Tattaunawa Ta Musamman Da Dokta Bukar Usman Da Sashen Hausa Na Rediyo Faransa (RFI)
Bisa Lambar Girmamawa da Kungiyar Ƙwararrun Masana Ta Najeriya Ta Ba Shi
Gabatarwa:
Masu sauraro, Assalamu alaikum. Barkan mu da saduwa da ku a cikin shirin Duniyarmu A Yau daga Sashen Hausa na Redio France International, tare da Bashir Ibrahim Idris. Ƙungiyar Ƙwararrun Masana ta Najeriya wadanda suka yi fice a fannin al’adu da rayuwar bil’adama da ake kira da Nigerian Academy of Letters ta karrama ɗaya daga cikin fitattun marubutan Najeriya, Dokta Bukar Usman saboda gudunmawar da ya bayar wajen rubuce-rubucen da yake yi, domin ci gaban al’umma, da ta sanya shi ɗaya daga cikin ’ya’yanta, a bikin da ya gabata a Jami’ar Legas. Bayan bikin, Dokta Usman ya ziyarci ofishinmu, inda za mu tattauna da shi a kan wannan karramawa da aka yi masa.
••••••• •••••••

Rfi Hausa: Dokta, barka da zuwa.
Dokta Bukar Usman: Malam Bashir, na gode.
Rfi Hausa: To da farko, me za ka ce game da wannan karramawar da wannan Ƙungiya mai matuƙar muhimmanci ta yi maka?
Dokta Bukar Usman: Kamar yadda na ce musu jiya, bayan da suka karrama ni, na ce ina godiya ƙwarai da gaske da mutunta ni da suka yi. Kuma na ce a halin yanzu a duniya, lallai mutane ko da sun ce ina rubutu, a kowace al’umma akwai jinin rubutu a jikinsu. Na ce kamar hamada ce, ana cewa babu itatuwa, babu… amma in ka dasa wani iri ka ba da ruwa zai tsira.
Saboda haka kowace al’umma tana da shi kuma idan ka duba wasu tsararrun marubuta na Najeriya, ba wajen fasaha kawai, ko kuma al’amuran da suka shafi al’umma (Arts) kawai suke rubutu ba. Na ce Allah Ya halicci mutane da hikima ta rubutu kuma bayan wannan, suka ce akwai wasu abubuwa da nake yi don taimakon al’umma. Na ce e, haka ya yi. Kuma a cikin duniya, ka yi abin kirki wanda mutane za su yaba, domin dai ni ban je na roƙi kowa ba. Su suka kira ni, suka ce ga shi. Ni da wani mutun ɗaya, Dokta Wale Okediran, wanda shi ne Babban Sakatare na Ƙungiyar Marubuta ta Afirka (PAWA) da ke Accra Ghana. Na ce masu ina godiya da wannan karramawa da suka yi mani.

Rfi Hausa: To, ko sun shaida maka dalilin da ya sanya suka zaƙulo ka daga cikin tarin mutanen da ke Najeriya, domin wannan karramawa?
Dokta Bukar Usman: Sun rubuto mani, cewa ga shi-ga shi kana taimakon al’umma, kana rubutu kuma ka yi fice, don haka muke son mu karrama ka, kai da wani ɗan Najeriya shi ma; ban da waɗanda membobin wannan Ƙungiya sababbi da yawa, an karrama su. Cikin waɗanda aka karrama da lambar yabo da ake kira da Honorary Fellows, mu biyu ne kawai Dokta, sauran duka Farfesoshi.
Rfi Hausa: Wannan ya nuna cewa sai da suka yi bincike, suka tantance irin gudunmawar da kake bayarwa da rubuce-rubucen da kake yi, kafin aka ɗauko ka?
Dokta Bukar Usman: Su dai ne suka sani amma a cikin mutanen da suke zaɓa, hanyoyin tantancewar da suke bi suna da tsauri matuƙa (very stringent). Suka ce, kafin ma ka zama Memba a Ƙungiyar, sai ka kai shekara 5 a muƙamin Farfesa. Kuma kamin ka zama Fellow na ƙungiyar sai ka kai shekara goma da zama Farfesa. Kuma ko da ka kai shekara biyar ko goman, ba kawai za su miƙa maka ba ne, sai sun yi bincike sosai, sun tantance. Don haka, namu ma sai da suka tantance.

