• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, September 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Abin Da Ya Sa Muka Karrama Jami’an Tsaro A Malumfashi

- Injiniya Muntari Sagir

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 5, 2025
in Babban Labari
0
Abin Da Ya Sa Muka Karrama Jami’an Tsaro A Malumfashi

Injiniya Muntari Sagir Malumfashi, yayin gabatar da jawabinsa a zauren taron

34
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Abin Da Ya Sa Muka Karrama Jami’an Tsaro A Malumfashi
– Injiniya Muntari Sagir

Daga Wakilinmu

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
Muntari Sagir da Galadiman Katsina Jastis Sadik Abdullahi Mahuta, yayin karrama DPO Bello Umar

_______________
Shugaban Kamfanin Gine-Gine na Muntasarab Global Concept Limited, Injiniya Muntari Sagir Malumfashi ya bayyana cewa babban abin da ya sanya suka karrama DPO na Malumfashi CSP Bello Umar da sauran jajirtattun jami’an tsaro da kuma dakarun tsaro na sa-kai da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi shi ne domin a jinjina masu kuma a ƙarfafa masu gwiwa, domin su ci gaba da yi wa al’umma hidima.

Injiniya ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da wakilinmu, jim kaɗan kafin gudanar da walima ta musamman da kamfaninsa tare da haɗin gwiwar Masarautar Gadiman Katsina suka shirya.

“Kamar yadda ka sani, a kwanakin baya mai girma Gwamna, Malam Dikko Umar Radda ya karrama shi DPO na Malumfashi, saboda yabawa da ƙoƙarinsa a wannan gari namu, wajen tabbatar da tsaro. Don haka ne mu ma muka ga ya dace mu taya Gwamna wannan aiki, kasancewar garinmu ne kuma yankinmu ne ake wa wannan hidima.” In ji Muntari Sagir.

Baya ga DPO Bello Umar, wanda aka yi wa karramamawa ta musamman , an kuma karrama babban jami’in soja, Manjo Ajibade da kuma shugaban dakarun tsaron sakai na Malumfashi, Baba Sanusi. Haka kuma an karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da dama, waɗanda suke ba da gudunmowa ta fuskar tsaro a Ƙaramar Hukumar Malumfashi.

A hagu, DPO na Malumfashi, CSP Bello Umar, yana amsar kambin karramawa daga hannun Galadima

A jawabinsa a zauren taron, Injiniya Muntari Sagir ya jinjina wa dukkan jami’an tsaro na gwamnati da ma ‘yan sa-kai, waɗanda ke taimakawa a kowane lokaci domin tabbatar da tsaro a yankin na Malumfashi. Ya buƙaci al’umma, musamman attajirai a yankin da su taimaka wa mabuƙata. “Babu shakka, a wannan lokaci al’umma na buƙatar taimako. Dom haka masu abin hannu su taimaka. Kuma ya kamata mu sani, ka ba da taimako ba ya sa abinka ya ƙare, sai ma albarka Allah zai sanya wa dukiyar taka.” In ji shi.

Bikin wanda ya gudana a zauren taro na tsohuwar Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Malumfashi a yau Lahadi, ya samu halartar Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Alhaji Muntari Abdullahi da Galadiman Katsina, Jastis Sadiƙ Abdullahi Mahuta da Manajan Darakta na Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina, Injiniya Tukur Hassan Tingilin da sauran manyan baƙi da dama.
_______________

Previous Post

Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

Next Post

Tunawa Da Aboki Auwal Ɗanbarno

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
Tunawa Da Aboki Auwal Ɗanbarno

Tunawa Da Aboki Auwal Ɗanbarno

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Wasa Farin Girki: Yau Ake Fara Gasar Kofin Duniya

Wasa Farin Girki: Yau Ake Fara Gasar Kofin Duniya

June 11, 2026
ALI BABA: Tattaunawa Ta Musamman Da Marubucin Littattafan Musulunci

ALI BABA: Tattaunawa Ta Musamman Da Marubucin Littattafan Musulunci

July 29, 2023
Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Emefiele Tatas

Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Emefiele Tatas

June 24, 2023
RAMADAN KARIM: 06-1447

RAMADAN KARIM: 06-1447

February 23, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
  • Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
  • SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.