• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 4, 2023
in Adabi
0
A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

Hajiya Uwa Idris

238
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Uwa Idris
Littafin Rabi’at’s Diary

A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

Related posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026

~~~~~~~
Sunanta A’isha Giɗaɗo Idris amma an fi sanin ta da laƙanin Hajiya Uwa. Marubuciya ce mai hazaƙa. Ta rubuta littattafai da dama a cikin Ingilishi da Hausa. A yanzu kuwa sunanta ya buga tambura a soshalmediya, inda take rubuce-rubuce da suka shafi zamantakewar aure da soyayya tsakanin maza da mata. Wasu na yi mata kirari da Lauyar Maza. Domin sanin cikakken tarihi da gwagwarmayar da take sha a fagen rubutu, Taskar Gizago ta tattauna da ita:
~~~~~~~

TG: Kina ɗaya daga cikin marubuta na dauri, ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice?

Hajiya Uwa: Ni sunana A’ishatu Giɗaɗo Idris, ana kuma kira na da laƙanin Uwa.
An haife ni ne a garin Zariya, watan Yuli, 1960.
Ban yi nisan karatu ba, yadda mutane da yawa suke zato. Na yi makarantar firamare a wurare da yawa. Amma na fi daɗewa a makarantar kwana ta Kakuri.

TG: Tun yaushe kika fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinki ga harkar rubuce-rubuce?

Uwa Idris: Na fara rubutu a 1991 ne, a lokacin da nake fuskantar ƙalubale game da zamana da mijina, a matsayin matarsa ta farko a lokacin. A lokacin ne na rubuta littafina na farko, mai taken “Rabiat” wanda na Turanci ne.

TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa kika buga a intanet?

Uwa Idris: Na rubuta littattafai tara. Na Hausa guda biyar, na Turanci guda huɗu. Kuma duk an buga su a takarda.
A intanet kuwa, na saka na Turanci duka a wattpad.com Sauran kuwa na Hausa ne, ban riga na saka ba tukuna.

TG: Waɗanne irin matsaloli kike fuskanta a matsayinki na marubuciya, musamman ma a soshalmidiya?

Uwa Idris: Tabbas matsalolin da nake fuskanta a matsayina na marubuciya a soshalmidiya suna da ɗan yawa, musamman matsalolin sun fi danganta da maganar mata da suke rashin sanin muhimmancin zamantakewar aure mai kyau.
Wasu matan da yawa, sukan ƙi na’am da ra’ayina tare da tunanin ina yawan ba su laifi a abubuwan da ke faruwa tsakaninsu da mazansu.
Wani lokacin kuma, ina samun waɗanda suke mani maganganu cikin zargi, ɓacin rai da adawa.
Wasu kuma su yi mani mummunar fahimta, tare da ganin laifina a rubuce-rubucena da suka danganci aure. Da yawan mutane masu bibiya ta sun sha nuna cewar sun gaji da ina zama lauyar maza.

TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori kika samu ko kuma akasin su?

Uwa Idris: Tun da na fara rubutu, na samu nasorori irin na zama sananniya a al’umma. Kuma ana yawan kallo na a matsayin wadda a hankali za ta kawo canji.

TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenki, da kike koyi da rubutunsu?

Uwa Idris: A marubuta ina koyi da Amina Abdulmaleek, Bashir Yahuza Mulumfashi, Alawiyya Wada Isa da Ibrahim Sheme.

TG: An daɗe ba a ji ɗuriyarki da sabon littafi ba, shin me ya faru, ko kin daina buga littafi ne?

Uwa Idris: Allah Sarki! Ban daina ba. Abin da yake faruwa shi ne, na ɗan shagala ne da rubutu a soshalmidiya. Sai nake ganin bari in ɗan jira sai na tuno da yanayin abin da nake son magana a kai. Amma in sha Allah bayan na gama littafin da ke gabana yanzu, mai taken “A Birkice Ra’ayin Yake” wanda na tarihin rayuwata ne, zan yi rubutu a kan zamani.

TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko ke ma kina da shirin hak?

Uwa Idris: Gaskiya zan so in zama mai rubuta script. Amma ban san yadda za a fara ba.

TG: Mene ne babban burinki dangane da rubutu?

Uwa Idris: Babban burina game da rubutu shi ne, ya zamana rubutu yana karɓuwa, kuma ya zama mara yawa sosai. A wannan zamanin babu abin da ba a so da yawa irin rubutu. Ina fatan a samu marubuta masu koyi da cewar duk abubuwan da yake faruwa a wannan zamanin, ba ƙarya ba ne, kuma su jure da bayanin cewa shi zamani ikon Allah ne.

TG: Ko kina da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanki da kuma al’umma masu karanta littattafanki?

Uwa Idris: Ina kira ga gwamnati da ta kafa hukuma mai kyau ta buga littattafai a kowace jiha, domin ta riƙa tallafa wa marasa ƙarfi, waɗanda ba su iya buga littattafansu da kansu. Sannan zan yi fatan marubuta su riƙa rubutu a kan canjin lokaci da ke ɓata wa matasanmu saiti.

Previous Post

Limamin Kirista Da Mabiyansa Dubu 100 Sun Musulunta

Next Post

Majalisar Dattijai Ta Samu Shugabanni

Related Posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)
Adabi

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
Adabi

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa
Adabi

Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa

August 29, 2026
Next Post
Majalisar Dattijai Ta Samu Shugabanni

Majalisar Dattijai Ta Samu Shugabanni

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

November 13, 2023
Burina In Samar Da Maslaha Tsakanin Ma’aurata – LIKITAR MA’AURATA

Burina In Samar Da Maslaha Tsakanin Ma’aurata – LIKITAR MA’AURATA

August 8, 2023
Shawara Ga Gwamnonin Arewa

Shawara Ga Gwamnonin Arewa

December 2, 2025
Abin Da Ya Sa Muka Karrama Jami’an Tsaro A Malumfashi

Abin Da Ya Sa Muka Karrama Jami’an Tsaro A Malumfashi

October 5, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.