Daga Mahmud Isa Yola
Ba na mantawa lokacin da muka je ziyarar aiki Jihar Kano a shekaru biyu da suka gabata, Shugaba Janar MB Marwa (mai ritaya), agogo ne sarkin aiki. Duk wanda ya fita aiki da shi, in bai yi shiri ba sai ya ji kunyar kansa saboda ko kaɗan idan ya fara aiki, bai san ya tsaya hutu ba. Mukan bar otal namu da misalin ƙarfe biyar zuwa biyar da rabi na safe, inda za mu tarar da shi ya shirya yana jiran mu. Haka za mu zagaya ƙwaryar jihar yana gane wa idanunsa tare da tattaunawa da shugabannin al’umma a kan yadda za a kiyaye jama’a daga faɗawa halakar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
A wannan lokacin ragwanci yake bayyana, kasala take nunawa, haka kuma a ɗaya ɓangaren, jajircewa ce kadai za ta tasirantar da aikin mutum.
Hafsat, ‘yar jarida ce da take kula da labarun da suka shafi sha da hulɗa da haramtttun magunguna. Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ko da na sakan ɗaya. Koyaushe idan na waiga motar da take ɗauke da ‘yan jarida, zan ga Hafsat tana riƙe da wayarta, ko takada da alƙalami. Yayin da da dama daga cikin abokan aikinta da muka fara tare suka yi ɓatan dabo.
Hafsat ta haɗa jajircewa da hazaƙa da sanin makamar aiki. Wannan ya sa a duk lokacin da ta yi aiki a kan labarun da suka shafi aikinmu, ba ni da fargabar samun matsala. Saɓanin wasu ‘yan jarida da a koyaushe dole sai mun bibiyi bayanansu, saboda gudun tuntuɓe n alƙalami ko ƙazamin aiki.
To amma, yanzu ne asalin ƙalubalen aiki zai cin ma Hafsat. Saboda misalin canjin wurin aikinta shi ne misalin direba wanda ya koma aikin VIO ko kuma Hukumar Kiyaye Haɗurra (Federal Road Safety Commission)Road. Saboda ta taso ne daga waɗanda ake lura da aikinsu zuwa waɗanda suke lura da aikin wasu!
Ɗazu nake ganin bidiyon da Hafsat take karanta labaru na ƙarshe, inda ta fashe da kuka saboda rabuwa da abokan aiki na arziki. Ina fata ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a sabon aikin da za ta fara kuma ina fata za ta ci gaba da jajircewa ƙwarai da gaske a kan aikinta.
Ina kuma sane da cewa ta bar giɓin da duk wanda zai cike shi sai ya yi da gaske kuma ni kaina zan yi kewar aiki da ita.
Allah Ya taimaka.
~~~~~~~
Malam Mahmud Mataimaki Ne Na Musamman Ta Fuskar Watsa Labarai ga Shugaban Hukumar Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoji, Janar Buba Marwa (mai ritaya).
~~~~~~~