Rfi Hausa: Wannan dai ba shi ne na farko ba, ka samu karramawa daban-daban, a matakai daban-daban, waɗanda idan muka ce za mu lissafa su, muna iya kwashe lokacin da muke da shi a wannan shiri. Kamar ita wannan da aka yi maka, ya za ta ƙarfafa ka kan waɗannan ayyuka da kake yi?
Dokta Bukar Usman: Batun ƙarfafawa, kafin mu shigo wannan ɗakin shirye-shirye (studio), mun yi ɗan zance kaɗan ko? Kuma na gaya maka cewa kwanakin baya ko shekarun baya, akwai lambar da aka ba ni ta ƙasa da kuma game da fasaha da rubutu. Sun yi yawa, kusan fiye da 23 a lokacin. To, wasu sun zo suka ce suna son su kara karrama ni, na ce don Allah a yi mani afuwa. Na ce abin ya isa haka nan, domin abin ba kayan ado ba ne. Amma daga baya sai abokan zama, yau da kullum suka ce mani, kai wannan abun da suke so su yi maka, ba kai kadai kawai suke karramawa ba, saboda haka bai kamata ka ce ba za ka karɓa ba. Shi ne na ji shawarar mutane, na ce to gaskiya ne.
Dalili ke nan na amshi wannan, sannan kuma na koma wa mutanen da a can baya suka ce za su karrama ni na ƙiya, na ce masu su yafe mani, na yi kuskure. Amma a yanzu haka, duk wani abu da Ubangiji ya nufa, zan karɓa. Kuma karramawa da suke yi mani, yana ƙara mani ƙaimi na ci gaba. Idan kana yin wani abu, idan mutane ba su yabawa, ai ba za ka ci gaba ba sosai. Amma idan yau ka yi wani abu, ana yi maka tafi, ai sai ka ƙara sosai ko?
Rfi Hausa: Sosai haka ne.
Dokta Bukar Usman: Kuma a yanzu haka, a ƙarshen wannan shekarar zan cika shekara 82 a duniya kuma ga shi Allah Ya ba ni lafiya. Ubangiji Ya taimake ni, duk littattafan da nake wallafawa, ba na sayarwa. Haka nake rabawa domin taimakon ilimi kuma zan ci gaba da rubutu in Allah Ya yarda, sai idan ƙarfi ya ƙare, na kasa. Wani ɗan jarida ya tambaye ni cewa, “yanzu ka daina rubutu ne?” Na ce a’a, in sha Allah kafin wannan shekarar ta shige ko kuma sabuwar shekara mai zuwa, akwai wasu littattafaina da za su fito. Lokacin da na cika shekara 80 a baya, na yi tunanin ai ya kamata in rubuta wani abu.
Rfi Hausa: Gaskiya ne.
Dokta Bukar Usman: To shi ne na tashi tsaye na tsara wasu abubuwa, in Allah Ya yarda littafin zai fito. Na duba baya, na ce kuma bari in dubi gaba batun sha’anin duniya da na Najeriya duka, na duba, na ba da ra’ayina a wannan littafin wanda zai fito sabo. Bayan haka, akwai wani da ya ce mani, “ka ba da tarihinka na aikin gwamnati. Ka ba da tarihinka na rubuce-rubuce. To, ina na tarihinka game da gudumawarka a fagen tatsuniyoyi?” Na ce masa ai na rubuta wasu littattafai a kan tatsuniyoyi, me ya sa kuma zan ƙara? Ya ce “a’a, ka je ka yi mana rubutu, daga tushe har zuwa yau.” Shi ne kuma idan Allah Ya yarda zan kammala aikin wallafar sa a nan kusa, domin yana kan hanya.

Rfi Hausa: To, masu sauraro za su so su ji wasu daga cikin littattafan da ka rubuta.
Dokta Bukar Usman: Littattafan suna da yawa, musamman fiye da arba’in. To yaya za a yi in iya lissafawa?
Rfi Hausa: …wasu daga ciki muka ce.
