Babban Labari:
Fusatattun Matasa Sun Yi Wa Mataimakin Gwamnan Zamfara Rajamu
Daga Wakilinmu

__________
Wasu fusatattun matasa sun yi wa Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Mani Mummuni, rajamu tare da yi masa ihu, domin nuna rashin amincewa, tare da kai hari kan ayarin motocinsa a garin Gwashi, da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, a jiya Lahadi.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito, lamarin ya faru ne lokacin da Mataimakin Gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar garin, sakamakon harin da aka kai a makon da ya gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da fararen hula guda tara.
Wani mazaunin garin, wanda ya zanta da wakilinmu kuma ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa al’ummar yankin suna cike da fushi da Mataimakin Gwamnan da ma gwamnatin jihar, sakamakon matsalolin tsaro da suke fuskanta a yankin, wanda ake bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan mazaɓun siyasa a ƙaramar hukumar.
Ya ce: “Lokaci na ƙarshe da suka kawo mana ziyara, shi ne sama da shekaru uku da suka gabata, lokacin yaƙin neman zaɓen shekarar 2023. Tun daga wannan lokacin, babu Mataimakin Gwamnan, babu kuma wata tawaga daga Gwamnatin Jihar da ya taɓa ziyartar mu, domin nuna damuwa game da matsalolin tsaro da suke ƙara ta’azzara a yankinmu.”
Ya ci gaba da cewa: “A yau, mun nuna wa duniya irin halin da muke ciki. Mun sha bayyana ƙorafe-ƙorafenmu a lokuta daban-daban amma ba a ɗauki wani mataki na magance matsalar rashin tsaro da ƙarancin ayyukan raya ƙasa ba.”
Mutumin ya ƙara da cewa, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga, al’ummar yankin sun shafe kwanaki shida a jere ba tare da samun damar fita, domin sayen muhimman kayayyakin buƙatun rayuwa ba.
Ya ce: “Mun shafe kwanaki shida zuwa bakwai ba tare da fita daga garinmu ba. Jami’an tsaro sun daina yi wa mutane rakiya, kuma babu wanda zai iya kasadar rayuwarsa ta hanyar fita. Idan muka ƙara shafe wasu kwanaki a irin wannan hali, ku yarda da ni, ko gishiri ma ba za a samu ba.”
Ya kuma koka kan rashin muhimman abubuwan more rayuwa a garin, inda ya ce: “Ba mu da hanyar mota mai kyau da za ta haɗa mu da sauran yankuna. Ba mu da ingantaccen asibiti, haka kuma ba mu da tsaftataccen ruwan sha. Gine-ginen makarantunmu kuwa sun lalace matuƙa.”
Wani mazaunin garin, wanda shi ma ya zanta da wakilin namu bisa sharaɗin a sakaya sunansa, ya bayyana cewa makarantar sakandaren garin ta lalace har ta kai ga dabbobi suna amfani da harabarta, a matsayin wurin fakewa.
Ya ce mata da yara da matasa da tsofaffin garin sun fito domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu ga Mataimakin Gwamnan, tare da nuna rashin gamsuwarsu da yadda Gwamnatin Jihar take tafiyar da al’amura.
A cewarsa, “mun fito da yawa, mata da yara da matasa da tsofaffi, muna yi wa Mataimakin Gwamnan ihun nuna rashin amincewa, muna kuma rera taken ‘Ba ma yi! Ba ma yi!’ Mun san ya zo ne domin neman ƙuri’unmu,l amma ba za mu zaɓe su ba.”
Ya ƙara da zargin cewa fusatattun matasan sun kai hari kan ayarin motocin Mataimakin Gwamnan. Ya yi iƙirarin cewa: “Ko shi kansa Mataimakin Gwamnan da ƙyar ya tsira kuma an lalata wata mota.”
Sai dai wani daga cikin mutanen da suka raka Mataimakin Gwamnan, wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa, ya musanta zargin cewa an kai hari kan ayarin motocin. Ya bayyana cewa masu zanga-zangar suna yankin kasuwa ne, yayin da taron Mataimakin Gwamnan ya gudana ne a kusa da asibitin garin.
A cewarsa, “abin da suke faɗa ba gaskiya ba ne. Mu muna wani wuri ne daban gaba ɗaya. Ita kuma motar da suke iƙirarin an lalata, motar jami’an tsaro ce, wadda ta samu matsalar inji. Daga baya aka yi amfani da wata mota wajen janye ta.”
Sai dai wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa Mataimakin Gwamnan ya zo ne tare da jami’an tsaro masu yawa, waɗanda suka hana mutane isa wurin da yake jawabi ga wasu mutane kan matsalar rashin tsaro.
Majiyar ta ce: “Yawan jami’an tsaron da aka tura wurin ya hana mutane samun damar kusantar Mataimakin Gwamnan, domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Duk da haka, mun yi masa ihun nuna rashin amincewa, tare da jifan ayarin motocinsa da duwatsu.”
“Ko shi kansa Mataimakin Gwamnan, da ƙyar ya tsira saboda matasan sun fusata kan yadda gwamnati ta kasa nuna damuwa da ɗaukar matakan kawo musu ɗauki.”
__________













