• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Dausayin Kauna

Soyayya: Yadda Wata Budurwa Ta Samu Mijin Kirki

webmaster by webmaster
May 29, 2023
in Dausayin Kauna
0
Soyayya: Yadda Wata Budurwa Ta Samu Mijin Kirki
65
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ADK (Alƙalin Dausayin Ƙauna) ya ci karo ne da wani muhimmin labari a turakar Facebook ta malami, ɗan siyasa kuma mai fashin baƙi kan al’amuran yau da kullum, Malam Abdullahi I. Mahuta. Labarin yana ɗauke da darussa masu yawa, musamman ma ga mata a wannan zamani. Ga yadda labarin yake:

Wani mutum ne ya haɗu da wata budurwa, ya nuna mata cewa yana son ta da aure amma bisa sharaɗi. Da budurwar ta tambaye shi ya gaya mata sharaɗin, sai ya ce mata:

Related posts

Shin Wai Akwai So? (1)

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
MENE NE SO?

MENE NE SO?

April 27, 2025

“Lallai kam zan aure ki amma bisa sharaɗi guda ɗaya tak! Wannan sharaɗi kuwa shi ne, mahaifyata tana kwance ba ta da lafiya sama da shekara goma. Don haka idan muka yi aure da ke, aikinki kawai shi ne ki kula mani da ita. Idan har za ki yi wa mahaifiyata wannan ɗawainiya, to bana buƙatar komai bayan wannan!”

Jin haka sai wannan budurwa ta shiga damuwa, kanta ya kulle, ta shiga tunane-tunane kala-kala game da wannan buƙatar ta manemin aurenta. A wani dogon tunanin da ta yi, sai ta ce wa kanta, “shin wannan mutum, a matsayin mata zai aure ni ko kuma ’yar aikin gida, mai share-share da wanke-wanke?”

Ganin cewa ta kasa gamsar da kanta da matakin da ya dace ta ɗauka, sai ta je wajen mahaifinta ta gaya masa abin da wannan masoyi nata ya ce. Kuma ta ɗauki alƙawarin duk shawarar da mahaifin nata ya yanke, za ta yi masa biyayya. Don haka sai ta saurara da kunnen basira, domin jin abin da zai gaya mata.

Mahaifin nata ya ce, “tun da kin nemi shawara daga gare ni, a matsayina na mahaifinki, wanda kuma ya san jiya da yau, to saurara ki ji ni.”

Bayan ya fahimci cewa lallai ɗiyar nan tasa ta shirya jin abin da zai gaya mata, sai ya ci gaba da magana.

“Ina son ki fahimta da wani abu guda, wato shi aikin alheri yana kare mutum daga afkawa cikin mummunar makoma. Madamar kika yi nazari kika auna abin da za ki aikata, kika tabbatar da cewa na alheri ne; to komai wahalarsa, idan kika aikata shi ba za ki yi nadama ba. Domin kuwa makomarsa za ta zama kyakkyawa.

“A game da mutumin nan da yake son auren ki kuma ya nuna cewa yana son ki kula da mahaifiyarsa, to tabbas ba zai zalunce ki ba. Idan har yana ƙaunar ki, to zai karrama ki. Idan ya ga abin da ba ya so a tattare da ke, ba zai zalunce ki ba. Ya ke ’yata, idan za ki ɗauki mahaifyarsa kamar mahaifiyarki, to babu matsala, ki aure shi kawai. Babu shakka idan dai har za ki yi wannan, to na san ba za ki cutar da ita ba ko kuma ki tauye haƙƙinta.”

Yarinya dai ta yi kasake, tana sauraren mahaifinta. Shi kuwa sai ya ci gaba da bayaninsa mai kama da huɗuba. “Daga ƙarshe, idan har kin ɗauki niyyar yin wannan aure da kyakkyawar niyya, to a duk lokacin da kika ji zuciyarki tana raya maki wani mummunan abu, to ki nemi tsarin Allah!”

Budurwa dai ta gamsu da bayanin mahaifinta kuma ta amince ta ɗauki shawararsa. Ta amince aka ɗaura mata aure da wannan mutum mai sharaɗi guda.

Bayan an yi auren sai ya ɗauke ta ya kai ta ɗakin mahaifiyarsa. Nan ta yi mamaki sosai, domin kuwa yadda ɗakin yake, kai ka ce aljannar duniya. Duk wani abin jin daɗin rayuwa akwai shi a cikin ɗakin.