Dokta Bukar Usman: Shi ne na ce maka na rubuta littafi kan batun aikina na gwamnati. Shi ma yana daga cikin dalilan da suka sanya na shiga harkar rubutu. Na ce na yi aikin gwamnati fiye da shekara 30, ya kamata duk inda mutum ya yi aiki, a ɗauko a yi rubutu… har da ku ma masu aikin jarida. Amma kana aiki, ka cika shekara 30, bayan ka gama sai ka je kawai ka zauna?
A’a, na ce a baya ina ta rubutu a cikin fayil, yanzu na shigo duniya, bari in yi abin da mutane za su karanta, mene ne abin da na yi a gwamnati? Yana ɗaya daga cikin abubuwan da ya sanya nake rubutu. Kuma ta ɓangaren tatsuniyoyi, na ce na gani lokacin da muke yara, iyayenmu idan sun je gona sun dawo, a lokacin babu talabijin babu rediyo; sai tatsuniya, da ake wa yara a cikin farin wata.

To yau ina muke? Wasu tsofaffin ma da suke yin tatsuniyar mutuwa suke. Shi ya sa na ga cewa ya dace in adana su a rubuce. Na ce wasu littattafan ma da Abubakar Imam, wani marubuci shahararre a Arewa ya rubuta, a lokacin muna karatu – Ka Yi Ta Karatu, Ka Kara Karatu, a yau waɗannan littattafan idan kana nema, da wuya ka samu, sai dai su Tom & Jerry.
Shi ne na ce ya isa haka nan, bari in yi ƙoƙari in tattara tatsuniyoyi namu, kafin waɗanda suke riƙe da su a ƙwaƙwalwarsu su ƙare. Yanzu na tattara tatsuniyoyi fiye da 4,000 daga dukkan ɓangarorin Najeriya kuma muna kai har yanzu ina kan ci gaba da hakan, ban dakata ba. Ina zaton wataƙila a laburare naku nan akwai littattafaina da na wallafa.
Rfi Hausa: Haka ne.
Rfi Hausa: To wai ita wannan rayuwa taka ta rubuce-rubuce, gado ne ko kuma taka-haye?
Dokta Bukar Usman: Babu gado. Iyayena ba su yi karatu ba. Lokacin da na tashi daga Biu a ƙasar Borno, na je makaranta a Maiduguri. Da na je makaranta a King’s College, a nan Legas, basu san sunan makarantar ba. Ba sa tambaya ta ina refot, ina mene ne na makaranta? Babu, amma idan na tashi zuwa makaranta, za su ba ni ɗan guzurin da za su ba ni. Kuma wurin karatu, iyayena ba su biya ko kwabo ba, duk gwamnati: Gwamnati ce, watau Gwamnatoci da Hukumomi na Biu da na Borno da na Arewa gaba ɗaya da na Jamhuriyar Najeriya, duk su suka ɗau nauyi na yi karatu.
Akwai ma ɗan abin kashewa da suke ba ni, wanda a ciki nake ɗan ajiyewa, har na je na yi wani gini a gidanmu, ɗaki ciki da falo. Har yanzu yana nan, a cikin kuɗin tallafin karatu da gwamnatin ke ba ni na gina. A lokacin nan ina karatu a Jami’ar Ahmadu Bello na gina wannan ɗakin a gidanmu da yake Biu. Yana nan, idan mutum ya je gidanmu na gargajiya zai ga wannan gini yana tsaye har yanzu.
Rfi Hausa: Masu sauraro har yanzu kuna tare da sashen Hausa Rediyo ta Faransa in da muke tattaunawa da bakon mu Dokta Bukar Usman tsohon Baban Sakatare a Ofishin Shugaban Kasa wanda ya kwashe fiye da shekaru talatin kamin ya yi ritaya kuma shahararren marubuci wanda aka karrama shi a nan Birnin Legas.

Rfi Hausa: Dokta Usman, zamani ya kawo mu lokacin da ake cewa mutane ko kuma matasa ba su son yin karance-karance kamar irin yadda kuka yi a da, musamman ma a wannan zamani na wayoyi da intanet da sauransu. Me ya haifar da haka?
