Zuwa Ga Sanata Ahmad Babba Kaita
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.
Bayan gaisuwa da fatan alheri, a madadin ni Bashir Yahuza Malumfashi, Fashin Galadiman Katsina-I da iyalina, ‘yan uwa da abokan arziki, ya Sanata Ahmad Babba Kaita; muna miƙa maka gaisuwa ta musamman tare da fatan alheri da addu’ar samun cikakkiyar lafiya.
Na samu labarin cewa kana jinya a asibiti, don haka muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya kasance tare da kai, ya sauƙaƙa maka wannan jarrabawa, ya ba ka ƙarfin zuciya da haƙurin da ake buƙata a lokacin rashin lafiya. Ya kuma mayar da wannan rashin lafiya ta zama kaffarar zunubai da ƙarin daraja a gare ka.
A matsayinka na ɗan siyasa da aka san ka da kula da talakawa da ƙoƙarin taimakon masu buƙata, muna fatan wannan lokaci na rashin lafiya zai zama ɗan lokaci ne kawai, sannan Allah ya dawo da kai cikin ƙoshin lafiya. Duk wanda ya san darajar lafiya ya san cewa ita babbar ni’ima ce da ba a cika gane muhimmancinta ba sai lokacin da aka rasa ta. Saboda haka, muna roƙon Allah ya dawo maka da lafiyarka cikin gaggawa, domin ka ci gaba da hidimarka ga al’umma da ayyukan alheri.
Manzon Allah (saw) ya bayyana cewa babu wata wahala ko cuta da take samun mumini face Allah ya sanya ta zama sanadin gafarar zunubansa. A cikin Sahihul Bukhari da Sahih Muslim, Annabi (saw) ya ce: “Babu wata gajiya, ko rashin lafiya, ko baƙin ciki, ko cutarwa, ko damuwa da ke samun Musulmi, har ma da ƙaya da ta soke shi, face Allah yana kankare wasu daga cikin zunubansa da ita.”
Wannan babban darasi ne ga mumini: rashin lafiya ba lallai ne ya zama azaba ba; tana iya zama jarrabawa, rahama da hanyar kusantar Allah idan mutum ya fuskance ta da haƙuri da tawakkali.
Saboda haka, ya Sanata, ka kasance mai kyakkyawan zato ga Allah a wannan lokaci. Ka sani cewa Allah shi ne mai bayar da lafiya, kuma shi ne mai ikon kawar da kowace irin cuta. Ka yi haƙuri, ka yawaita addu’a da zikiri. Wannan lokaci ya kasance maka wata dama ta ƙara kusanci da Allah da kuma tunani kan ni’imomin da ya yi maka a rayuwa.
A ƙarshe, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da sunayensa kyawawa da siffofinsa maɗaukaka, ya saukar maka da cikakkiyar lafiya, ya warkar da duk wata cuta da ke jikinka, ya kare ka daga dukkan sharri. Ya tsawaita rayuwarka cikin imani da lafiya, ya kuma dawo da kai gida cikin aminci da farin ciki.
Allahumma Rabban-nas, adhhib al-ba’s, ishfi anta ash-Shafi, la shifa’a illa shifa’uk, shifa’an la yugadiru saƙaman.
Allah ya amsa addu’o’inmu, ya ba ka lafiya mai ɗorewa, ya sanya wannan rashin lafiya ta zama kaffarar zunubai da ɗaukaka matsayi a gare ka. Amin Ya Rabbal-Alamin.
__________













