Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
Tare da nauyayyar zuciya na samu labarin rasuwar marubuci, ɗan uwa mai barkwanci da zumunci, Malam Auwalu Garba Ɗanborno.
Batun cewa shi mutumin kirki ne, wanan tabbas ne. Ga shi mai tsinkaye da zurfin tunani, musamman a rubuce-rubucensa mutum zai tabbatar da haka.
Muna roƙon Allah Ya yi masa rahama, Ya tallafa wa zuri’arsa. Amin!













