MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana
__________
A yau Talata, 06-02-1448 (Hijiriyya), 21-07-2026 (Miladiyya), al’ummar Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina, da muka jima muna ƙishirwar hanyoyin cikin gari da sauran ayyukan ci gaba, haƙurinmu ya yi rana.
A yau, muna cikin farin ciki, domin kuwa mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda, zai jagoranci gagarumin bikin saka harsashin gina hanyoyi guda 20 ringis a cikin garin Malumfashi da kewaye.

Babu shakka, wannan babban abin murna ne kuma abin yabawa ne. Bisa ga wannan, ni Bashir Yahuza Malumfashi, Fasihin Galadiman Katsina da dukkan iyalina, Muna godiya ga Mai Girma Gwamna kuma muna taya al’ummar Malumfashi murna. Allah ya ƙaro mana ci gaba, Amin.
__________











