Kimanin watanni biyu da suka gabata, na sake fuskantar makamancin wannan al’amari. Na tsayar da motata a kan titin Zoo Road, kusa da shagon Sufi Mart, sai wasu ‘yan mata biyu suka ƙaraso wurina, ɗauke da wani ƙaramin bokiti mai haske, wanda ake iya ganin abin da ke cikinsa.

Ɗaya daga cikinsu ta tambaye ni cikin karin harshen Kanuri:

“Alhaji, za ka siya?”

Ban ma damu da sanin abin da suke sayarwa ba. Kai tsaye na ce musu “a’a.”

Ba tare da ɓata lokaci ba, sai ɗaya daga cikinsu ta sake tambayata:

“To, kana son mata?”

Na shiga matuƙar mamaki! Na buɗe ƙofar motata na fito. Abu na farko da ya faɗo mini a rai shi ne, wataƙila sun ɗauka ni saurayi ne.

Sai na ce musu su bar gefen titin, su zo ɗaya gefen, inda zan iya tattaunawa da su yadda ya kamata.

Na tambaye su abin da suke nufi da kalmar “mata.” Sai ɗaya daga cikinsu ta bayyana mini cewa tana nufin budurawa.

Daga nan na tambaye su daga ina suka fito. Suka ce daga Maiduguri suke.

Da na tambaye su shekarunsu, dukansu biyun suka amsa cikin ƙarfin gwiwa, cewa shekarunsu ashirin ne.

Na ƙara tambayar su inda iyayensu suke. Sai suka ce suna Maiduguri.

Nan take na fara yi musu wa’azi da nasiha, ina ƙoƙarin fahimtar da su irin haɗari da munanan sakamakon hanyar da suke neman bi.

Amma abin da ya fi ba ni mamaki shi ne, ɗaya daga cikinsu ta katse ni da cewa:

“Alhaji, idan ba ka yi, ka bar mu, mu sami wani.”

Daga nan suka juya suka tafi! Abokina, wanda ya shiga cikin shagon sayayya, ya fito ya tambaye ni ko su wane ne waɗannan ‘yan mata.

Na ce masa, “karuwai ne.”

Cikin tsananin mamaki ya ce, “karuwai!”

Sai na amsa masa: “A’a, koyon karuwanci suke yi!”

Har yanzu wannan magana tana sa ni tunanin inda al’ummarmu ta dosa. Shin lalacewar tarbiyya ta kai wannan matsayi ne, har ‘yan mata za su iya tunkarar manyan mutane da rana tsaka, ba tare da jin kunya ba, suna neman su yi lalata da su domin kuɗi?

Me ya faru da tarbiyyar iyaye? Ina iyaye da masu kula da waɗannan ‘yan mata suke? Waɗanne irin yanayi da matsaloli ne suka jefa su cikin wannan hali?

Kuma mene ne irin wannan ɗabi’a take bayyana mana game da halin da al’ummarmu take ciki a yau?

Ba wai ina rubuta wannan bayani ne domin in yi Allah wadai da wani ba, ba tare da fahimtar yanayin rayuwarsa da matsalolin da yake fuskanta ba.

Talauci, cin zarafi da amfani da mutane, tasirin miyagun abokai da sauran matsalolin zamantakewa, suna iya ingiza mutane zuwa aikata abubuwan da ba su dace ba, musamman idan suka tsinci kansu cikin matsanancin ƙuncin rayuwa.

Amma duk da haka, ba za mu iya yin biris da ƙara yaɗuwar wannan matsala ta yadda matasa ke shiga harkokin neman kuɗi ta hanyar lalata a kan titunanmu ba.

Idan har al’umma ta fara ɗaukar abubuwan da ya kamata su tayar da hankali a matsayin al’amuran yau da kullum, to lokaci ya yi da za mu tsaya mu yi tunani mai zurfi, tare da yi wa kanmu wasu tambayoyi masu muhimmanci, ko da kuwa amsoshinsu za su kasance masu wuyar karɓa.

Allah ya shiryar da ‘ya’yanmu, ya kare matasanmu daga faɗawa cikin munanan ɗabi’u, ya kuma dawo da kyawawan ɗabi’un ƙwarai, waɗanda suke zama ginshiƙan haɗin kai da zaman lafiyar al’ummarmu.

Ina rubuta wannan tsokaci ne cikin matuƙar damuwa da tashin hankali a zuciyata, domin ni ma uba ne kuma ina da ‘ya’ya.

__________

Previous Post

Yanzu Dai Ta Tabbata Cewa Arewa Ta Tunibu Ce

Next Post

A Review of Aisha Umar Kadafur Poetry Collection: Echoes of Memory

Related Posts

Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)
Sharhi

Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

June 3, 2026
SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)
Sharhi

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi
Sharhi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024
Next Post
A Review of Aisha Umar Kadafur Poetry Collection: Echoes of Memory

A Review of Aisha Umar Kadafur Poetry Collection: Echoes of Memory

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TSOKACINMU NA YAU (26)

TSOKACINMU NA YAU (26)

March 26, 2025
THE WARRIOR

THE WARRIOR

September 29, 2026
A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

July 4, 2023
TSOKACINMU NA YAU (11)

TSOKACINMU NA YAU (11)

March 11, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa
  • Babban Saƙon Injiniya Muntari Sagir Ga Al’ummar Malumfashi
  • NASIHARMU TA YAU (36)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa

Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa

November 1, 2026
Babban Saƙon Injiniya Muntari Sagir Ga Al’ummar Malumfashi

Babban Saƙon Injiniya Muntari Sagir Ga Al’ummar Malumfashi

October 29, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.