Dokta Bukar Usman: Zamani ne ya canja. Amma wani ɗan jarida a shekarun da suka shuɗe ya tambaye ni irin haka, na ce ba za a ce don canjin zamani mutane ba za su yi karatu ba. A’a, idan ka duba yanzu ba ana gasar ƙwallo a Olympic a Faransa ba, ka duba sitadiyom yadda mutane suke cika? Suna da akwatunan talabijin a gidajensu. Me ya sa suke zuwa sitadiyom kallon wasan?
Haka ma abin yake a wajen karatu. Kodayake mutum yana da wayar hannu, yana karatu da ita amma ba za a ce wani lokaci zai zo da mutum ba zai ɗauki littafi ya karanta ba, babu. A haka za mu yi ta tafiya. Ga canjin zamani, yadda mutane za su je su yi harkoki a zamanance amma rubutu dai har yanzu, mutane za su riƙe littafi su karanta. Shi ne na ba da misali da yadda mutane a ƙasashen Turai ba su tsayawa a gida domin kallon wasanni a talabijin, suna cika sitadiyom nasu har yau. Za ka ga mutane kimanin 60,000, wani 80,000 a sitadiyom. Me ya sanya suke tururuwar cika gidajen wasannin a zahiri? To haka za mu ci gaba da tafiya.
Rfi Hausa: Dokta, Najeriya ta samu kanta a cikin wani yanayi na dimbin yaran da ba su zuwa makaranta, musamman a yankin Arewa da muka fito. Alƙaluma sun ce daga cikin yara kusan miliyan 18 da ba sa zuwa makaranta, sama da miliyan 14 suna Arewacin Najeriya. Me za ka ce a kan wannan?
Dokta Bukar Usman: Wannan gaskiya ne. Yanzu idan kana tafiya a layi, a cikin garuruwa na Arewa, da yawa za ka gani yara riƙe da ƙoƙo suna ta bara. Kuma wasu na ganin cewa sai karatun allo za su yi, ban da na duniya. Ni kuma ina ganin cewa kar a bar karatun allo amma ya kamata a haɗa karatun allo da kuma ilimin zamani. Kuma ina fatan gwamnatoci da hukumomin Arewa za su tashi tsaye su shawo kan waɗannan matsaloli na karatu.
Haka ma ta fannin noma, muna da ƙasa babba amma za ka ga mutane ba su yin noman zamani, kamar yadda za ka gani a ƙasashen waje. Na ce a yau na shekara tamanin da wani abu amma idan na tashi daga Maiduguri zuwa Abuja, a kan hanya, ba wata gona da za ka gani ka ce, zo ka ga wata gona abin sha’awa duk daji ne yawanci. A da mutanen Najeriya ana cewa miliyan 20, yau ana cewa miliyan 200 da wani abu.
A yanzu haka da fartanya kawai za mu ciyar da mutane? Ba zai yiwu ba, dole ne a kawo kayan aikin gona na zamani, waɗanda za su sanya mu iya ciyar da mutanenmu. A Arewa abin kunya ne a ce har yanzu muna da ƙasa amma mun ƙyale ta ba mu nomawa yadda ya kamata. Ya kamata mu tashi tsaye.
Gwamnatocin Arewa, ga abubuwa guda ukku da mutum zai so a ce an tsaye a kansu: Wajen noma, ilimin zamani da kuma tsaron ƙasa. Yadda hankalin mutane zai kwanta, su je gona su dawo gida, ba abin da zai dame su. A yau saboda tashin hankali ana cikin damuwa ƙwarai da gaske. Manoma, ba ma kawai rashin kayan aiki ba, ko suna da kayan aikin ma, su je gonar a yau ma akwai wahala saboda matsalar tsaro.
Ya kamata gwamnatocin Arewa su tashi tsaye, su tunkari samar da waɗannan abubuwa guda uku, noma, karatun zamani da kuma inganta tsaro, domin mutane su samu kwanciyar hankali, su iya zuwa gonakinsu su dawo lafiya. Don farashin kayan abinci sai hauhawa yake yi saboda manoma ba su samun damar zuwa gonakinsu koda da fartanyar ma, ba ma batun na’urar noman zamani ba.
Rfi Hausa: To ita wannan matsala ta rashin zuwan yara makaranta, daga gwamnati ne ko kuwa daga Iyayen yara ne?

