• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, August 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

YADDA SHARA TA MAMAYE BIRNIN KATSINA

Yazid Nasudan by Yazid Nasudan
September 18, 2023
in Gizago
0
YADDA SHARA TA MAMAYE BIRNIN KATSINA

Tsibin shara a Birnin Katsina

34
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

YADDA SHARA TA MAMAYE BIRNIN KATSINA!

Daga Yazid Nasudan

Related posts

Tsakanin Rarara Da Pantami: Yayin Da Maroƙi Ya Zaci Shi Wani Ƙusa Ne…

August 2, 2026
Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

July 30, 2026

~~~~~~~

Birnin Katsina kamin yanzu yana cikin birane mafiya tsafta a duk fadin Arewacin Najeriya tunda aka kafa hukumar SEPA a zamanin tsohon Gwamnan Jihar katsina Mal Umaru Musa Yar’adua yanayin tsabtar Birnin ya sauya inda a kan ga Jami’an hukumar suna ta sintiri da motocin su suna kwashe duk wata shara da aka tara a cikin unguwannin birnin, baya ga wasu ma’aikatan hukumar da suke share titunan Birnin duk safiyar Allah Ta’ala. Haka Kuma duk shekara lokacin bazara Jami’an hukumar kan bi ko Ina a fadin Birnin katsina su bude magudanan ruwa su kwashe duk wata shara ko dattin da aka zuba ciki.

Shara a wani titin Katsina

A baya bayan nan lokacin shugaban hukumar na karshe Alhaji Isah Saidu Barda hukumar ta kai kololuwar matsayi na cigaba inda bayan tsabatace Birnin katsina har ta rika gudanar da wasu ayyukan da suka hada da sarrafa sharar domin samar da taki da ta kan sayar ga manoma, ga Kuma shaguna mallakin hukumar da ta gina a wuraren daban daban cikin Birnin katsina kamar a Gwangwan ta gina kasuwar zamani da Kuma wasu a kusa rawun din liyafa. Sai dai duka wancan cigaban da Hukumar ta fara samu wanda ake ganin da ya dore nan gaba zai iya kai hukumar ga matakin da zata iya dogara da kanta, alamu na nuna cewa an baro bide baya, domin a halin da ake ciki ko sharar ma hukumar bata iya kwashewa bare Kuma a sa ran wani abu daban.

Wani abin takaici yanzu hukumar bata iya kwashe shara har sai mutane sun yi koke koke a kan hakan, Kuma idan za’a kwashe sharar har sai an gayyato Yan jarida suna dauka wai ga hukumar SEPA na kwashe shara Kai jama’a !!! Da wama ya san lokacinda suke kwasheta ? Ba sai dai ka ga babu ita ba kawai.

A halin da ake ciki yanzu gaba daya duk wani wurin da ake tara shara a Birnin katsina cike yake da sharar har ta kusa mamaye tituna, a wasu wuraren zaka ga titi ya koma hannu daya yayinda tarin sharar ya mamaye dayan hannun, a wasu wuraren ma sharar ta kashe hanya baki daya ba a iya wucewa, kamar a sabon layi bayan gidan su tsohon Gwamnan Jihar katsina Barista Ibrahim Shehu Shema hanyar ma yanzu babu ita shara ta cike wurin baki daya.

MATSALOLIN DA HAKAN KE IYA HAIFARWA

1. Idan aka yi la’akari da lokacin da ake ciki na damina wanann tarin sharar idan ruwa ya cigaba da bugunta za ta cigaba da rubewa, yayin da hakan zai sa wari ya addabi mutanen da ke makwabtaka da wurin zuba sharar.
2. Na biyu tarin sharar na iya zama wata mafaka ta kwayoyin cutar ka iya haddasa yaduwar cututtuka a cikin al’uma kamar su kwalera, sankarau, kyanda, typoid da sauransu, mun gode Allah bana ba’a samu bullar ko daya daga cikin su ba, Amma barin sharar nan na iya yin sanadin hakan Allah ya kare mu.
3. Shima sauro zai iya amfani da wannan wuri ya cigaba da hayayyafa yana cigaba da haddasa wa jama’a zazzabin malariya.
4. Baya ga kananan yara da dabbobi da a kullu yaumin suke shiga cikin bolar suna tsince tsincen da ka iya haddasa damuwa a cikin al’uma.

Duk da yake bamu san menene dalilin koma bayan wannan hukuma ba, Amma dai abune da Kowa ya saani cewa hukuma irin wannan wadda aikinta ya shafi al’uma Kai tsaye, Kuma aiki na kullum. Lallai tana da bukatar kyakkyawa Kuma ingantaccen shugabanci, tana da bukatar shugaban da yake iya yin amfani da basirarsa da kwarewarsa wajen nemo sabbin dabarun tafiyarda ita ba tare da ya tsaya jiran gwamnati a kowane lokaci ba.

~~~~~~~

Yazid, marubuci kuma mai tsokaci kan al’amuran al’umma, yana rubutu ne daga Birnin Katsina, Najeriya.

~~~~~~~

Previous Post

RABON MUƘAMAN SHUGABA TINUBU: Kuskure Kan Kuskure

Next Post

CURRICULUM VITAE OF RASULULLAH (صلي الله عليه وسلم)

Related Posts

Tsakanin Rarara Da Pantami: Yayin Da Maroƙi Ya Zaci Shi Wani Ƙusa Ne…

August 2, 2026
Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?
Gizago

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

July 30, 2026
Saƙon Godiya Da Bangajiya
Gizago

Saƙon Godiya Da Bangajiya

July 22, 2026
Next Post
CURRICULUM VITAE OF RASULULLAH (صلي الله عليه وسلم)

CURRICULUM VITAE OF RASULULLAH (صلي الله عليه وسلم)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

June 10, 2023
Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

June 3, 2026
Wawason Dukiyar Al’umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba’asin Tsohon Gwamna Matawalle

Wawason Dukiyar Al’umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba’asin Tsohon Gwamna Matawalle

June 3, 2023
KARUWANCI GUBAR KASHE MATA

KARUWANCI GUBAR KASHE MATA

January 19, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina
  • Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi
  • Zango Local Government Enjoys First-Ever General Hospital

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina

Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina

August 8, 2026
Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi

Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi

August 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.