Ya matsa kusa da gadon mahaifiyar tasa ya ce, “Mama ga amarya na kawo miki.”

Mahaifiyar tasa ta buɗe idonta da ƙyar saboda laulayin ciwo, ta kalle ta. Ta yi masu addu’a sosai!

Amarya ta ce, kullum ranar Allah mamakin yadda rayuwar gidan nan take yi. Ta ce awa 24 abinci da abin sha ba su yankewa a ɗakin mahaifiyarsa. Duk wani nau’in jin daɗin rayuwa akwai shi a ɗakin.

Babban abin da yake ba ta mamaki shi ne, ta ce a kullum da safe mijinta da kansa yake ɗaukar mahaifiyar tasa ya yi mata wanka, ya taje mata kai, y shafa mata mai, ya ɗauko kaya ya saka mata. Haka, in ya dawo da dare, hidimarta yake yi. Duk kayan da mahaifiyarsa ta saka ba ta maimaitawa. Haka kuma duk lokacin da ya yi mata wanka sai ya ɗauko sabon zanin gado ya shimfida mata.

Duk dare kuma yana tashi kamar sau uku don ya juya ta, don kar ta gaji da kwanciyar ɓari ɗaya. Amarya ta ce ƙurewar abin da ya fi ba ta mamaki shi ne, “ba ni da wani abu da nake yi sai dai in bai wa mahaifiyar tasa maganin da take sha da rana da kuma abincin rana. Ragowar na safe da na dare duk shi yake ba ta da kansa.”

Mijin nata ya kasance yana cewa “haƙƙina ne in kula da mahaifiyata, ba haƙƙin wani ba, domin kamar haka ta riƙa kula da ni lokacin da nake yaro. Na auro ki ne kaɗai don kula da ita a lokacin da na tafi aiki. Amma matuƙar ina gida, to duk aikinta ni zan yi kuma babu wanda zai taya ni.”

Amarya ta ce, a haka duk ƙarshen wata sai ya ba ta kyautar Naira 250,000. “Kuma ban taɓa ganin wani abin ƙyama a tattare da shi ba. Abu ɗaya na sani, babu abin da yake so kamar abin da zai faranta wa mahaifiyarsa rai!”

Bayan shekara guda amarya ta haifi ɗa namiji. Ta ɗauke shi ta kai shi wajen mahaifiyar mijinta ta ce, “don Allah ki roƙa mani Allah, ni ma Allah Ya sa wannan yaron nawa ya yi mani irin biyayyar da ɗanki yake maki!”

Dattijuwa ta kalle ta ta ce: “Ya ke ’yata, ki yi iyaka ƙoƙarinki sa’annan ki roƙi Ubangiji Ya tarbiyantar maki da ’ya’yanki, domin dukkan al’amarin gaba ɗaya a hannunSa yake!”

Sharhin ADK:
Ni kuwa ADK na ce: Ikon Allah! Na tabbata da tun da farko ba mahaifinta ta nema da shawara ba, da ba za ta dace da irin wannan zaɓin ba. Da misali ta nemi shawarar kawaye, da tuni za su hure mata kunne, su ce kada ta auri wannan mutumin, domin ’yar aiki za ta zama. Amma ga shi ta samu alheri da albarka cikin sauƙi. Wannan babban darasi ne ga mata, musamman na wannan zamanin, su riƙa neman shawarar iyayensu, maimakon ƙawaye. Ko yaya kuke gani jama’a? 

Previous Post

GIZAGAWAN NAJERIYA Sun Yi Wa ‘Dan Uwansu Alkotonawi Gangamin Addu’a

Next Post

Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (1)

Related Posts

Shin Wai Akwai So? (1)
Dausayin Kauna

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
MENE NE SO?
Dausayin Kauna

MENE NE SO?

April 27, 2025
KANA SON FAHIMTAR MATA?
Dausayin Kauna

KANA SON FAHIMTAR MATA?

November 9, 2023
Next Post
Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (1)

Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (1)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 – Sadiya Yakasai

Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 – Sadiya Yakasai

July 12, 2023
NO TO WAR

NO TO WAR

June 20, 2025
Za Mu Zamanantar Da Ayyukan Hukumar Ruwa – Injiniya Tukur

Za Mu Zamanantar Da Ayyukan Hukumar Ruwa – Injiniya Tukur

June 27, 2023
REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

August 21, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.