• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, July 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

TALAUCI: Yadda Matasan Arewa Ke Gararamba A Legas A Wulaƙance

Abbas Ibrahim Ɗalibi by Abbas Ibrahim Ɗalibi
October 4, 2023
in Babban Labari
0
TALAUCI: Yadda Matasan Arewa Ke Gararamba A Legas A Wulaƙance
23
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TALAUCI: Yadda Matasan Arewa Ke Gararamba A Legas A Wulaƙance

Daga Abbas Ibrahim Ɗalibi

Related posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026

~~~~~~~
Waɗansu matasa huɗu, majiya ƙarfi sun tashi daga Kano suka hau tirela suka tafi Legas da nufin neman aikin ƙarfi.

Yanzu wani abokina, Hon. Mohammed Fayama Jarimi ya turo mini hoton yaran nan, ya ce sun same su ne suna gararamba a kan babbar hanyar nan ta Legas zuwa Ibadan.

Ya ce yaran sun ce su ‘yan Jihar Kano ne a Unguwar Fagge. Sun je Kwanar Dawaki suka ba da Naira 5,000 aka ɗauko su a tirela domin su je Legas su nemi ƙwadago.

Ya ce yaran sun tara Naira dubu biyar ne ta hanyar sayar da ruwan leda da suke yi a Kano.

Fayama, ya ce yanzu haka yaran suna wajensu, sun saya masu abinci, duba da yanayin da suka same su na jigata.

Ya ce ɗaya yaron ya ce mamansa ta rasu amma babansa yana Unguwar Fagge. Ɗaya kuma ya ce auren babansa da mamansa ya mutu, yanzu haka mahaifiyarsa tana Jihar Yobe, inda take aure a can.

Ya ce yaran suna da ƙarancin shekarun da bai kamata a ce sun taho Legas cirani ba.

Mutum zai yi mamakin ko kwana nawa yaran nan suka yi a hanya a cikin tirela, ko yaya suke yi su ci abinci!

Akwai wani matashi mai ƙarancin shekaru da ya taɓa faɗa min cewa ya biyo tirela daga Kano zuwa Legas. Sai da suka shafe sama da kwana 30 a hanya kafin su isa Legas. Ya ce direban da ya biyo, kayan laifi ya ɗauko, din haka cikin sanɗa yake tafiya. A haka sai da suka shafe kwanaki 30 kafin su iso Legas.

A gaskiya ana cikin wani hali, ta yadda yara masu ƙarancin shekaru suke samun kansu cikin mawuyacin hali. Ya kamata duk mahaifin da Allah Ya ba shi ‘ya’ya, ya tabbatar ya riƙe amanar da Allah Ya ɗora masa, wajen ba su kulawa daidai gwargwadon ikonsa. Amma yin watsi da yara abu ne mai matuƙar hatsarin gaske.
~~~~~~~

Previous Post

BINTA OLA: Allah Ji Ƙan Ki Da Rahama

Next Post

MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

Related Posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista
Babban Labari

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo
Babban Labari

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria
Babban Labari

Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

June 25, 2026
Next Post
MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Huɗubar Limamin Masallacin Eriya Malumfashi

Huɗubar Limamin Masallacin Eriya Malumfashi

June 30, 2023
Visit to Biu

Ziyara Biu

May 11, 2024
TAURARON GIZAGO: Idris Ibrahim Kubau

TAURARON GIZAGO: Idris Ibrahim Kubau

August 13, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

August 13, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.