Dokta Bukar Usman: Uhm, to, ba laifin iyayen yara ba ne. Lokacin da na tafi makaranta, iyayena ma ba su ba ni izinin cewa in tashi in je ba. Ina wasa a kan layi sai dogari ya kama hannuna ya kai ni gaban Sarki, tare da abokina. Muna makarantar tsangaya ne a lokacin, aka kai mu gaban Sarki muka durkusa. Sarki ya ce mana mu tafi makaranta kuma haka aka kai mu makarantar kai tsaye. Ina magana ne a shekarar 1951. Don haka ba laifin iyaye ba ne batun ilimin yara.
Idan dai gwamnati ta tsaye, mutane za su je. Ma’ana ta gina makarantu, domin a yanzu wasu wuraren ma babu makarantun. Kodayake idan gwamnati ta tsaye, ko a gindin bishiya sai a yi karatun. Amma dai ana son a samu kwanciyar hankali, yadda yara za su je makaranta su dawo ba tare da wata fargaba ba. Ba batun iyaye ba ne ba. Kamar yadda na ce, iyayena ba su yi karatu ba, ba su ma san yadda nake zuwa makaranta ba, sai dai in je su ga na dawo, sai dai su ba ni guzuri.
Na tashi daga Maiduguri zuwa Legas, ina maganar shekarar 1964, akwatina ya fadi a kan hanya. Na zo nan, Baturen makaranta ya ba ni akwatinsa. A lokacin daga Maiduguri zuwa Legas babu kwalta sai hanya mai gargada-gargada, shi ne akwatina ya faɗi da satifiket nawa, har yau ba a same su ba.
To, ba batun iyaye ba ma, gwamnati tana da haƙƙi ta gina makarantu domin mutane su je kuma waɗanda iyayensu ba su da halin biya, ya kamata a biya masu. Ni daga firamare har zuwa jami’a, iyayena ba su biya ko kwabo ba tun daga 1951 har zuwa 1969 da na gama karatu a Jami’ar Ahmadu Bello.
Rfi Hausa: Daga ƙarshe, wane saƙo kake da shi ga masu sauraronmu, musamman ma masu karance-karancen littattafan da ka wallafa?
Dokta Bukar Usman: To, ni dai na yi nawa rubutu. Kamar yadda Mamman Shata ya ce game da masu sana’a, ka kasa yau ba a saya ba, ka kasa gobe ba a saya ba, ai za ka daina. To amma kodayake na ce ba na sayar da littattafaina amma har yanzu mutane suna buƙatar a ba su su karanta. Ba a nan cikin gida Najeriya ba, har ƙasashen waje, littattafaina sun shiga wurare daban-daban.
To abin da nake godiya ke nan, cewa ashe burina na rubutu ya cika. Saboda abubuwan da na yi a gwamnati da kuma tatsuniyoyi da na tattara don kada su ɓace, har yanzu mutane suna yabawa kuma shi ne yake ƙarfafa mani gwiwa. Idan dai ina raye kuma Ubangiji Ya ba ni lafiya kuma Ya ba ni hanya da dama in wallafa, zan ci gaba. Sai dai kwakwalwa na ya kasa. Kuma ina fatan wasu ma za su biyo bayana, su yi haka.
Rfi Hausa: Dokta Bukar Usman, mun gode sosai da wannan ziyara da ka kawo mana muka tattauna.
Dokta Bukar Usman: Ni ma ina godiya, Malam Bashir. Kuma ina son in miƙa ta’aziyyata ta babban abokin aikinku kuma abokin aikina, Malam Muhammed Hamissou Salissou, wanda ya rasu. Allah Ya ji ƙan shi.
••••••• •••••••
Rfi Hausa: To mun gode sosai. To masu sauraro, da haka muka kawo ƙarshen wannan shiri. A madadin babban baƙon namu, Dokta Bukar Usman, marubuci kuma tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya da Injiniyanmu, Mustapha Adebisi da Sashen Hausa na Gidan Radio France International, sai kuma Ƙaribullah Abdulhamid Namadobi da Bashir Ibrahim Idris muke cewa ku huta lafiya.
••••••• •••••••













