Daga Bashir Yahuza Malumfashi
A yayin wata shigar burtu, Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi ya yi ziyarar ba-zata a Babban Asibitin Dutse, a ranar Litinin da ta gabata, inda ya kama ma’aikatan kula da lafiyar al’umma suna hada-hadar cinikin magungunan da aka ware don bayarwa kyauta ga ƙananan yara marasa lafiya, ‘yan ƙasa da shekara biyar.
Lamarin dai ya baƙanta ran Gwamnan, inda cikin fushi ya ce abin da suka aikata ya saɓa wa tsarin jihar na kula da lafiyar ƙananan yara ‘yan qasa da shakara biyar a kyauta.
Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamna Namadi, wanda tare da shi aka kai ziyarar ta ba-zata, Malam Hamisu Muhammad Gumel ya ce Gwamnan ya bayyana wannan mummunan hali da ma’aikatan suka nuna a matsayin zagon ƙasa. Domin a cewarsa, abin ya saɓa wa tsarin jihar na kula da lafiyar ƙananan yara ‘yan ƙasa da shakara biyar a kyauta, tare da mata masu shayarwa.
“Gwamna Namadi ya nuna matuƙar damuwarsa ganin cewa, majinyata har da ‘yan ƙasa da shekara biyar ana sayar musu da magunguna a asibitin, wanda hakan sam bai dace ba, domin cin amanar gwamnati ne, inji Hamisu Gumel.
Ya ce Gwamnan da kansa ya tattauna da mata masu juna biyu da masu jinyar yara a asibitin, inda ya samu kashi 70 cikin 100 suka shaida masa cewa sun sayi maganin ne kuma ba a ba su gidan sauro ba.
Ya koka da halin sakaci da hukumar gudanarwar asibitin ke yi, alamarin da ya bayana da cewa, “daidai yake da zagon ƙasa. Kuma ku sani, duk waɗanda suka aikata wannan aika-aika, tabbas sai an hukunta su,” a cewar shi.
Wannan ziyara ta ba-zata da Gwamnan ya kai a ranar Litinin ɗin, ci gaba ne na bibiyar ma’aikatun gwmanati da yake kai wa ba zato, ba tsammani a faɗin jihar.
Ko a ranar 19 ga Yuni ma, Gwamnan ya kai irin wannan ziyara a Babbar Sakatariyar jihar da ke Birnin Dutse, inda ya gano cewa, ma’aikata kaɗan ne da wasu manyan jami’an gwamnati suka zo wajen aiki. Daga cikin Manyan Sakatarorin mulkin jihar 22, mutum uku ne kawai aka samu a bakin aiki a ofisoshinsu, a daidai lokacin ziyarar ta Gwmna.












