• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, July 28, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

Mohammed Bala Garba by Mohammed Bala Garba
August 13, 2023
in Gizago
0
NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

Shugabannin Ƙungiyoyin Musulmin Nigeria da suka gana da Shugabannin Mulkin Sojan Niger

58
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

Daga Mohammed Bala Garba

Related posts

Saƙon Godiya Da Bangajiya

Saƙon Godiya Da Bangajiya

July 22, 2026
MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana

MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana

July 21, 2026

Haƙiƙa mun sani kuma mun yarda, cewa ba Nijeriya ba ce za ta yaƙi ƙasar Nijar, ƙungiyar ECOWAS ce.

Kamar yadda Malam Hasheen ya yi bayani, ƙungiyar ECOWAS ƙungiya ce ta haɗakar ƙasashen yammancin Afrika, irin su: Benin da Burkina Faso da Carve Verde da Cote d’Ivoire da Gambia da Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Liberia da Mali da Niger da Nigeria, Senegal da Sierra Leone da kuma Togo.
Waɗannan ƙasashen sun haɗu ne a ƙaƙashin ƙungiyar bisa yarjejeniyar aiki tare da kuma taimakon kai-da-kai don tabbatar da wanzuwar demokraɗiyya a tsakaninsu. Dalilin da ya sa wasu suke ganin kamar Nijeriya ce za ta yaƙi Nijar shi ne, saboda kasancewarta uwa ko kuma kan gaba a cikin ƙungiyar ECOWAS. Wannan kuma ya biyo bayan ƙarfin tattalin arzikin da take da shi da kuma ƙarfin soja da yawan al’umma. Duk da yake masana da kuma ƙwararru suna ganin ƙasar Nijeriya ita kaɗai (ba tare da haɗaka da wata ƙasa ba) za ta iya yin karin kumallo da sojojin juyin mulkin Nijar, ta mayar da farar hula kan mulki, amma kuma wasu na ganin reshe zai iya juyewa da mujiya, saboda yaƙi ɗan zamba ne.

Ko ba don wannan ba ma, akwai wasu dalilai da ya sa kaso mai yawa na al’ummar Nijeriya (ko kuma Arewancin ƙasar) ba sa goyon bayan yunƙurin ECOWAS. Daga cikin akwai:

1- Arewancin Nijeriya zai shiga tsaka-mai-wuya da hatsari saboda yadda abin zai shafi yankin ta dalilin maƙwabtakar da yake yi da ƙasar Nijar, musamman a wannan lokacin da yankin yake farfaɗowa daga cikin yaƙin da aka shafe sama da shekaru goma ana yi da Boko haram. Wannan ya sa mafi yawa ko na ce masu hangen nesa ba sa goyon baya.
2- Dalili na biyu shi ne, lamarin zai shafi fararen hular da suke ƙasar Nijar da kuma waɗanda suke Arewancin Nijeriya. Domin yaƙin ba a iya kan sojoji zai tsaya ba (mu dubi ƙasar Sudan a matsayin misali).
3- Sannan kuma zai ƙara durƙusar da kasuwancin da ke tsakanin Nijar da Nijeriya ko kuma Arewancin Nijeriya.
4- Rashin sanin abin da yaƙin zai iya haifarwa, saboda yaƙi ɗan zamba ne. Shin ECOWAS ce za ta yi nasara ko kuwa sojojin juyin mulkin Nijar ne? Sannan kuma mene ne makomar al’ummar Nijar da na Nijeriya bayan yaƙin?
5- Mu ‘yan Nijeriya da muke ƙarƙashin demokraɗiyya a yanzu, me ta tsinana mana a tsawon lokacin da aka kwashe ana yi har da za mu jefa rayukan wasunmu a hatsari? Wannan tunanin ire-irena ne masu ƙananan hange.
Waɗannan dalilai da kuma ƙarin wasu, su suka sa mafi yawan al’ummar Nijeriya ko kuma na Arewacin Nijeriya ba su goyon bayan yunƙurin ECOWAS na amfani da ƙarfin soja a kan ƙasar Nijar. Idan da wata hanyar da ya kamata a ɓullo (ban da yaƙi) domin dawo da farar hula kan karagar mulki a Nijar, to muna murna amma ba mu yarda da yaƙi ba. Idan kuwa babu, to a ƙyale al’ummar ƙasar Nijar da mu kanmu mu zauna lafiya. Domin ba ƙasar Nijar ba ce kaɗai sojoji suke mulki a cikin Afirka.

Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya a ƙasarmu da maƙwabtanmu da Afirka da ma duniya baki ɗaya, Amin.
~~~~~~~
Mohammed Bala Garba, marubuci/manazarci ne. Ya aiko saƙon nan daga Maiduguri (09, Agusta, 2023).
~~~~~~~

Previous Post

TAURARON GIZAGO: Idris Ibrahim Kubau

Next Post

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

Related Posts

Saƙon Godiya Da Bangajiya
Gizago

Saƙon Godiya Da Bangajiya

July 22, 2026
MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana
Gizago

MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana

July 21, 2026
Tsakanin Gwamna Bago Da Wasu Malamai…
Gizago

Tsakanin Gwamna Bago Da Wasu Malamai…

July 21, 2026
Next Post
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Malamina Yana Sauke Alƙur’ani A Ƙasa Da Rabin Awa – Sheikh Maƙari

Malamina Yana Sauke Alƙur’ani A Ƙasa Da Rabin Awa – Sheikh Maƙari

June 26, 2023
Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Dr. Yunusa Zuba- Abuja

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Dr. Yunusa Zuba- Abuja

August 4, 2023
Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

October 5, 2025
Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai

Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai

September 11, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • A Voice for Eternity
  • A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions
  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

A Voice for Eternity

A Voice for Eternity

July 28, 2026
A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions

A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions

July 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.